Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu
Published: 28th, October 2025 GMT
An ɗage sauraron shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, matarsa Hafsat, da wasu mutum shida a ranar Litinin bayan sun kasa miƙa takardun da ake buƙata a kotu.
Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da su bisa tuhume-tuhume 11 da suka shafi cin hanci, haɗa baki wajen yin laifi, da karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai miliyoyin Naira.
Lokacin da aka fara sauraren shari’ar, lauya mai kare gwamnati, Adeola Adedipe (SAN), ya ce sun shirya fara gabatar da shaidu, amma lauyoyin Ganduje da sauran waɗanda ake tuhuma suka nemi ƙarin lokaci, inda suka bayyana cewar ba a ba su wasu takardu ba.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Amina Adamu-Aliyu, ta umarci dukkanin ɓangarorin su kammala miƙa takardunsu kafin zaman kotun na gaba, sannan ta ɗage shari’ar zuwa 26 ga Nuwamba, 2025.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Yaba Wa Jami’an Tsaro Kan Ceto Dalibai 100 Da Aka Sace A Neja
“Umarna ga jami’an tsaro har yanzu ita ce cewa dole ne a ceto dukkan daliban da sauran ‘yan Nijeriya da aka yi garkuwa da su a fadin kasar nan, a dawo da su gida cikin aminci. Dole ne mu tabbatar da an kirga duk wanda lamarin ya rutsa da shi.
“Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiki tare da Jihar Neja da sauran jihohi don tsare makarantu da kuma samar da ingantacciyar muhalli mai aminci da dacewa domin karatun ‘ya’yanmu.
“Daga yanzu, jami’an tsaro tare da gwamnonin jihohi dole su hana afkuwar garkuwa da mutane a nan gaba. Ya kamata yaranmu su daina zama abin hari ga mugayen ‘yan ta’adda da ke kokarin dakile iliminsu tare da jefa su da iyayensu cikin azaba marar misaltuwa.”
ShareTweetSendShare MASU ALAKA