Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba
Published: 29th, October 2025 GMT
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu October 28, 2025
Daga Birnin Sin Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona October 28, 2025
Daga Birnin Sin Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin October 28, 2025
এছাড়াও পড়ুন:
Ƙaddamar da Kyautar Jaruman Indomie Karo na 17: Matasan Najeriya Sun Fafata, An Samu Zakaru
An kammala bikin bayar da Kyautar Jaruman Indomie karo na 17, inda aka karrama matasan da suka nuna hazaƙa da jarumtaka, kuma suka zama jakadun Najeriya a fannoni daban-daban.
Wannan gagarumin biki ya gudana a birnin Legas a ranar 16 ga Oktoba, 2025, ƙarƙashin shirye-shiryen kamfanin Dufil Prima Foods, masu samar da Indomie Instant Noodles, a wani ɓangare na shirin kamfanin na kyautata dangantaka da al’umma (CSR).
Kamfanin ya tabbatar da bayar da kyaututtuka ga Jaruman Indomie — wani girmamawa na musamman ga matasan da suka nuna jarumta da Ƙirƙire-ƙirƙire a faɗin ƙasar.
Taken bikin na bana shi ne “Jaruman da Ba a San Su ba”, inda fitattun matasa uku daga sassan Najeriya suka fito a matsayin zakaru, bayan sun nuna bajinta, halin kirki, da jarumta.
Daga ranar 11 zuwa 13 ga Oktoba, 2025, miliyoyin ’yan Najeriya suka bibiyi shirye-shiryen talabijin na ƙasa domin jin labaran waɗannan matasa masu ban mamaki, waɗanda suka motsa zukata tare da ƙarfafa gwiwar al’umma.
Bayan wani dogon tsarin tantancewa da aka gudanar a duk faɗin ƙasar — wanda ya haɗa da hirarraki da makarantu da al’umma — an zaɓi zakaru uku daga rukuni daban-daban:
Abraham Umoren, mai shekaru 9 daga Jihar Akwa Ibom, ya lashe gasar Physical Bravery — jarumta ta zahiri.
Ismail Muhammad, mai shekaru 13 daga Jihar Kwara, ya lashe gasar Social Bravery — jarumta ta zamantakewa.
Hassan Adamu, mai shekaru 15 daga Jihar Yobe, ya lashe gasar Intellectual Bravery — jarumta ta basira.
An zaɓi waɗannan jarumai ne daga dubban matasa da aka gabatar daga sassa daban-daban na ƙasar, bayan watanni na bincike da tantancewa daga kwamitin masu zaman kansu da Dufil Prima Foods ta amince da su.
Da yake jawabi a ƙarshen bikin, Manajan Sadarwa na Rukunin Kamfanoni na Dufil Prima Foods, Temitope Ashiwaju, ya ce: “Kowace shekara muna ganin zurfin jarumta, fasaha, da baiwar da yaran Najeriya ke nunawa. Wannan shiri ne da muke alfahari da shi domin tallafa wa matasa wajen ciyar da ƙasa gaba.”
Ya ƙara da cewa: “Kyautar Jaruman Indomie ba kawai biki ba ne, amma madubi ne da ke nuna makomar Najeriya. Labaran waɗannan yara suna tunatar da mu cewa jarumta ba ta takaitu ga shekaru ko matsayi ba, sai dai a cikin ayyukan da ke ɗaga darajar wasu.”
Zakarun matasan sun nuna farin ciki da godiya bisa wannan dama, inda kowannensu ya gode wa Indomie saboda wannan girmamawa, tare da yin alƙawarin ci gaba da yin abin alheri a cikin al’ummominsu.
“Ba mu taɓa tsammanin za a yi irin wannan biki ba,” in ji Abraham Umoren, yana ƙara da cewa: “Na gode Indomie. Zan ci gaba da taimaka wa wasu gwargwadon iyawata.”
A bana, an gudanar da wannan biki na farko a matakin jihohi, inda aka girmama matasa daga kowanne rukuni, tare da faɗaɗa damar da aka samu don karrama ƙarin matasa masu kawo sauyi a Najeriya.
Tun daga lokacin da aka fara wannan shiri a shekarar 2008, matasa 59 suka riga sun amfana da tallafin karatu na miliyoyin naira — a matsayin yabo da ƙarfafa gwiwarsu don ci-gaban al’umma.
Bikin na bana ya bai wa iyalai, malamai, da shugabanni damar jin labaran da ke ci gaba da karfafa bege da juriya a cikin al’ummomi.
Kyautar Jaruman Indomie ta ci gaba da zama shaida ga jajircewar kamfanin Dufil Prima Foods, wanda ya daɗe yana ƙoƙarin haɓaka shugabanci, nuna tausayi, da kishin ƙasa a cikin manufofinsa na cigaban Najeriya.