Al-Burhan: Sojojin Sudan Sun Janye Daga El-Fasher Saboda Kare rayukan Fararen Hula
Published: 28th, October 2025 GMT
Babban hafsan hafsoshin Sojin Sudan kuma shugaban majalisar gudanar da mulkin kasar ya bayyana cewa; Rundunar sojin kasar ta bar birnin El Fasher ne domin gujewa “kisan fararen hula” da dakarun kai daukin gaggawa ke yi
Shugaban Majalisar Gudanar da Mulkin Soja ta Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce: shugabannin sojoji sun yanke shawarar barin birnin El Fasher da ke Jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan ne, domin kare birnin da ‘yan kasar daga afkawa cikin matsalar kisan kai a hannun Rundunar Rapid Support Forces ta dakarun Kai Daukin Gaggawa.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Anadolu, al-Burhan, wanda ke jagorantar rundunar sojin Sudan, ya ce a wani jawabi da aka watsa ta talabijin a gidan talabijin na gwamnati: “Kowa yana bin abin da ya faru a El Fasher, kuma shugabannin da ke can, ciki har da kwamitin tsaro, sun yanke shawarar cewa dole ne su bar birnin saboda halaka da kisan fararen hula.”
Ya bayyana cewa shugabannin sojoji a El Fasher “sun yanke shawarar barin birnin, kuma sun amince da fice daga cikinsa, bisa sharadin cewa za su bar birnin zuwa wuri mai aminci don ceton sauran ‘yan kasar da sauran birnin daga halaka.” Ya kara da cewa: “Wannan yana daya daga cikin matakan ayyukan soji da aka dora musu a matsayinsu na al’ummar Sudan, kuma koyaushe suna fadin hakan, kuma suna maimaitawa: al’ummar Sudan za su yi nasara, kuma Sojojin Sudan za su yi nasara.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Baqaei: Iran ta daɗe tana aiki don haɓaka zaman lafiya a duniya October 28, 2025 An Yi Girgizar Kasa Mai Karfi A Kasar Turkiya October 28, 2025 Ouattara Na Kasar Ivory Coast Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa October 28, 2025 MDD Ta Yi Kira Da Abude Kafar Shigar Da Kayan Agaji Zuwa Garin El-Fashar October 28, 2025 Wilayati: Kasashen Ian, China Da Rasha Suna Taka Rawa A Fagen Kafa Sabon Tsarin Duniya October 28, 2025 Zaben Ivory Coast: Alassane Ouattara na kan gaba da tazara mai yawa October 27, 2025 Pezeshkian: Hadin kan Musulmi zai iya dakile zalincin kasashen waje October 27, 2025 Amurka ta tsare wani dan jarida musulmi saboda sukar Isra’ila October 27, 2025 Kashi 84% na ‘yan Faransa ba su gamsu da Macron ba a matsayin Shugaba October 27, 2025 Iran ta bukaci MDD ta nisanci nuna bangaranci game da masu keta dokokin duniya October 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mayakan Kungiyar Kurdawa Ta PKK Sun Fice Daga Turkiyya Zuwa Iraki
Kungiyar Kurdawa ‘yan tawaye ta PKK ta sanar da janye dukkan dakarunta daga Türkiyya zuwa arewacin Iraki
Kungiyar kurdawa ‘yan tawaye ta PKK ta sanar da janye dukkan dakarunta daga cikin kasar Turkiyya zuwa arewacin Iraki a yau Lahadi.
Kafafen yada labarai sun ambato wata sanarwa daga kungiyar ‘yan tawayen kurdawar tana cewa: “Ta janye dukkan mayakanta daga cikin kasar Turkiyya zuwa yankunan arewacin kasar Iraki.
A watan Fabrairun da ya gabata ne, Abdullah Ojalan, wanda ya kafa kungiyar Ma’aikata ta Kurdistan (PKK) a Turkiyya, ya yi kira da a rusa kungiyar, yana mai kira ga mayakan kungiyar da su ajiye makamansu su koma ga daukar matakin siyasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Za Ta Karbi Bakuncin Taron Kungiyar Tattalin Arziki TA “Eco” A Gobe Litinin October 26, 2025 Bahrain: Fursunoni 90 Suna Yajin Cin Abinci Saboda Neman ‘Yanci October 26, 2025 Shugaban Kasar Nigeria Ya Yi Sauye-sauye A Rundunonin Sojan Kasar October 26, 2025 Iran Ta Ki Zuwa Taron Sherme-Sheikh Ne Saboda Kar Ta Zama Mai Shaidar Zur Akan Kisan Kiyashin Gaza October 26, 2025 Jami’ar ABU Ta Karyata Zargin Da Ake yi Na Kera Makamin Nukiliya A Asirce October 25, 2025 M D D Ta ce Akalla Mutane miliyan 1.5 Ne Ke Bukatar Taimakon Gaggawa A Gaza October 25, 2025 Tony Balai Na Fuskantar Turjiyar Kasashen Larabawa Game Da Rawar Da Zai Taka A Gaza. October 25, 2025 Yau Ne Ake Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Ivory Coast October 25, 2025 Iran Za ta Karbi Bakunci Taron Ministocin Cikin Gida Na Kungiyar ECO October 25, 2025 Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Kiran Da A Nisanci Siyasantar Da Kwamitin Tsaron Majalisar October 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci