HausaTv:
2025-12-13@00:00:05 GMT

Hamas : Netanyahu Yana kokarin wargaza yarjejeniyar tsagaita wuta

Published: 28th, October 2025 GMT

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa duk da jajircewar kungiyar na mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da ita, firaministan gwamnatin Isra’ila yana kokarin karya sharuddanta.

Hazem Qassem, kakakin kungiyar, ya ce “Mun yi wa masu shiga tsakani bayani kan cikas din da ke hana neman gawarwakin fursunonin Isra’ila kuma mun nemi su samar mana da karin kayan aiki.

Mai magana da yawun Hamas ya kuma bayyana cewa: “Mun sanar da Alkahira game da ayyukan bincike na ‘yan Isra’ila, kuma muna ci gaba da sanar da masu shiga tsakani game da ci gaban binciken.

Duk da tsagaita wuta da aka yi tsakanin gwamnatin Tel Aviv da kungiyar Hamas, sojojin Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare.

Na baya bayan su ne ta jirgin sama mara matuki a kusa da garin Khan Younis da ke kudancin Zirin Gaza, inda suka kashe akalla mutane biyu, a cewar majiyoyin lafiya.

Masu ba da agajin gaggawa a Asibitin Nasser sun ba da rahoton cewa wani jirgin sama mara matuki na Isra’ila ya kai hari kan wasu a garin Abasan al-Kabira a ranar Litinin.

Tun bayan fara yakin kare dangi na Isra’ila a watan Oktoba na 2023, gwamnatin mamaye ta kashe akalla Falasdinawa 68,527 galibi mata da yara.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka China za ta dauki mataki idan takunkuman Iran sun shafi muradunta October 28, 2025 Rasha ta gargadi Faransa game da tura sojoji Ukraine October 28, 2025 Pezeshkian: Hadin Kai A Tsakanin Kasashen Gabas Ta Tsakiya Ba Zabi Ba Ne, Amma Dole Ne October 28, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Waje Kan Harkokin Siyasa Na Iran Ya Ce: Iran Ba Ta Kula Da Matsin Lamba October 28, 2025 Baqa’i: Dokar Majalisar Shawarar Musulunci Ce Ke Jagorantar Hadin Kan Iran Da Hukumar IAEA October 28, 2025 Sojojin Isra’ila Sun Kai Hare-Hare Kan Yankin Gaza A Matsayin Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta October 28, 2025 Al-Burhan: Sojojin Sudan Sun Janye Daga El-Fasher Saboda Kare Rayukan Fararen Hula October 28, 2025 Baqaei: Iran ta daɗe tana aiki don haɓaka zaman lafiya a duniya October 28, 2025 An Yi Girgizar Kasa Mai Karfi A Kasar Turkiya October 28, 2025 Ouattara Na Kasar Ivory Coast Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa October 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Ayatollah Khamenei : Iran na samun ci gaba duk da kalubale da dama

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya ce duk da kalubale masu yawa da ake fama dasu a fadin, kasar tana samun “ci gaba, kuma tana kokari,” ta hanyar juriya, da kuma tabbatar da adalci ga mutanenta.

“Mmatsaloli a fadin kasar suna da yawa, amma al’umma, kowace rana, da juriya, kuma bisa yardar Allah kasar tana ci gaba, tana kokari,” in ji shi.

Jagoran ya bayyana hakan ne yau Alhamis yayin da yake jawabi ga dubban jama’a a bikin tunawa da ranar haihuwar Sayyada Fatima Zahra (SA) a Tehran.

Ayatollah Khamenei ya tabo wani bangare game da yakin farfaganda bayan harin watan Yuni da Isra’ila da Amurka suka kai wa Iran, wanda ya tilasta wa makiya su tsagaita wuta.

“A yau, bayan yakin da muka gani, muna tsakiyar yakin farfaganda da kafofin watsa labarai na makiya,” in ji shi.

Ya soki wadanda ke ikirarin sake barkewar yaki, yana mai cewa “Wasu suna ta kara nuna yiwuwar sake gwabza yaki, wasu kuma suna kara ruruta hakan da gangan don sanya mutane cikin rashin tabbas da damuwa, amma da yardar Allah, ba za su yi nasara ba.”

Ayatollah Khamenei ya ce ‘’burin makiyi” shi ne share tasiri, manufofi, da ra’ayoyin juyin juya halin Musulunci.

“Tsawon shekaru, azalumai na duniya sun yi kokarin canza asalin addini, tarihi, da al’adu na kasar Iran, amma juyin juya halin Musulunci ya sa duk wannan kokarin bai yi amfani.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kyaftin Traoré : Yau Burkina ta zama misali a duniya December 11, 2025 Iran da Kazakhstan Sun rattaba hannun kan yarjeniyoyi da dama a tsakaninsu December 11, 2025 Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta December 11, 2025 Kasashen ECOWAS sun rage kudin sufirin jiragan sama a tsakaninsu   December 11, 2025 Dakarun IRGC 3 Sun Yi Shahada A wani Harin Ta’addanci A Kudancin Kasar Iran December 11, 2025 Hamas: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Bangaren Farko Na Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza December 11, 2025 Iran Ta Yi Tir Da Yanke Tallafin Da MDD Take Bawa Yan Gudun Hijiran Afganistan December 11, 2025 Ansarallah: Dole Ne Kasar Yemen Ta Tsarin Musulunci Na Kaiwa Ga Daukaka December 11, 2025 Shugaban Iran Ya Isa Astana Babban Birnin Kazakhstan December 11, 2025 ECOWAS ta bukaci waware batutuwa na siyasa ta hanyoyin lumana a yammacin Afirka December 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta soki Kasashe Masu Karfi Na Bawa Isra’ila Dama Ta Musamman Wajen Kai Hare-hare
  • Ben Gafir Ya Yi Sha Alwashin Rushe Kabarin Sheikh Izzuddin Alkassam
  • Ayatollah Khamenei : Iran na samun ci gaba duk da kalubale da dama
  • Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta
  • Hamsa: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Bangaren Farko Na Yarjeniyar Tsagaita Bude Wuta A Yankin
  • Kasashen Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5 
  • Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD
  • Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye
  • Nasarar Da Iran Ta Samu A Yakin Kwanaki 12 Kan HKI Yana Jawo Hankalin Kasashen Duniya
  • Antoni Gutress Ya Yi Allawadai Da Kutsen Da “Isra’ila” Ta Yi A Cibiyar Unrwa