2025-10-27@21:35:29 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3085
«dake bukatar kankara»:
Shugaba Alassane Ouattara, ya sake lashe zaɓen shugabancin ƙasar Ivory Coast wanda ya ba shi sabon wa’adin mulki a karo na huɗu. Ouattara mai shekaru 83, ya samu kashi 89.77 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, kamar yadda hukumar zaɓe ta ƙasa ta tabbatar a ranar Litinin. Tinubu ya gana da sabbin hafsoshin tsaro An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi Fiye da mutane miliyan tara ne suka cancanci kada ƙuri’a a zaben da aka gudanar a ranar Asabar, wanda aka gudanar cikin yanayi na fargaba, bayan da manyan abokan hamayyarsa biyu — tsohon shugaban ƙasa Laurent Gbagbo da tsohon shugaban Credit Suisse, Tidjane Thiam — aka hana su tsayawa takara. Sakamakon ya nuna cewa, duk da ƙarancin fitowar...
Wani rahoto da hukumar kula da kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta fitar a yau Litinin ya nuna cewa, ribar da manyan masana’antun kasar Sin suka samu cikin watanni tara na farkon shekarar 2025 da muke ciki, ta karu da kashi 3.2 cikin dari. A cewar hukumar ta NBS, masana’antun da ke samun kudaden shiga da suka kai akalla yuan miliyan 20 (kimanin dala miliyan 2.8) a shekara-shekara, sun samu jimillar ribar da ta kai yuan tiriliyan 5.37 a cikin watanni taran. A watan Satumba, ribar da manyan masana’antun ke samu ta farfado sosai, inda ta karu da kashi 21.6 cikin dari a kan na makamancin lokacin a bara, kamar yadda hukumar ta NBS ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare...
Da yake miƙa takardar naɗin, Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Alhaji Aminu Hammayo, ya taya sabon Sarkin murna, tare da kira gare shi da ya bi dokokin gwamnati da na ƙasa wajen gudanar da mulkinsa. Ya ce gwamnatin jihar ta tabbatar da naɗin ne bayan ta binciki cancanta, da halayya, da tarihin mulki na sabon Gung Zaar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro October 27, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno October 27, 2025 Manyan Labarai Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum October 26, 2025
Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta
A yau Litinin 27 ga Oktoba, kungiyar jigilar kayayyaki da sayayya ta kasar Sin ta ba da rahoton bayanan ayyukan jigilar kayayyakin dake bukatar kankara a watannin Yuni da Yuli da Agustan bana. Bayanan na nuna cewa, a karkashin jagorar manufofi da bukatun kasuwa, aikin jigilar kayayyakin dake bukatar kankara ya nuna samun ci gaba mai karfi tare da fadada girman kasuwa. Bayanan sun nuna cewa, jimillar da aka samu a wannan bangare a wadannan watanni 3 ta kai tan miliyan 117.3, wadda ta karu da kashi 4.72% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. A cikin watanni 3 na farko na wannan shekara, jimillar jigilar abincin dake bukatar kankara ta kai tan miliyan 309.3, wadda ta karu da...
A Ivory Coast sakamakon wucin gadi na zaben shugaban ya nuna cewa Shugaba Alassane Ouattara, wanda ke jagorantar kasar tun 2011, na kan lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga Oktoba, 2025 da gagarumin rinjaye. Rahotanni sun ce Ouatara ya samu kashi 89.77% na ƙuri’un da aka kaɗa, bisa ga sakamakon wucin gadi da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (IEC) ta fitar dazu. Duk da cewa sakamakon zaben bai ƙare ba tukuna, amma Ouatara da ke jagorantar tun 2011 yana kan hanyarsa ta zuwa wa’adi na huɗu a kan karagar mulkin ƙasar, bayan sake zaɓensa a 2015 da 2020. A wannan Litinin, Hukumar zaɓe ta ƙasa da ƙasa (IEC) ta sanar da cewa Alassane Ouattara, mai shekaru 83, na...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno October 27, 2025 Manyan Labarai Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum October 26, 2025 Labarai “Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA” October 26, 2025
Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta Ifopa faransa, ta nuna cewa kasha 84 cikin dari na ‘yan kasar basu gamsu ba da Emmanuel Macron a matsayin shugaban kasa. A cewar kuma wannan binciken da aka yi aka kuma wallafa a jaridar le Journal du Dimanche, kashi 16% ne kawai na mutanen Faransa suka “gamsu” da aikinsa a Fadar Élysée, yayin da kashi 84% suka nuna rashin gamsuwa da shi. Kiyasin farin jinin shugaban bai taba raguwa haka ba. Emmanuel Macron, wanda kwarin gwiwarsa ke ci gaba da durkushewa, yanzu ya ba wa kashi 54% na masu jefa kuri’arsa kunya a zagaye na farko na 2022. Rikice-rikicen da aka samu sakamakon rusa Majalisar Dokoki ta kasa, murabus, sannan sake nada Lecornu...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta nisanci nuna bangaranci a cikin ayyukanta musamman game da yadda Amurka da Isra’ila ke keta dokokin kasa da kasa. Da yake bayyana hakan mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta zama wakiliya game da hakkokin duk kasashe, yayin da yake yabon ka’idojin kungiyar. Ya bayyana hakan ne a lokacin da MDD ta cika shekaru 80 da kafuwarta. Mista Baghai Ya Yi Allah wadai Da ta’addancin Da Amurka Da Isra’ila Suka Yi Wa Iran A Watan Yunin Da Ya Gabata. Iran ma ta bi sahun wasu kasashe a duniya da a ranar Litinin din nan, 27 Ga...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka? October 27, 2025 Labarai Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote October 27, 2025 Labarai An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga October 27, 2025
Duk makarantu a fadin ƙasar Mali da ke Yammacin Afirka za su ci gaba da kasancewa a rufe daga ranar 27 ga Oktoba zuwa 9 ga Nuwamba, sakamakon tsananin ƙarancin man fetur da ya janyo tsaikon harkokin sufuri da na yau da kullum. Ministan Ilimi na ƙasar, Amadou Sy Savane ya sanar a ranar Lahadi cewa dukkan cibiyoyin ilimi za su dakatar da ayyukansu na tsawon makonni biyu saboda ƙarancin man fetur da ake fama da shi. Paul Biya mai shekara 92 ya lashe zaɓen Kamaru Sule Lamiɗo na neman takarar Shugaban PDP na Ƙasa Amadou Sy Savane ya shaida wa gidan rediyon gwamnati na ORTM cewa an shirya sake buɗe makarantu a ranar 10 ga watan Nuwamba. Tsawon makonni...
Kobi ta ce, an samu buƙata daga wajen mutane bakwai, inda aka tantance su domin fafata neman sa’a, daga baya mutane uku suka janye suka bar mutane huɗu domin fafata neman nasara a zaɓen. “Bayan gudanar da zaɓen, Birgediya Janar Marcus Kokko Yake (Rtd) shi ne ya yi nasara. “Za a gabatar da sakamakon nasarar da ya samu wa gwamnan domin amincewar da gabatar wa Gung-Zaar na farko takardar naɗinsa a matsayin Sarkin masarautar Zaar,” sanarwar ta shaida. Wannan matakin dai na zuwa ne yayin da al’ummar Sayawa ke zanga-zangar adawa da yunƙurin gwamnatin jihar Bauchi ta Bala Muhammad wajen naɗa musu wani a matsayin Sarkin masarautar Sayawa wato (Gung Zaar). Masu zanga-zangar dai sun bayyana...
Shugaba Paul Biya na Jamhuriyar Kamaru ya sake lashe zaɓen Shugaban Ƙasar domin fara wa’adi na takwas na shekara bakwai. Kotun Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ta sanar cewa Mista Paul Biya mai shekaru 92 ya samu nasara ne bayan ya samu 53.66 na kuri’un da aka jefa a yayin da babban abokin hamayyarsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35.19. Da haka biya zai ci gaba da mulki inda zai kammala sabon wa’adin yana dan shekara 99. Zuwa ƙarshen wa’adin, Biya wanda ya shekara 43 a gadon mulki tun 1982 zai cika shekara 50 a kan mulki. A halin yanzu shi ne shugaban kasa mai ci mafi tsufa a duniya. Shi ne kuma zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na biyu a tarihin...
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana matukar bakin ciki game da wannan lamarin. Gwamnan, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli ya fitar, ya yi ta’aziyya ga iyalan da suka rasu da kuma dukkan al’ummar Nafada, yana addu’ar Allah ya jikan mamatan. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum October 26, 2025 Labarai “Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA” October 26, 2025 Manyan Labarai Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano October 26, 2025
Duk da saukar farashin abinci a kasuwanni a sassan Najeriya, manoma na kokawa cewa sun shiga damuwa saboda asarar da suka tafka na kuɗaɗen da suka kashe wajen noma gonakinsu, lamarin da suka ce ya rage musu ƙwarin gwiwa su ci gaba da sana’ar. Wasu daga cikin manoman da wakilinmu suka zanta da su sun ce sun adana amfanin gona tun shekarar bara suna jiran farashi ya tashi, amma hakan bai faru ba, illa ƙara faduwa da farashin ya yi. A watan Satumban 2024 Gwamnatin Tarayya ta buɗe ƙofa na kwanaki 150 don shigo da hatsi kamar shinkafa, dawa, masara da alkama daga ƙasashen waje ba tare da biyan haraji ba, domin rage tsadar abinci. Amma wannan shigo da kaya...
Matatar Dangote ta sanar da shirin ƙara ƙarfin sarrafa man fetur daga ganga 650,000 zuwa miliyan 1.4 a kowace rana, wanda zai sanya ta zama babbar matatar mai mafi girma a duniya. Shugaban kamfanin, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana hakan a taron manema labarai a Legas, yana mai cewa faɗaɗawar na nuna ƙwarin gwuiwa ga tattalin arziƙin Nijeriya da hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu na mayar da ƙasar cibiyar sarrafa mai ta duniya. Dangote ya ce aikin faɗaɗawar “tana nuna amincewa da ƙarfin Afrika wajen tsara makomar makamashinta,” yana mai yabawa gwamnati bisa manufofi irin su Naira-for-Crude Policy da One-Stop Shop Initiative, waɗanda suka ƙarfafa zuba jari a ɓangaren mai. Ya kuma tabbatar da cewa matsalolin da suka...
A baya bayan nan, kundin da aka amince da shi yayin cikakken zama na hudu na kwamitin kolin JKS na 20, ya tanadi tsare-tsaren musamman na fadada bude kofofin kasar ga sassan waje, da dora muhimmancin gaske ga samar da sabon yanayin hadin gwiwar cimma moriyar juna. A halin yanzu, a hannu guda ana ganin zurfafar sabon zagayen juyin-juya-halin fasahohi, da sauyi a ci gaban masana’antu, a gabar da duniya ke bukatar bude kofa da rarraba gajiya sama da duk wani lokaci a baya. A daya hannun kuma, tsarin daukar matakan kashin kai da kariyar cinikayya na dada kamari, kuma duniya na fuskantar yanayin rashin daidaiton ci gaba da gibi a fannin jagoranci. A wannan yanayi mai sarkakiya da duniya...
Shugaban ƙungiyar ta ƙasa, Frank Ogunojemite, ne ya sanya rattaba hannunsa a wasiƙar kamar yadda Jaridar PUNCH, ta samu kwafinta. Shugaba ya bayyana cewa, ya kafa hujjar buƙatar soke tsarin, kan ƙalubalen da take fuskanta, na kashe kuɗaɗe masu yawa, musamman wajen safarar mayan Kwantainonin da ake shigoa da su daga ƙasashen da ke a Afirka ta Yamma Ya ce, wannan tsarin ya sanya a yanzu, ana yiwa masu safarar kaya zuwa cikin Tashar wani sabon cajin kuɗi da kuma jinkirin da suke samu, wajen shigar da kayan zuwa cikin Tashar. Ogunojemite ya buƙaci Hukumar da ta tabbatar da wanzar da tsarin a matsayin na bai ɗaya a ɗaukacin Tashishin Jiragen Ruwan ƙasar. “Muna gabatar da wannan buƙatar ce, domin...
Ya ƙara da cewa Basira ‘Yar Guda ta bayyana cewa za ta amince da aure ne kawai idan Idris ya mallaki gidansa na kansa, ba wanda yake haya ba. Wannan ne ya sa kotu ta dakatar da yanke hukunci domin bai wa Hisbah damar tabbatar da cewa an bi tsarin aure yadda ya dace da shari’ar Musulunci. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji October 26, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Masu Ƙananan Sana’o’i Biliyan 75 Domin Bunƙasa Kasuwancinsu October 26, 2025 Wasanni Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru October 26, 2025
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta doke babbar abokiya hamayyarta, Barcelona da ci 2 da 1 a filin wasa na Bernabeau. Wasan tsakanin manyan ƙungiyoyin biyu shi ne wasa mafi girma na hamayya a duniya. Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a Najeriya An kama mutum 25 kan zargin shirya auren jinsi a Kano Madrid ta karɓi baƙuncin Barcelona a gasar Laliga a wasan mako na 10. Wasan ya ƙayatar, inda kowace ƙungiya ta nuna bajinta tare da murza leda yadda ya kamata. Ɗan wasan gaban Real Madrid, Kylian Mbappe ne ya fara jefa ƙwallo a minti na 22, yayin da Fermin Lopez ya warware wa Barcelona a minti na 38. Kafin tafiya hutun rabin lokaci, ɗan...
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran a shirye take ta shiga tattaunwa ta diflomasiyya da Amurka domin cimma “mafita kan batun nukiliya cikin mutunta juna. “Iran ta sha sanar da cewa ba ta taba yin watsi da diflomasiyya ba kuma,” in ji Araghchi a wata hira da akayi da shi. “Ba za mu yi sulhu kan abinda ya kasance hakkin mutanen Iran ba kuma ba za mu lamunci mamaye da cin zarafi a kan mutanen Iran ba; duk da haka, a shirye muke mu fuskanci kowace mafita mai hikima,” in ji Araghchi. Ya sake nanata cewa Iran ba ta bukatar makamin nukiliya. Ya ce Tehran ta shiga tattaunawa da Washington game da shirin makamashin nukiliyarta don ba...
A birnin Paris, an gudanar da wata zanga-zanga a filin jirgin saman Roissy-Charles-de-Gaulle game da shigar da makamai da kayan aikin soja na Faransa zuwa Isra’ila. An shirya zanga-zangar ne bisa kiran wasu kungiyoyi da nufin bayyana rawar da Faransa ke takawa wajen samar wa sojojin Isra’ila makamai da kayan soji, musamman ta babban filin jirgin saman kasa da kasa na Roissy-Charles-de-Gaulle. A cikin sanarwar manema labarai, da suka fitar masu shirya zanga zangar sun yi Allah wadai da jigilar kayan aikin sojan inda suka nemi a dakatar da duk kayan da Faransa ke fitarwa wadanda za su iya taimakawa wajen kai hare-haren sojojin Isra’ila. Wannan yunkurin ya zo ne bayan da gidan yanar gizon bincike na Faransa mai suna...
Sai dai ya yabawa masu ba da agajin gaggawa, da jami’an tsaro da kuma ‘yan sa-kai da suka yi aiki tuƙuru wajen ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su, tare da ba su agaji, yana mai cewa ɗaukin gaggawan da suka kai ya taimaka wajen rage munin ibtila’in. A yayin da take addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa, ƙungiyar Gwamnonin Arewan ta bada tabbacin cewa za ta ci gaba da haɗa hannu da hukumomin tarayya dana jihohin da abin ya shafa don ƙarfafa tsarin rigakafi da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin al’umma. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Masu Ƙananan Sana’o’i Biliyan 75 Domin...
Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa kwamitin shugaban ƙasa kan ba da tallafi ya ƙaddamar da rabon naira miliyan 50, inda mutum miliyan 1 za su samu naira dubu hamsin kowanensu tare da wasu shirye-shirye na bunƙasa ƙananan sana’o’i. Ya ƙara da cewa ƙanana da matsaƙaitan sana’o’i a Jihar Katsina za su samu 250,000 daga gwamnatin tarayya wanda zai taimaka wa sana’o’insu wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatinsa tana aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya wajen ƙirƙirar ayyuka, wanda yanzu haka an samar da kuɗaɗai har naira biliyan 5.5, inda aka raba biliyan ɗaya ga mutane 701 a faɗin jihar. Gwamna Raɗɗa...
Dasuki, wanda shine shugaban rikon kwarya na Shirin Makomar Matasa A Yanzu, wani shiri na hada matasa da harkokin siyasa da aka kaddamar a ranar 1 ga Oktoba, 2025 a Abuja, ya bayyana cewa sanarwar shirin na cewar kashi 70% na kujerun majalisar wakilai a zaben 2027 su kasance na ‘yan Nijeriya kasa da shekaru 40, ba kawai magana ce ta fafutuka ba, har ila yau kalubale ne ga shugabanni. Matakin Dasuki ya kasance wani muhimmin lamari a farfajiyar siyasar Najeriya, inda ’yan siyasa kalilan ke ja da baya daga mukaman su. Sanarwar sa an fassara ta sosai a matsayin wakilcin gwagwarmayar adalci tsakanin tsararraki wanda ya taimaka wajen jagoranta, wanda ke nufin rage gibin da ke tsakanin tsofaffi...
“Yayin da ake gudanar da samamen bisa ga bayanan sirri daga wasu mazauna garin Farin Ruwa da ke karamar hukumar Shanono, jami’an hadin gwiwa na rundunar yaki da ta’addanci ta rundunar da kuma jami’an rundunar da ke Shanono, sun gudanar da samamen na kwarewa a ranar Juma’a, 24 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 02:00 na dare. Hakan ta sa, an samu nasarar kama wasu mutane biyu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne,” in ji sanarwar. Kwamishinan ‘yansanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa al’ummar Farin Ruwa, yana mai bayyana yadda suka bayar da bayanan sirrin a matsayin muhimmin abu ga nasarar aikin. Ya bukaci mazauna yankin da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani...
Wannan nasara mai ban mamaki ta sa kungiyar Niger Tornadoes ta koma matsayi na biyu a teburin gasar, inda yanzu take da maki 17 a kasan Nasarawa United. Hakazalika, sakamakon ya bar Kano Pillars a cikin mawuyacin hali a gasar yayin da ta ke matsayi na 19 da maki 8 kacal. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus October 25, 2025
“Ban taba tunanin zan zama taurariya a duniya ba.” Daga Yobe Zuwa Fagen Duniya An haife ta a Jihar Kano kuma ta tashi a Yobe, labarin Nafisa ba shi da wuya kamar yadda yake da ban sha’awa. Mahaifinta ya rasu tun tana jaririya, kuma mijin mahaifiyarta mai suna Alhaji Yusuf Umar Kaigama ya rene ta, wanda ya dasa mata dabi’u na tarbiyya da azama. Tana kuma ɗauke da tsatson sarautar zuriyar sarakuna biyu masu daraja ta masarautar Kano, wato Sarkin Kano Ibrahim Dabo da Sarki Abdullahi Maje Karofi. Amma bayan jinin sarautar da take ɗauke dasu, yunwar ta na neman ilimi ya sa ta zama daban. A yanki da matsalar staro ta yi katutu wanda kuma yake dakushe duk wani...
Wakilan kasar Sin da na Amurka sun yi taro da safiyar yau Asabar don tattaunawa kan batutuwan tattalin arziki da cinikayya. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis da ta gabata, wani mai magana da yawun ma’aikatar harkokin kasuwanci ta kasar Sin, ya bayyana cewa, bangarorin biyu za su gudanar da shawarwari kan muhimman batutuwa game da huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, bisa muhimmiyar yarjejeniyar da shugabannin kasashen biyu suka cimma yayin da suka tattauna ta wayar tarho a wannan shekarar. Mataimakin firaministan kasar Sin kuma memba na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin He Lifeng ne ke jagorantar tawagar kasar ta Sin a tattaunawar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)...
Matakatin shugaban Amurka Donald Trump na nada tsohon fira ministan birtaniya Tony Blair a matsayin mai ruwa da tsaki cikin alamuran gaza bayan dakatar da bude wuta ya fuskancin turjiya daga kasashen larabawa da kuma na musulmi, Balair shi ne mutum daya da aka ayyana sunansa daga cikin mambobin kwamitin tabbatar da sulhu da trump ya bada shawara na sanya ido bayan kawo karshen yaki tsakanin bangarorin biyu. Akwai damuwa sosai da shakku kan kasancewar Blair daga cikin masu ruwa da tsaki a alamuran yankin, musamman bayan goyon bayan da ya nuna wajen kai wa iraki hari tare da tsohon shugaban Amurka na wancan lokacin a shekara ta 2003 ,a gefe daya kuma yana kare Isra’ila, jamai’an diplomasiyan larabawa sun...
A gun cikakken zaman taro na hudu na kwamitin kolin JKS na 20 da aka gudanar tun daga ranar 20 zuwa 23 ga wannan wata a nan birnin Beijing, an yi bincike da zartas da shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15, inda aka gabatar da jagora da burika kan yadda za a raya kasar a wannan lokaci, kana an tsara taswirar bunkasa kasar Sin a shekaru 5 mazu zuwa. Ga duk duniya, shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar ba shiri na kasar Sin kawai ba ne, kuma ba kasar Sin ba ce wadda ta fara tsara shirin, amma kasar Sin ita kadai ta kiyaye aiwatar da irin shirin. Sirrin tafiyar da harkokin kasar...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakin gaggawa a harkar tsaron sararin samaniya, domin hana ’yan ta’adda na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare. Zulum, ya faɗi haka ne a ranar Juma’a a garin Mafa, bayan wani hari da Boko Haram suka kai. Sauke Hafsoshin Tsaro: Za a yi wa Janar-Janar 60 ritaya daga aiki ’Yan sanda sun taimaka wa ’yan daba rusa gidaje — Al’ummar Shendam Ya ce, “Babban abin da nake son magana a kai shi ne amfani da jirage marasa matuƙa. An shaida min cewa sun yi amfani da su a Dikwa, kuma hakan abu ne mai tayar da hankali.” Gwamnan ya bayyana cewa yawaitar irin waɗannan jirage a...
Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, wanda Kwamishinan Ruwa, Alhaji Aminu Dodo Iya, ya wakilta, ya jaddada cewa sarautun gargajiya su ne ginshiƙin zaman lafiya da ci-gaban al’umma. Ya ce shugabannin gargajiya na taka rawa wajen haɗa kan jama’a da gwamnati, tare da tabbatar da ɗorewar cigaba a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales October 25, 2025 Manyan Labarai Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce October 25, 2025 Labarai Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa October 25, 2025
Ya ƙara da cewa cibiyar Centre for Energy Research and Training (CERT) ta jami’ar ABU, wadda aka kafa tun 1976, tana aiki tare da IAEA da kuma ƙasashe kamar Amurka, da Rasha da China, kuma ba ta taɓa gudanar da wani shiri na makamin nukiliya ba. A cewarsa, “ABU tana ci gaba da sadaukar da kai wajen inganta kimiyya da fasaha don ci gaban ƙasa da kuma tabbatar da zaman lafiya ta hanyar amfani da makamashin nukiliya ta hanya mai amfani da jama’a.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi October 25, 2025 ...
Mataimakin babban kwamandan rundunar sojin Iran kan hadin gwiwa ya jaddada cewa: Sojojin Iran a shirye suke su fuskanci kowace barazana Mataimakin Babban Kwamandan Rundunar Sojin Iran kan Hadin Gwiwa, Rear Admiral Habibullah Sayyari, ya ce: An zabi Sojojin Iran daga cikin mafi kyawun matasa a kasar kuma suna shirye su fuskanci kowace barazana. A gefen bikin bude gasar cin kofin duniya ta 4 ta sojojin masu harba kibau (SIZM 2025), wadda rundunar sojin sama ta shirya a kungiyar masu harbi a ranar Juma’a da yamma, Rear Admiral Sayyari ya yi magana da manema labarai game da matakin shirye-shiryen Sojojin da kuma rawar da wasanni ke takawa wajen inganta karfinsu. Ya jaddada cewa, “Wasanni suna da matukar muhimmanci ga lafiyar...
Sauyin shugabannin tsaro dai ya nuna matakin da Tinubu ke ɗauka wajen sake fasalin tsaro, amma kuma ya buɗe sabon babi na tattaunawa kan yadda ake kula da tsofaffin hafsoshin da suka ba ƙasa hidima tsawon shekaru. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi October 25, 2025 Manyan Labarai Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe October 25, 2025
Mazauna unguwar Tudun Wada da ke garin Shendam a Jihar Filato sun zargi wasu jami’an ’yan sanda da ba wa ’yan daba kariya wajen rusa gidajensu. Shaidu sun ce sama da ’yan sanda 100 ɗauke da makamai ne suka isa yankin da misalin karfe 5 na safiyar Laraba, suka ba wa wasu ’yan daba kariya yayin da suke lalata gine-ginen jama’a Lamarin ya jawo zanga-zangar da mazauna yankin, ciki har da mata da yara, suka gudanar don nuna adawa da abin da suka kira “cin zarafi daga jami’an tsaro.” Mazaunan sun bayyana cewa rushewar gidajen ta faru ne da haɗin gwiwar iyalan Fuanter duk da cewa ana shari’a a gaban kotun ɗaukaka ƙara kan mallakar filayen. Sun ce suna da...
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin, ya bayyana cewa su na nazarin dokoki guda 69 da kuma buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da kuma ƙudirin ƙirƙirar ƙananan hukumomi 278 bisa ga tsarin kundin mulkin 1999. Barau, wanda shi ne shugaban Kwamitin Bita na Tsarin Mulki a majalisar dattawa, ya bayyana hakan ne a taron haɗin gwuiwa da kwamitocin majalisar dattawa da kwamitocin majalisar wakilai kan gyare-gyaren dokokin tsarin mulki da suka gudanar a Lagos. Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu Firimiyar Nijeriya: Barau FC Ta Samu Nasarar Farko A Tarihinta Ya jaddada cewa an dauki lokaci mai tsawo wajen tattaunawa da al’umma da masu ruwa-da-tsaki da ƙungiyoyi daban-daban, domin kawo waɗannan ƙuduri...
Rashin Biyan Yan-fansho Bisa Lokaci Ta tabbata a lokacin mulkin Kwankwaso, “yan fansho a Kano, kan jira tsawon Watanni zuwa Shekaru ba tare da an biya su hakkokinsu na barin aiki ba. Haka ɗan-jummai Ganduje, yakan dan fara biyan hakkokin “yan fanshon, sai kuma a ga ya watsar. Sai a dauki tsawon lokaci yana ɓaɓatun za a ci gaba da biya, amma sai a ji shiru. Sai aka wayi gari karɓar fansho, musamman giratuti, ya zama tamkar tafiya Lahira, yau ne? Gobe ne? Babu wata cikakkiyar amsa!. Haƙiƙa kwata-kwata babu tausai, mutane sun kwashe akasarin Shekarunsu na haihuwa suna masu hidimtawa ƙasa dare da rana, cikin yanayi na sanyi, ruwan sama da garjin rana, dole ne su fito, su aje...
Kungiyar kwallon kafa ta “Futsal” ta matan Iran ta zura kwallaye 14-0 a wasan da ya hada ta da takwararta ta kasar Bahrain mai masaukin baki. A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai aka bude wasannin nahiyar Asiya na kwallon kafar Futsal a kasar Bahrain. A wasan farkon, kungiyar ta Iran ta sami nasara akan takwararta ta Hong kong ta hanyar zura kwallaye shida. Wasa na biyu da Iran din ta yi shi ne da kungiyar kasar Bahrain, da ta sami galaba da kwallaye 14 da 0. ‘Yan wasan na Iran sun kunshi Fatima Shukrani, Niyayash Rahmani, Dhanaz Bakiri, Haidis Yari da kuma Narjis Amir Muhsini. Ya zuwa yanzu dai kungiyar kwallon Futsal ta Iran tana da maki...
Ya bayyana cewa sarakuna suna taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba, musamman a fannin ilimi, inda ya ce zai tabbatar yara sun koma makaranta. Haka kuma, ya ce zai goyi bayan gwamnati a ɓangaren kiwon lafiya da tsaro, domin inganta rayuwar jama’a. Sabon Sarkin, wanda kuma shi ne shugaban hukumar kula da ilimi a matakin farko (SUBEB) ta Jihar Bauchi, ya bayyana farin cikinsa da godiyarsa ga Allah da Gwamna Bala Muhammad saboda wannan dama da ya samu. Ya yi alƙawarin yin aiki tuƙuru domin ci gaban masarautarsa da Jihar Bauchi gaba ɗaya, tare da kira ga jama’ar Duguri da su haɗa kai wajen gina masarautar. “Mu mutanen Duguri a shirye muke mu taimaka wa gwamnati a duk abin...
Ya ce Hukumar Binciken Ƙasa ta Nijeriya (NGSA) za ta jagoranci kwamitin, domin ita ce ke da ikon tattara bayanan ma’adinai na ƙasa baki ɗaya. “NGSA ta yaba da ƙoƙarin gwamnatin Jihar Kaduna bisa gaskiya da bayyana bayanai, tare da yin kira da a gudanar da binciken tabbatarwa mai zaman kansa,” in ji shi. Ya ƙara da cewa wannan haɗin gwiwar zai ƙara goyon bayan masu zuba jari a sashen ma’adinai na Nijeriya, tare da faɗaɗa bayanan kimiyyar ƙasa, wanda zai taimaka wajen haɓɓaka tattalin arzikin ƙasa ta hanyar albarkatun ma’adananta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Yayansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri October 24, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya October...
Jam’iyyar ADC ta nemi Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana wa ’yan Najeriya ainihin dalilin da ya sa ya sauya hafsoshin tsaron ƙasa ba zato ba tsammani. Aminiya ta ruwaito yadda shugaban ƙasa ya sauya hafsoshin tsaron da ya naɗa shekaru biyu da suka wuce. Gwamnan Bauchi ya naɗa ɗan uwansa a matsayin sabon Sarkin Duguri ’Yan sanda sun kama ɗalibi da ya soki Gwamnan Neja A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ya ce jam’iyyar ta damu ganin yadda aka yi sauyin ba zato ba tsammani bayan jita-jitar yunƙurin juyin mulki. “Ko da yake shugaban ƙasa yana da ikon yin irin waɗannan sauye-sauye, amma mum damu da wannan mataki biyo bayan...
Gwamna Raɗɗa ya ƙara da cewa wannan zaman sulhu da ɓarayin daji da ake yi al’umma ce take yi ba wai gwamnati ba, ita gwamnati tana iya yin sulhu da ɗan bindigar da ya tuba ya yarda da zaman lafiya kuma ya ajiye mukaminsa. A cewarsa, rawar da gwamnati take iya takawa shi ne, ta ƙarfafa zaman lafiya, sannan ta tabbatar an bi doka da oda a cikin al’umma. Ya ce abubuwa da gwamnati ke lura da su shi ne, al’umma ta mori zaman lafiya domin bunƙasar tattalin arziki da sauran su. Tunda farko a jawabinsa, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Hon. Nasiru Mu’azu Danmusa ya bayyana cewa Gwamna Raɗɗa ya rage ƙarfin harkokin rashin tsaro a Jihar Katsina....
Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), ya jagoranci wani taron karawa juna sani a ranar 27 ga watan Augusta, domin jin ra’ayoyin wadanda ba ‘yan jam’iyyar ba, dangane da shawarwarin da kwamitin kolin JKS ya gabatar game da tsara shirin raya kasa na shekaru 5 karo na 15, da ke da nufin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar. (Fa’iza Muhammad Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Shugaban Kasar Sin Zai Halarci Taron APEC Da Ziyarar Aiki A Korea Ta Kudu October 24, 2025 Daga Birnin Sin Fahimtar Sabon Tunani: Samar Da Wadata Ga Dukkan Jama’a Ta Daidaita Gibin Dake Tsakanin Hamshakai Da...
Hammayo ya shawarce shi da ya gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci tare da haɗa kan ƙabilu don tabbatar da zaman lafiya. A baya-bayan nan ne Gwamna Bala Mohammed ya rattaba hannu kan dokar kafa sabbin masarautu 13 a jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya October 24, 2025 Manyan Labarai Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa October 24, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu October 24, 2025
Ƙungiyar Arewa Unity Women in Media, ta kai tallafi Makarantar Masu Buƙata ta Musamman da ke Gombe, domin taimaka wa gwamnati wajen kula da rayuwar ɗaliban da ke da buƙata ta musamman. Tallafin ya ƙunshi gidajen sauro, bargo da tabarmi, wanda aka raba wa ɗaliban a lokacin bikin miƙa kayan tallafin. ’Yan sanda sun kama ɗalibi da ya soki Gwamnan Neja ’Yan sanda sun sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa Shugabar ƙungiyar, Lois Hassan daga GMTV Gombe, tallafin na da nuna kulawa da ƙauna ga ɗaliban, tare da tabbatar musu cewa al’umma ba ta manta da su ba. Ta ƙara da cewa ƙungiyar Arewa Unity Women in Media ƙungiya ce mai zaman kanta da ke gudanar da...
Tawagar kamfanin na Rano Air a wurin ganawa da gwamnan, ta haɗa da Babban Manajan (Ayyuka), Abah O. Godwin; da Accountable Manager Alhaji Lawal Sabo Bakinzuwo; da Shugaban Sashin Ayyuka na ƙasa Bashir Abdullahi Wudilawa; da Shugaban Sashin Bunƙasa Harkokin Kasuwanci na kamfanin, Auwal Sulaiman Ubale. Jami’an kamfanin sun tabbatarwa gwamnan cewa kamfanin na Rano Air zai samar da nagartacciyar hidima abar dogaro, mai inganci kuma mai haba-haba ga kwastomomi, ta yadda za a samu sauƙin tafiye-tafiyen kasuwanci da bunƙasa harkokin tattalin arziki a faɗin jihar da Arewa Maso Gabas baki ɗaya. “Gwamna Inuwa Yahaya ya yi maraba da wannan ci gaba, inda ya bayyana hakan a matsayin wata shaida kan yadda Jihar Gombe ke da zaman lafiya da kwanciyar...
Shugaba Tinubu, ya gode wa tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, da sauran tsoffin hafsoshin bisa gudunmawar da suka bayar. Ya kuma bukaci sabbin hafsoshin da su tabbatar sun cancanci nadin da aka musu ta hanyar nuna ƙwarewa, haɗin kai wajen tsaron Nijeriya. “Shugaban ƙasa ya bukaci sabbin hafsoshin tsaro da su tabbatar da cewa sun cancanci nadin da aka musu ta hanyar nuna ƙwarewa, faɗakarwa, da zumunci wajen tsaron ƙasa,” in ji sanarwar. Sanarwar ta bayyana cewa dukkanin sabbin naɗin za su fara aiki nan take. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi October 24, 2025 Labarai Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025, Injiniya Abdullahi Sule October 24, 2025...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC Uku Da Wasu October 24, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji October 24, 2025 Manyan Labarai Nnamdi Kanu Ya Sake Bayyana A Kotu Ba Tare Da Lauya Ba, Zai Kare Kansa Da Kansa October 24, 2025
Wasu jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) guda uku da ke hanyarsu ta zuwa jihar Anambra domin shirye-shiryen zaben gwamna na ranar 8 ga Nuwamba, sun shiga hannun ‘yan bindiga a jihar Kogi. Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa an yi garkuwa da jami’an ne a ranar Talata, a ƙauyen Aloma da ke ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi. Tinubu Ya Rantsar Da Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC Sienna da suka ke tafiya da ita ya bayyana a cikin wani kiran waya cewa ƴan bindigar sun tare hanya, suka buɗe musu wuta, har suka lalata gilashin gaban motar, lamarin da ya tilasta...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƙarfin Niyyar Manzon Allah (SAW) Da Matakinsa Na Aƙlul A’ala October 24, 2025 Manyan Labarai Gobara Ta Tafka Ɓarna A Kasuwar Shuwaki, Ta Ƙona Fiye da Rumfuna 500 A Kano October 24, 2025 Manyan Labarai Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu October 24, 2025
“Shirin gwamnan na aiwatar da sabon tsarin albashi duk da ƙalubalen tattalin arziki ya nuna tausayinsa, gaskiya, da girmama kimar ma’aikata,” in ji shugabannin kungiyoyin. Kungiyoyin sun kuma yaba da kokarin gwamnatin wajen gyara da inganta fannonin ilimi da kiwon lafiya inda suka bayyana gyaran da sabunta azuzuwan karatu a dukkan kananan hukumomi 23, amincewa da tsarin ritaya bayan shekaru 65 ko shekaru 40 na aiki ga malamai, da kuma dawo da sama da naira miliyan 500 na ajiyar ( ENDWELL) da aka rike a baya, a matsayin muhimman nasarori. Ma’aikatan sun kara jinjina wa dawowar tsarin biyan gudunmawar adashin gata na malaman makaranta wato (ENDWELL) na kowane wata, inda suka bayyana cewa tsarin yana taimakawa wajen inganta...
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa matasa dubu ɗaya (1,000) za su samu horo kan tsaron yanar gizo (cyber security) da fasahar binciken dijital (digital forensics) ta hanyar Cibiyoyin Koyon Fasahar Dijital ƙarƙashin Shirin Renewed Hope Initiative (RHI) a Jihar Nasarawa. Uwargidan Shugaban Ƙasan ta bayyana haka ne yayin bikin kaddamarwa da miƙa Cibiyar Koyon Fasahar Dijital (Digital Learning Center) a Lafia da wasu jihohin ƙasar. Sanata Oluremi Tinubu ta ce, shirin horon matasan wanda za a rika gudanarwa a kowane mako daga yanzu har zuwa watan Disamba na shekara mai zuwa, yana da nufin yakki da laifukan yanar gizo (cyber crimes) da kuma ƙarfafa matasa su samu ƙwarewa ta yadda za su dogara da kansu a...
Uwargidan Shugaban Ƙasa ta Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta kaddamar da Dijital E-Learning Library a Gusau, Jihar Zamfara — ɗaya daga cikin jihohi goma da aka zaɓa a faɗin ƙasar domin aiwatar da wannan muhimmin aiki ƙarƙashin Shirin Renewed Hope Initiative (RHI) tare da haɗin gwiwar Hukumar bunkasa ayukkan fasaha ta kasa (NITDA). A yayin bikin kaddamarwar, Sanata Tinubu ta bayyana cewa wannan aiki ba wai game da fasaha da kwamfuta kawai ba ne, amma yana nufin ƙarfafa matasa, rage gibin fasaha (digital divide), da kuma buɗe sabbin ƙofofin ilimi da ƙirƙira ga al’ummar Zamfara da ma Najeriya baki ɗaya. Uwargidan Shugaban Ƙasa, wacce Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta wakilta, ta bayyana cewa ilimi shi ne...
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa gobara ta lalata rumfuna 529 daga cikin rumfuna na wucin gadi a Kasuwar Shuwaki da ke ƙaramar hukumar Gari, Jihar Kano. Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Kano. A cewarsa, hukumar ta samu kiran gaggawa misalin ƙarfe 3:25 na rana daga Abdulmalik Muhammad na ofishin kashe gobara na Gari, yana sanar da aukuwar gobara a kasuwar. Ya bayyana cewa, da zarar sun samu bayanin, hukumar ta aika jami’ai da motocin kashe gobara zuwa wurin domin kashe wutar tare da hana ta yaduwa zuwa sauran sassan kasuwar. Saminu ya ce yankin kasuwar yana da fadin kimanin...
Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa (NEC) ta amince da shirin Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu na sake fasalin da kuma zamanantar da cibiyoyin horar da jami’an tsaro a faɗin ƙasar. Wannan mataki ya biyo bayan taron majalisar na 152 da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda Ministan Tsare-tsaren Kasafi da Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya gabatar da jawabi kan dabarun cimma burin Shugaban Ƙasa na samar da tattalin arzikin da ya kai darajar dala tiriliyan guda. An kafa kwamitin da Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ke jagoranta don tsara cikakken tsari na gyaran da sabunta cibiyoyin horar da jami’an ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro cikin wata guda. Mambobin kwamitin sun haɗa da gwamnonin jihohin...
Baya ga haka, sabon ginin ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma ta Jihar Zamfara da aka sake ginawa da kuma sabon ginin kwalejin fasaha da kimiyya na Jihar Zamfara (ZACAS) da aka gyara, sun yi matuƙar haskaka Gwamnatin Dauda Lawal. Har ila yau, jihar ta samu gagarumin ci gaba wajen inganta fannin kiwon lafiya ta hanyar zuba jari, wajen gyarawa da inganta asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a faɗin jihar. A ƙoƙarinsa na rage mace-macen mata masu juna biyu da mace-macen jarirai, an ɗauki ma’aikatan kiwon lafiya tare da horar da su da sayen magunguna da kayan aiki da ɓullo da ayyukan kula da lafiyar mata da ƙananan yara kyauta. Sannan, an gyara asibitin ƙwararru na...
Baya ga haka, sabon ginin ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma ta Jihar Zamfara da aka sake ginawa da kuma sabon ginin kwalejin fasaha da kimiyya na Jihar Zamfara (ZACAS) da aka gyara, sun yi matuƙar haskaka Gwamnatin Dauda Lawal. Har ila yau, jihar ta samu gagarumin ci gaba wajen inganta fannin kiwon lafiya ta hanyar zuba jari, wajen gyarawa da inganta asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a faɗin jihar. A ƙoƙarinsa na rage mace-macen mata masu juna biyu da mace-macen jarirai, an ɗauki ma’aikatan kiwon lafiya tare da horar da su da sayen magunguna da kayan aiki da ɓullo da ayyukan kula da lafiyar mata da ƙananan yara kyauta. Sannan, an gyara asibitin ƙwararru na...
Kazalika, har yanzu batun tsohon shugaban Majalisar Wakilai wato Salisu Buhari, na 1999, na yin amfani da Takardun karatu na bogi da ya yi iƙirarin ya samo daga Jama’iar Toronto, baƙalar na ci gaba da kafa babban misali, a ƙasar. Badaƙalar ta sa, ba ta tsaya nan ba, ya kuma ƙaryar shekarun na haihauwa, domin kawai, ta tsaya takarar siyasa, a wancan lokacin, wanda kuma ya nuna turjiya daga sauka daga muƙamin na nsa duk da ɗimbin hujjojin da suka bayyana a kansa, inda bayan komai ya bayyana ƙarara, ya sauka daga kan muƙamin shugabancin Majlisar a 2000, ya kuma ɓarke da kuka a Majalisar, ya amsa cewar, Takardunsa na bogi ne. Haka ita ma, tsohuwar ministan kuɗi Kemi Adeosun,...
Sashen haƙar ma’adinai na Cote d’Ivoire da ke samun ci gaba cikin sauri zai fuskantar matsala da tsaiko kafin zaɓen shugaban ƙasa na ranar Asabar, yayin da Shugaba Alassane Ouattara ke neman wa’adi na hudu. A cewar Reuters, haƙar ma’adinai muhimmin ɓangare ne daga cikin ayyukan da Ouattara yake mayar da hankali a kansu, don haɓaka tattalin arzikin kasar wadda ita ce ta farko wajen samar da koko a duniya. Tun lokacin da ya hau mulki a 2011, ayyukan samar da zinare suka habaka daga kimanin tan 10 na metric a 2012 zuwa fiye da tan 58 a 2024, tare da burin kaiwa tan 100 nan da 2030. Majiyoyi uku na masana’antar haƙar ma’adinai sun ce masu hakar ma’adinai suna...
Sakatare-Janar na kwamitin hadin gwiwa na yankin Gulf Jassim Al-Badawi ya yi kakkausar suka kan amincewa da wasu kudirori guda biyu a majalisar Knesset ta Isra’ila da ke da nufin kakaba ikon Isra’ila kan yankin yammacin kogin Jordan da ta mamaye. A rahoton talabijin ta Aljazeera, Jassim Al-Badawi a cikin wata sanarwa a jiya Alhamis ya jaddada cewa, matakin da majalisar Knesset ta Isra’ila ta dauka, wani mataki ne da ya saba wa kudurorin kasa da kasa, da kuma kawo cikas ga kokarin da kasashen duniya ke yi na samun zaman lafiya mai dorewa. Haka nan kuma ya jaddada cewa ayyukan gina matsugunan da gwamnatin sahyoniyawan suke yi a fili take ga hakkokin tarihi na al’ummar Palastinu da dokokin kasa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cikin ‘yan watannin da suka gabata, an sake ganin karuwar hare-haren Boko Haram da ISWAP musamman a yankin Arewa maso Gabas. Kazalika, ko a kwanan nan ma anga irin wadannan hare hare. Wadannan hare-haren sun fi karkata kan sansanonin sojoji, inda ake samun asarar rayuka da dama, da kuma lalata kayan aikin gwamnati. Rahotanni daga Borno da Yobe da ma wasu sassan kasar nan sun nuna yadda ‘yan ta’adda suka sake samun karfi wajen kai hare-hare cikin dare, tare da amfani da dabaru irin na soji da kuma kayan yaki na zamani. Wannan lamari ya jawo tambaya daga al’umma: shin wannan karin hare-hare alama ce ta dawowar kungiyar Boko Haram da...
Wasu daga cikin sojojin sun ji rauni amma suna cikin ƙoshin lafiya. Haka kuma, wasu gine-gine da motocin da ke kusa sansaninin sun lalace yayin artabun. Rundunar sojin ta yaba da jarumtar dakarunta, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da kare ƙasar daga duk wata barazana. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Rantsar Da Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 23, 2025 Manyan Labarai Yadda DSS Suka Kama Masu Safarar Makamai Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kaduna October 23, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas October 23, 2025
Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya rantsar da Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). An gudanar da bikin rantsarwar ne a ranar Alhamis a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, mako guda bayan Majalisar Dattawa ta amince da nadinsa a ranar 16 ga watan Oktoba. Sanarwar Bayan Taron Jks: Mene Ne Sirrin Kwarin Gwiwar Kasar Sin? Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Waɗanda Fashewar Tankar Mai Ta Rutsa Da Su A Neja A yayin taron, Shugaba Tinubu ya buƙaci Farfesa Amupitan da ya tabbatar am gudanar da sahihancin zaɓe a Nijeriya tare da inganta INEC domin tabbatar da gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci. An tabbatar da naɗin Amupitan bayan Majalisar Dattawa ta...
An zargi mayaƙan Boko Haram da ISWAP da kai hare-hare wasu yankuna biyar da ke Jihohin Borno da Yobe. Sun kai hare-haren ne garuruwan Mafa, Dikwa, Marte, da Ajiri a Jihar Borno, da kuma Katarko a Jihar Yobe. Jami’an tsaro sun kama Sowore saboda shirya zanga-zanga DSS ta cafke mutum 3 kan zargin sayar wa ’yan bindiga makamai a Kaduna Rahotanni sun bayyana cewa ’yan ta’addan sun fara kai hari wani shingen sojoji da ke Mafa, sannan suka sace makamai da sabbin babura da sojoji ke amfani da su. Wata majiyar tsaro ta ce: “Sun zo da yawa kuma ɗauke da muggan makamai. Sun sace makamai da baburanmu. Yawansu dana gani abun mamaki ne.” Ba a tabbatar da adadin sojojin...
Kungiyar gwagwarmyar ta Hamas ta yi maraba da matakin da kotun kasa da kasa ta ICJ ta dauka na karyata ikirarin da HkI ta yi kan hukumar bada agaji ga falsdinawa yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya . Gwamnatin Sahyuniya ta yi ikirarin karya kan hukumar ta UNRWA inda kafafen yada labarai na kasashen turai suka yayata ba tare da wani bincike ba kan gaskiyar lamarin, inda kotun ta ICJ ta majalisar dinkin duniya ta mayar da martani kan ikirarin karya da isra’ila ta yi kuma ta kare hukumar UNRWA ta bayyana irin ayyukan jinkai da take yi da gudanarwa ga alummar falasdinu. Babban kotun duniya ta umarci isra’ila da ta bada dama a shiga da kayayyakin agaji zuwa...
Har ila yau, an kama wasu mutane biyu da ake zargi a kauyen Doka da ke Kachia, kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, yayin da ake zarginsu da safarar bindigogi kirar AK-47 guda uku ga ‘yan bindiga a cikin wata mota kirar Golf. Da yake mayar da martani kan wannan ci gaban, Gwamna Uba Sani ya yabawa hukumar DSS kan nasarar da ta samu, inda ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kawar da miyagun laifuka a fadin jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas October 23, 2025 Manyan Labarai Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki October 22, 2025...
“Allah ya albarkace mu da shugaba mai tsoron Allah da kishin jama’a – mutum ne mai kaunar al’ummar jihar Kano da Nijeriya, kuma me aiki tukuru domin ganin ci gabansu,” in ji Yusuf. Ya kuma jaddada kudirin sa na ciyar da jihar gaba bisa tsarin falsafar Kwankwasiyya, wanda ke jaddada hidima, rikon amana, da tallafawa. A nasa jawabin, Kwankwaso ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar NNPP da na Kwankwasiyya na kasa baki daya da su ci gaba da hada kai da kuma jajircewa wajen ci gaban jam’iyyar. Ya kuma mika godiyarsa ga shugaban NNPP na kasa Dr. Ajuji Ahmed, da sauran shugabannin jam’iyyar daga jihohi sama da 30, da masu biyayya da suka halarci bikin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA ...
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da yin ƙarin albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikata daga cfa 30,000 zuwa cfa 42,000, wanda ya yi daidai da naira 108,780 a Najeriya. Wannan ƙarin albashi na daga cikin matakan gwamnatin domin inganta rayuwar ma’aikata da ƙarfafa su wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum, kamar yadda gwamnatin ta sanar. Majalisar Ministocin gwamnatin ce ta ɗauki wannan mataki a taron da ta gudanar jiya Laraba, inda kuma minsitocin suka tattauna hanyoyin da za a tabbatar da cewa ƙarin albashin zai shafi dukkan ma’aikatan gwamnati ba tare da rarrabewa ba. Wannan mataki ya zo ne bayan da gwamnatin ta lura da ƙaruwar farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi a ƙasar. Gwamnatin ta bayyana cewa...
Masu Tasiri a Kafafen Sada Zumunta sun samu horo kan RMNCAH+N, Tsarin Iyali da Rigakafin Cin Zarafin Mata
Ƙungiyar Centre for Communication and Social Impact (CCSI) tare da haɗin gwiwar abokan aikin ta na EngenderHealth Consortium sun shirya taron horo na yini ɗaya a Kano domin ƙarfafa ƙwarewar ’yan jarida da masu tasiri a kafafen sada zumunta (social media influencers) wajen yada sahihan bayanai da tallafawa manufofin kiwon lafiya da daidaito tsakanin jinsi. Taron, mai taken “Daga Masu Bi zuwa Masu Faɗa Aji: Amfani da Kafafen Sada Zumunta wajen Yaɗa Sawun Lafiya da Daidaito”, ya mayar da hankali ne kan batutuwan Reproductive, Maternal, Newborn, Child, and Adolescent Health plus Nutrition (RMNCAH+N), Family Planning (FP), da Gender, Youth, and Social Inclusion (GYSI). Manufar wannan horo ita ce canza masu tasiri a kafafen sada zumunta zuwa ƙwararrun masu...
Kwamishinan Ilimi Na Kano Ya Yi Kira Da A Karfafa Shugabancin Makarantu Domin Inganta Karatun Dalibai
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda, ya jaddada muhimmancin samun ƙwararrun shugabannin makarantu wajen inganta koyarwa da haɓaka sakamakon karatu a fadin makarantun jihar. Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi, Kwamared Balarabe Abdullahi Kiru, ya sanya wa hannu. Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wajen taron horaswa na kwanaki biyu mai taken “Leading Learning for Gender Equality in Education” wanda British Council ta shirya domin wakilai daga jihohin Kano, Kaduna, Plateau da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT). Dr. Makoda ya ce, jagoranci mai ƙarfi da tsari a cikin makarantu shi ne ginshiƙin cimma ingantaccen ilimi. Ya kara da cewa, shugabannin makarantu...
Gwamnatin Tarayya ta koka da cewa, duk da wayar da kan jama’a da kuma gargadin da ake ci gaba da yi, wasu mutane har yanzu suna kasada da rayukansu ta hanyar yunƙurin ɗibar mai yayin da tankunan dakon mai suka faɗi. Ya jaddada cewa, kowace rai ta ɗan Nijeriya tana da daraja kuma irin wadannan bala’o’in da za a iya rigakafin su, na nuna bukatar kara wayar da kan jama’a game da haɗurran da ke tattare da hakan cikin gaggawa. Ya ce, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), an umurce ta da ta hada karfi ga kokarin Gwamnatin Jihar ta hanyar samar da kayan agaji da taimakon magunguna ga wadanda abin ya shafa da iyalansu. ShareTweetSendShare...
Hon. Musa ya kara da cewa, aikin zai mayar da hankali ne kan nazari da binciken kimiyyar kasa a yankunan da ake tunanin cewa suna dauke da uranium, danyen man fetur, da iskar gas, da nufin tattara dukkan bayanan da ake bukata don ci gaba da aiki. A cewar kwamishinan, amincewar wani bangare ne na manufofin gwamnatin Gwamna Umar Namadi na binciko albarkatun ma’adanai na jihar don haɓaka tattalin arzikin cikin gida mai ɗorewa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki October 22, 2025 Manyan Labarai Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi October 22, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta...
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya yi gargadin cewa amincewar da majalisar dokokin Isra’ila ta yi na samar da kudirorin doka da nufin tsawaita ikon Isra’ila a gabar yammacin kogin Jordan “barazana ne ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. Babban jami’in diflomasiyyar na Amurka ya shaidawa manema labarai a lokacin da yake shirin tafiya Isra’ila cewa, ” wannan ba wani abu ne da za mu iya ba da goyon baya gare shi ba a wannan lokaci.” Furin nasa na zuwa ne bayan da majalisar dokokin Isra’ila ta kada kuri’a kan samar da wani kudirin mallake Gabar Yamma da Kogin Jordan a matsayin yankin Isra’ila. Kudirin wanda wani dan majalisar Isra’ila mai tsattsauran ra’ayi ya gabatar na zuwa ne...
Tehran ta yi maraba da hukuncin da wata kotun Faransa ta yanke na yi wa ‘yar kasar Mahdieh Esfandiari saki bisa sharadi. ‘yan sandan Faransa sun dai kama ‘yar Iran din ce bisa zarginta da goyan bayan ta’addanci mai nasaba da nuna goyan bayan al’ummar Gaza . Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran,Esmail Baghaei ya ce Tehran za ta ci gaba da bin diddigin shari’ar Esfandiari, ‘yar kasar wacce malamar jami’a ce mai shekaru 39 da ke zaune a Lyon, har sai ta samu cikakken ‘yanci tare da komawa gida,” in ji Baghaei. Esfandiari, wacce ta zauna a Faransa kusan shekaru takwas, an cafke ta ne a asirce a ranar 1 ga Maris, 2025, wanda ya sa danginta sanar da hukumomin...
Ƙungiyar ‘yan jaridu ta Nijeriya (NUJ), reshen jihar Kano, ta mika sakon taya murna ga Ahmed Mu’azu bisa naɗin da aka yi masa na mataimaki na musanman a ɓangaren yaɗa labarai ga shugaban hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON), Abdullahi Usman Saleh. A matsayinsa na ɗan asalin jihar Kano, ɗaukaka darajar Malam Ahmad Mu’azu zuwa wannan matsayi abin alfahari ne ga masu aikin jarida a jihar. ‘Yansanda Sun Cafke Wani Matashi Ɗan Shekara 15 Da Ake Zargi Da Yin Fashi Da Makami A Gombe Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe Naɗin nasa ya nuna irin ƙwarewarsa da sadaukarwarsa a ɓangaren yaɗa labarai da yake da shi. Mu’azu kafin wannan muƙamin ya...
Gwamnatin Jihar Ondo ta roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu bayan gargaɗin da Hukumar Tsaro ta DSS, ta yi na cewar wasu mayaƙan ISWAP na shirin kai hari wasu sassan jihar. A cikin wata sanarwa, Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Mista Idowu Ajanaku, ya bayyana cewa irin waɗannan rahotanni abu ne na yau da kullum a harkokin tsaro. NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Haraji Da Zai Fara Aiki A 2026 Idan Tinubu ya gaza zai yi wuya a samu shugaban da zai yi nasara — Shehu Sani Ya ce hukumomin tsaro suna yawan musayar bayanai irin waɗannan domin daƙile duk wata barazana. Ajanaku, ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnati tare da hukumomin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ranar 26 ga watan Yuni, shekara ta 2025, gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan sabon tsarin haraji wanda za a fara aiwatarwa daga ranar 1 ga Janairu, 2026. Wannan sabon tsarin haraji na daga cikin matakan da gwamnati ke cewa zai taimaka wajen kara samun kudaden shiga da kuma rage dogaro da albarkatun mai. Sai dai, jama’a da dama ba su da cikakken bayani game da irin wadannan sabbin haraji ko menene suke nufi ba. NAJERIYA A YAU: Halin Da Muka Shiga Sakamakon Haihuwar ’Ya Mai Cutar Motsewar Kwakwalwa DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Shin ko ta wadanne hanyoyi ne wannan sabon haraji zai shafi rayuwar...
Ƙungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ), reshen jihar Kano, ta mika sakon taya murna ga Ahmed Mu’azu bisa nadin da aka yi masa a matsayin mataimakin mai tsara dabara kan harkokin yada labarai a hukumar alhazai ta kasa (NAHCON). A matsayinsa na dan asalin jihar Kano, daukaka darajar Malam Mu’azu zuwa wannan matsayi abin alfahari ne ga masu aikin jarida a jihar. ‘Yansanda Sun Cafke Wani Matashi Ɗan Shekara 15 Da Ake Zargi Da Yin Fashi Da Makami A Gombe Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe Nadin nasa ya nuna aikin ƙwarewa da sadaukarwa a ɓangaren yaɗa labarai da yake da shi. Mu’azu ya taɓa yin aiki a Sashen Hulda...
Shugaban ƙasa mai ci, Alassane Ouattara, shi ne wanda aka fi yi wa hasashen nasara a zaɓen da za a gudanar a Ivory Coast ranar Asabar, sakamakon rashin wasu jiga-jigan ’yan adawa da za a fafata da su a zaɓen. Ouattara, mai shekara 83, yana riƙe da madafun iko tun daga shekarar 2011, lokacin da ƙasar ta fara warwarewa daga rikicin siyasa kuma ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke taka rawa wajen bunƙasar tattalin arzikin yammacin Afirka. Jerin ’yan wasan da ke takarar lashe kyautar gwarzon Afirka na bana Idan Tinubu ya gaza zai yi wuya a samu shugaban da zai yi nasara — Shehu Sani A ƙarƙashin mulkinsa, Ivory Coast — wacce ita ce babbar mai...
A cewar sanarwar, “A ranar 15 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 11:00 na rana, wata mata da ke zaune a unguwar Federal Low-Cost, Gombe, ta bayyana cewa a daidai wannan ranar da misalin karfe 2:30 na dare, wani wanda ba ta san ko wanene ba, dauke da wuka ya kai mata hari, inda ya sace mata kayanta. “Abubuwan da aka sace, sun haɗa da iphone 13 Pro Max, an kimanta kudinta akan ₦800,000, kwamfutar ‘Apple MacBook’ da darajarta ta kai ₦250,000, da agogon ‘Apple’ da darajarsa ta kai ₦35,000, ‘power bank’ na Oraimo wanda darajarsa ta kai ₦30,000, da jakar makaranta akan darajar ₦25,000.” Abdullahi ya ce, nan take jami’an ‘yansanda na shiyyar suka dauki matakin kama...
Tun daga lokacin da kasar Sin ta fara kera jiragen kasa masu saurin gudu a shekarar 2007 da samfurin CRH1 mai gudun kilomita 250 cikin sa’a guda, ba ta tsaya ba har zuwa yanzu da ta kera wannan sabon na zamani samfurin CR450 wanda shi ma an yi masa tsarin da za a ci gaba da inganta shi. Wannan fasaha wacce ta kara jaddada matsayin kasar Sin na ci gaba da zama jagora a fagen kere-keren jirgin kasa mafi gudu a duniya, ba kasar Sin kawai za ta amfanar ba har ma da sauran sassan duniya musamman a wannan zamani da kasar ta Sin ke kara bude kofarta ga kasashen waje da kuma neman cimma burin samar da al’umma mai...
Ya ce tallafin da Shugaba Tinubu ya amince da shi ba rance ba ne, wani bangare ne na yunkurin gwamnati na cire shingen da ke hana ’yan kasuwa ci gaba. Ya ƙara da cewa gwamnati ta kafa asusun Naira Biliyan 75 da sunan tallafin ga ƙananan masana’antu da yan kasuwa (MSME Intervention Fund), wanda ke bai wa ’yan kasuwa rancen har zuwa Naira miliyan 5 da kaso tara cikin ɗari (9%) a matsayin kudin ruwa, da kuma Naira biliyan 50 a ƙarƙashin shirin Shugaba kasa Bola Tinubu da ke bai wa ƙanana ’yan kasuwa tallafin kuɗi kyauta bisa wasu sharuɗɗa domin bunƙasa kasuwanci (Presidential Conditional Grant Scheme) da ke ba da tallafin Naira 50,000 ga ’yan kasuwa miliyan ɗaya...
Ahmed maiyaki, ya dade yana bayar da gudummawa a harkar yada labarai a a fadin kasar nan bayan kasancewarsa tsohon ma’aikaci a sashin hausa na rediyon Faransa ( FRI). Jihar Kaduna ta kwashe shekaru takwas babu ma’aikatar yada labarai wacce tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya rufeta , sai bayan lashe zaben gwamna Uba Sani ya dawo da ma’aikatar wacce aka dorawa alhakin kula da yada manufofin gwamnatin jihar . ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi October 22, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta October 22, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Amince...
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Zamfara ta gargaɗi direbobi da sauran jama’a game da rufe lambobin motoci, musamman a cikin garin Gusau, babban birnin jihar. Gargaɗin ya biyo bayan ƙaruwa da ake samu na rahotanni da kuma lura da direbobi da ke tafiya da lambobin motoci a rufe, wanda rundunar ta bayyana a matsayin karya dokokin hanya da ke kawo barazana ga tsaro da zaman lafiya. A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, rundunar ta bayyana cewa wannan dabi’a tana nuna ƙoƙarin kaucewa binciken jami’an tsaro tare da yiwuwar taimaka wa aikata laifuka. Sanarwar ta ƙara da cewa, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya jaddada cewa rundunar...
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce babu wanda zai yi nasara wajen rusa tarihin Kano da aka kafa tsawon shekaru. Ya bayyana hakan ne a Abuja, a ranar Talata, yayin gabatar da littattafai biyu da Dokta Munzali Dantata, ya rubuta; Behind the City Wall da Aminu Dantata: Life and Times of a Nigerian Entrepreneur. An gano sauro a karon farko na tarihin ƙasar Iceland Gwamnatin Borno rufe makarantun jihar saboda rigakafin ƙyanda da Polio A cewar Sarkin, tarihin Kano ya samo asali ne daga tsohuwar al’ada ta jajircewa, ilimi, kasuwanci, da ƙwarewa. “Mun zo nan ne don murna, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne muna taya Kano murna, birni wanda ya samar da iyalan Dantata...
Wannan tsarin na taimaka wa yara su samu ilimi mai zurfi da zai ba su damar daidaita da tsarin rayuwarsu na yau da kullum. Makarantun suna da ɗakunan kwana, gidajen malamai, wutar lantarki mai amfani da hasken rana, rijiyoyin burtsatse, kujeru, kayan karatu, da cibiyar koyon sana’o’i kamar ɗinki, sassaƙa, kwamfuta, da sauransu. Haka kuma, gwamnan ya gyara Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta Jihar Zamfara da kuma Kwalejin Fasaha da Kimiyya ta Zamfara (ZACAS). A ɓangaren lafiya kuwa, gwamnatinsa ta gyara asibitoci da cibiyoyin lafiya da dama a faɗin jihar. Don rage mace-macen mata da jarirai a yayin haihuwa, ya ɗauki ƙarin ma’aikatan lafiya, tare da samar da magunguna da kayan aiki, tare d harkar kyautata kiwon...
A gefe guda kuma ta roƙi jama’a su yi watsi da rahoton jaridar, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da aikinta cikin gaskiya da amana. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta October 22, 2025 Labarai Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal October 22, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe October 22, 2025
Babaganaru, ya taɓa jagorantar ƙungiyar inda ya lashe kofunan gasar NPFL guda biyu a shekarun 2011/12 da 2012/13 a lokacin da ya yi aiki a baya. Ana sa ran zai kawo gogewa da a wannan sabon babi na horar da ƙungiyar. A halin yanzu Pillars tana matsayi na 18 a kan teburin gasar bayan wasanni takwas, inda ta samu nasara biyu kacal, ta yi canjaras biyu da kuma rashin nasara huɗu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta October 20, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara October 20, 2025 Wasanni Kano Derby: Barau FC...
Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya, Fasaha da Kirkire-Kirkire ta Jihar Borno ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun Firamare da Sakandare na gwamnati da masu zaman kansu na tsawon kwanaki biyu domin gudanar da aikin rigakafin cututtukan ƙyanda da shan inna. Sanarwar umarnin rufe makarantun ta fito ne daga ofishin Kwamishinan Ma’aikatar, a ranar Talata, a birnin Maiduguri. Labarin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya ƙarya ne – Sarkin Musulmi Fashewar tankar mai ta yi ajalin mutum 30 a Neja A cewar sanarwar, za a rufe makarantun daga ranar Alhamis, 23 ga Oktoba, zuwa Juma’a, 24 ga watan Oktoba, 2025. An kuma umarci dukkan makarantun da su ci gaba da ayyukansu daga Litinin, 27 ga Oktoba, 2025, kamar yadda aka saba....
Piwuna, ya ce gwamnati ta gaza cika alƙawurran da ta ɗauka duk da sanarwar kwanaki 14 da ASUU ta bayar tun a ranar 28 ga Satumba, 2025. Ya ce babu wani abin da aka cimma wanda zai hana ƙungiyar aiwatar da shawarar majalisar zartarwarta na fara yajin aikin. “Dukkanin rassan ASUU a faɗin ƙasar nan an umarce su da su janye ayyukansu daga misalin ƙarfe 12 na dare ranar Litinin,” in ji Piwuna Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin cikin wannan lokaci, za ta ɗauki mataki mafi tsanani bayan kammala yajin aikin gargaɗi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe...
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya karyata zargin kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya, yana mai cewa wannan ikirari ƙarya ne kuma bai kamata a ci gaba da yada shi ba. Sarkin ya bayyana hakan ne a taron Babban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Arewa na shekarar 2025, wanda aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, a ranar Talata, da taken: “Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Al’umma Domin Samun Zaman Lafiya da Tsaro Mai Dorewa a Arewa.” Masu kwacen waya sun kashe ma’aikaciyar lafiya a Zariya Majalisa ta soma binciken yadda aka kashe $4.6bn na tallafin kiwon lafiya Ya ce: “Sun dade suna cewa ana kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya daga ƙasashen Yamma kamar Amurka, Kanada da sauransu. A ina? Yaushe?...
Cikakken bayani na tafe… ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja October 22, 2025 Manyan Labarai Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi October 21, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja October 21, 2025
Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin cikinta game da gobarar tankar mai da ta tashi a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja, inda mutane 38 suka rasa rayukansu. A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta jajanta wa jama’a da gwamnatin Jihar Neja, musamman iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma Gwamna Mohammed Umar Bago. Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya “Tunaninmu yana tare da iyalan da wannan mummunan lamari ya shafa. Muna godiya ga ma’aikatan agajin gaggawa bisa taimakon da suka bai wa waɗanda abin ya rutsa da su,”...
Gwamna Yusuf ya lura cewa, wasu kafafen yada labarai na yanar gizo suna amfani da manhajojin su wajen yada “labarai masu raba kan addini da siyasa,” wanda a cewarsa, za su iya gurgunta hadin kan al’umma da kwanciyar hankali idan ba a magance su ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisa Ta Tabbatar Da Yusuf A Matsayin Sabon Shugaban NPC, Wasu 2 A Matsayin Kwamishinoni October 21, 2025 Manyan Labarai Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi October 21, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja October 21, 2025
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira biliyan ɗaya domin gyaran ajujuwan karatu a wasu makarantu na gwamnati. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse. A cewarsa, majalisar zartarwar jihar ta amince da kashe fiye da Naira miliyan 528 domin gyaran ginin ajujuwa a wasu zababbun makarantu na gwamnati a fadin jihar. Ya bayyana cewa, manufar aikin ita ce inganta yanayin karatu, tabbatar da tsaro, da kuma samar da iingantaccen ilimi karkashin shirin gwamnatin jihar na farfado da ilimin asali. Sagir Musa ya kuma ce, majalisar ta amince da kashe sama da Naira miliyan 512 domin samar...
Har ma abun da ba kasafai ake gani ba, tattalin arzikin Sin yana cike da karfin tinkarar duk wani hadari da ka iya kunno kai. Ba sabunta kayayyaki kirar kasar da kara musu inganci kadai aka samu ba, har ma abokan cinikin kasar a ketare suna ta kara yawa. A jiya Litinin ne aka bude cikakken zama na 4 na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 a nan Beijing, inda za a tattauna da kuma ba da shawarwari kan shirin shekaru biyar-biyar na 15 na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin. Kasashen duniya na sa ran cewa, kasar Sin za ta ba da sababbin damammarkin neman samun ci gaba ga duniya, bisa ga...
Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya rattaba hannu kan dokar ƙirƙirar sabbin masarautu 13 wadda za ta ba da damar naɗin hakimai sama 111 a faɗin jihar. Sabbin masarautun da gwamnan ya ƙirƙira sun haɗa da: Burra, Duguri, Dambam, Bununu, Lere, Darazo, Jama’a, Lame, Toro, Ari, Warji, Giade da kuma masarautar Gamawa. Uba Sani ya yi wa ma’aikatan manyan makarantu ƙarin kashi 70 a albashi Fashewar tankar mai ta yi ajalin mutum 30 a Neja Da yake jawabi a gidan gwamnati, Bala Mohammed ya gargadi masu son siyasantar da lamarin ko kawo cikas wajen aiwatar da dokokin, yana mai cewa hukumomin tsaro za su dauki matakin da ya dace. “Ba za mu lamunci duk wanda zai yi ƙoƙarin tayar da...
“Wadanda aka nada sun bayyana a gaban kwamitin don tantancewa a ranar Talata, 14 ga Oktoba, 2025,” in ji shi. “Kwamitin bai samu koke ko korafe-korafe ba a kansu, sun nuna shiri da cancanta akan ayyukan da aka zabo su”. Ya bayyana sunayen wadanda aka tantance a matsayin: “Aminu Yusuf (Jihar Neja) – Shugaba, Joseph Haruna Kigbu (Jihar Nasarawa) – Kwamishina, Tonga Betara Bularafa (jihar Yobe) – Kwamishina. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi October 21, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja October 21, 2025 Manyan...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia October 21, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia October 21, 2025 Daga Birnin Sin Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka October 20, 2025