A zantawarsa da manema labarai, jagoran tafiyar Shelkh Umar Shehu Zaria wanda kuma shi ne, babban limamin Masallacin Mus’ab Ibn Umair, Sun jaddada cewa, su ba su da wani buri na daban face ganin an samu zaman lafiya, hadin kai, da mutunta juna a tsakanin mabiya addinai da jama’ar Kaduna baki daya.

“Wadannan malamai guda biyu suna fakewa da malunta suna cin mutunci Manzon Allah SAW.

Da’awarsu a Kaduna barazana ce ga zaman lafiya, saboda fitina a jihar Kaduna ba za ta haifar da abu mai kyau ba,” inji shi

 

Ofishin kula da harkokin addinai karkashin jagoranci Malam Tahir Umar Tahir, ya karɓi takardar korafin kuma ya tabbatar da cewa, zai gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin da kuma daukar matakin da ya dace bisa doka.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal October 28, 2025 Labarai Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe October 28, 2025 Manyan Labarai Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260 October 28, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

Waɗannan matsalolin, sun sanya ake yin jigilar  kayan ta kan hanya, a manyan motoci, wanda hakan ya sanya masu ruwa da tsaki a fannin ke ci gaba da kokawa, saboda kuɗaɗen da suke kashewa masu yawa, wajen jigilar kayansu

wanda hakan ya saɓawa manufar ta kafa Tashodhin  Jiragen Ruwan ta kantudu.

Injiniya Kayode Opeifa Shugaban Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa na ƙasa ya tabbatar da waɗannan matsalolin a taron 2025 Ƙungiyar ‘Yan Jarida Wakilai  da ke ɗauko rahotannin ɓangaren sufuri TCAN, da aka gudanar a jihar Legas.

A cewar Kayode, ƙalubalen rashin tsaro, a jihar Neja, hakan ya tilasta Hukumar dakatar da jigilar kayan ta hanyar amfani da Jirgin ƙasa zuwa Kaduna.

Sai dai ya bayyana cewa gwamnonin jihohin Neja da Kaduna, sun yi haɗaka domin lalubo da mafita kan lamarin.

Wani Babban Jami’i a Tashar ta kantudu da ke a jihar Kaduna wanda bai buƙaci a sakaya sunansa ya shedawa LEADERSHIP cewa, baya ga ƙalubalen rashin tsaro, ambaliyar ruwan sama da ta auku a jihar Nije, ta janyo yin gaba da wasu ƙarafan da Jirgin ƙasa ke bi, wanda hakan ya dates ɗaukacin duk wata zirga-zirgar Jiragen zuwa Tashar.

“Muna ci ga da jiran Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta ƙasa NRC, domin ta gyran hanyar ta layin Dogon, wanda kuma idan harkar tsaro ta ƙaru, hakan zai bai wa masu hada-hadar safarar kaya a Jiragen Ƙasan, su samu damar ci gaba da yi zuwa Tashar ta Kantudu, da ke a jihar ta Kaduna, “ A cewar babban jami’i.

Ya ƙara da cewa, yayin da ayyukan sufurin suka tsaya tska, hakan ya sanya ba a yin safarar kaya a cikin Jiragen zuwa Tashar.

Sai dai, wasu masu ruwa da tsaki a fannin sun bayyana fargabar da cewa, ci gaba da ɓata lokaci da ake yi na rashin yin amfani da Tashar hakan zai karya masu ƙwaiwa na ci gaba da yin amfani  da Tashar wajen yin safarar kayansu zuwa Tashar.

Bugu da ƙari, sun bayyana cewa, hakan zai kuma mayar da hannun Agogo bayan na ƙiƙarin Gwamnatin Tarayya na ci gaba da ɗaga darajar Tashoshin na Kandu, da aka samar a ƙasar, musamman wajen samar da sauƙin gudanar da hada-hadar kasuwanci a yankin Afirka.

Sai dai, duk da wannan ƙalubalen Hukumar ta NRC da kuma sauran gwamnonin jihohin da abin ya shafa, na kan yin aiki daomin sake dawo da zirga-ziragar kaya zuwa Tashar ta hanyar ƙara ƙarfafa tasaro da kuma sanya wasu ƙarafan na layin Dogo, da ambaliar ruwan saman, ta yi gaba da su.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano October 26, 2025 Labarai Gwamnatin Kaduna Tare Da  AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma October 26, 2025 Wasanni Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru October 26, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe
  • Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu
  • Baqaei: Iran ta daɗe tana aiki don haɓaka zaman lafiya a duniya
  • Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Masu Ƙananan Sana’o’i Biliyan 75 Domin Bunƙasa Kasuwancinsu
  • Matsalar kashe-kashe a Nijeriya ba ta da alaƙa da addini — Femi Kayode
  • Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna
  • An kama mutum 25 kan zargin shirya auren jinsi a Kano
  • Gwamnatin Kaduna Tare Da  AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma
  • An ba da tallafin N2m ga iyalan jami’in NSCDC da aka kashe a Jigawa