Aminiya:
2025-10-28@10:26:03 GMT

Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 80 a Kebbi

Published: 28th, October 2025 GMT

Jami’an tsaron hadin gwiwar sun kashe fiye da ’yan bindiga 80 da suka yi yunƙurin kutsawa Jihar Kebbi ta iyakarta da Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa, sojojin sama da na ƙasa sun gudanar da sumame a dajin Makuku, inda suka yi ruwan wuta kan sansanonin ’yan ta’adda, suka kuma kashe da dama daga cikinsu.

Dakarun sun kuma ceto mutane biyu da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su.

A wata sanarwa da Daraktan Tsaro na Ofishin Majalisar Zartarwa ta Jihar Kebbi, Abdulrahman Zagga, ya fitar, an bayyana cewa dakarun sun yi nasarar daƙile wani mummunan hari da sama da ’yan bindiga 400 suka kai garin Ribah, inda aka yi musu mummunar ɓarna.

An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi Rikicin ADC: Sanata Nenadi ta zama shugaba a Kaduna

Mai ba Gwamnan Jihar Kebbi shawara kan harkokin sadarwa da dabarun mulki, Abdullahi Idris Zuru, ya shaida wa manema labarai, cewa wannan aiki ya nuna tsayin daka da ƙarfin dakarun tsaro wajen yaƙi da ’yan ta’adda.

Ya ce, “Dakarun sun yi aiki tuƙuru don hana ’yan bindigar kutsawa cikin Kebbi. Wannan sumame wani ɓangare ne na ci gaba da ƙoƙarin daƙile ta’addanci da fashi da makami a fadin jihar.

“Sojojin Najeriya suna ci gaba da kai hare-hare a dazuka da yankunan da ke kan iyaka, musamman a dajin Makuku.”

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar tana aiki kafaɗa-da-kafaɗa da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Jami an Tsaro Tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

Amnesty International Ta Bukaci Bayyana Makomar Masu Fafutukar Kare Hakkin Bil’Adama Da Suka Bace A Uganda  

Kungiyar Kare Hakkin Bil’Adama ta Amnesty International ta matsa wa Uganda lamba ta bayyana makomar masu fafutukar kare hakkin bil’adama na Kenya

Kungiyar Kare Hakkin Bil’Adama ta Amnesty International Kenya ta ƙara matsin lamba ga hukumomin Uganda kan su saki masu fafutukar kare haƙƙin ɗan adam na Kenya Bob Njagi da Nicholas Oyo, waɗanda suka ɓace a babban birnin Kampala, a farkon watan Oktoba. Ana zargin gwamnatin Uganda da Rashin bayyana makomar mutanen biyu.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a yau ranar Litinin, ƙungiyar ta Amnesty International ta kwatanta halin da ake ciki a Uganda a yanzu da mulkin tsohon shugaban ƙasa Idi Amin (1971-1979), wanda aka danganta shi da ɗaya daga cikin mafi munin lokutan take haƙƙin ɗan adam a tarihin ƙasar.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sun Yi Da’awar Kwace Karin Wasu Garuruwa A Sudan October 27, 2025 Qalibaf: Sakon Iran, Rasha da China ga MDD manuniya ce ta hadin gwiwa mai karfi October 27, 2025 Sheikh Naim: Hezbollah a shirye take ta fuskanci Isra’ila idan yaki ya barke October 27, 2025 Catherine Connolly ta lashe zaben shugaban Ireland October 27, 2025 Hamas ta sake jaddada wajabcin aiwatar da Shirin tsagaita wuta a Gaza October 27, 2025 Sudan: Dakarun sa kai na Jama’a a Arewacin Darfur sun karyata RSF kan kwace iko da El Fasher October 27, 2025 Araghchi : Iran na maraba da tattaunawar diflomatsiyya da Amurka amma cikin mutunta juna October 26, 2025 Ana Zaman dar-dar gabanin bayyana sakamakon zaben shugaban kasa a Kamaru October 26, 2025 Faransa : An yi Zanga-zangar adawa da isar da makamai zuwa Isra’ila October 26, 2025 Hamas : Ba za mu bari Isra’ila ta sami hujjar ci gaba da yaki a Gaza ba October 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi
  • An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi
  • Amnesty International Ta Bukaci Bayyana Makomar Masu Fafutukar Kare Hakkin Bil’Adama Da Suka Bace A Uganda  
  • Ɗalibi ya kashe abokinsa, ya binne gawarsa a rami a Filato
  • Ɗalibi ya kashe abokinsa, ya binne shi a rami a Filato
  • Matsalar kashe-kashe a Nijeriya ba ta da alaƙa da addini — Femi Kayode
  • ‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano
  • An ba da tallafin N2m ga iyalan jami’in NSCDC da aka kashe a Jigawa 
  • Sauke Hafsoshin Tsaro: Za a yi wa Janar-Janar 60 ritaya daga aiki