Leadership News Hausa:
2025-12-12@11:24:09 GMT

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

Published: 28th, October 2025 GMT

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba October 27, 2025 Manyan Labarai Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa October 27, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro October 27, 2025

.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Ta Kara Samar da Shirye-shiryen Inganta Rayuwar Masu Buƙata ta Musamman

Daga Usman Muhammad Zaria

Hukumar kula da masu bukata ta musamman a jihar Jigawa za ta gudanar da aikin gyaran gidajen gajiyayyu na shiyyar Birnin Kudu da Gumel a sabuwar shekara.

Shugaban hukumar, Malam Sale Zakar Kafin Hausa, ya bayyana haka lokacin kare kiyasin kasafin kudin 2026 a gaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa.

Ya ce gidan gajiyayyu na shiyyar Birniwa yana cikin kyakkyawan yanayi da kulawa sosai ta fuskar abinci da sutura da kayan wanka da na wanki da sauran bukatun rayuwa, dan haka gwamnati ta kuduri niyyar gyara sauran gidajen gajiyayyun domin kyautata yanayinsu.

Malam Sale Zakar ya ce an Kara yawan mata masu juna biyu da masu shayarwa da ke amfana da Shirin kula da lafiyar iyali daga 20 zuwa 30 a mazabun jihar 287.

Ya kara da cewa za kuma a kara yawan masu amfana da tallafin masu bukata ta musamman daga 150 zuwa 200 a kowacce karamar hukuma, inda masu bukata ta musamman 540 ke samun tallafin naira 10, 000 a duk wata.

A nasa jawabin shugaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Birnin Kudu Alhaji Muhammad Kabiru Ibrahim ya bayyana gamsuwa da tanade tanaden da aka yiwa mata da yara da tsoffi da marasa galihu da mata masu juna biyu da masu shayarwa da nakasassu.

Ya kuma yi addua’ar Allah Ya sa kasafin kudin ya yi tasiri wajen inganta rayuwar masu karamin karfi da marasa galihu a sabuwar shekara.

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Za A Yi Manyan Zabuka A Kasar Habasha A Watan Yuni Na 2026
  • Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa Bisa Garkuwa Da Kashe Mai Gidansa A Kano
  • Gwamnatin Jigawa Ta Kara Samar da Shirye-shiryen Inganta Rayuwar Masu Buƙata ta Musamman
  • Katsina Ta Amince Da Bayar Da Alawus Na Naira 30,000 Duk Wata Ga Malaman Karkara
  • Zanga-zanga ta ɓarke bayan haɗarin tirela ta kashe mutum a Yobe
  • Yadda za ku cike neman aikin dan sandan Najeriya na 2025/2026
  • Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa
  • Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Benin – Soyinka
  • Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Jamhuriyar Benin – Soyinka
  • Kamfanin Mangal ya kori direba kan dauko yara 21 da aka kama a Kogi