An raba wa iyalan ’yan sandan da suka mutu tallafin N31m a Jigawa
Published: 28th, October 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jigawa ta raba tallafin Naira miliyan 31 ga iyalan jami’ai 59 da suka rasa rayukansu a bakin aiki.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, inda ya bayyana cewa wannan mataki na nuna irin ɗawainiyar da rundunar ‘yan sandan ke yi wajen kula da jin daɗin jami’anta da iyalansu.
Aminiya ta ruwaito cewa Kwamishinan ‘yan sandan Jigawa, CP Dahiru Muhammad ne ya wakilci Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, wajen raba tallafin a ƙarƙashin shirin nan na tallafa wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka mutu a bakin aiki wato Group Life Assurance (GLA) da kuma IGP Family Welfare Scheme.
Da yake miƙa tallafin, CP Dahiru ya bayyana jami’an da suka rasu a matsayin “jarumai da suka sadaukar da rayukansu wajen kare al’umma domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kan ƙasa.”
Ya ce ba za a taba mantawa da gudummuwarsu ba, yana mai jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da tallafa wa iyalansu domin rage raɗaɗin rashinsu.
Ya kuma shawarci iyalan mamatan da aka rabawa tallafin da su yi tattalin kuɗaɗen wajen ci gaban iyalansu.
A nasa jawabin, wanda ya wakilci iyalan waɗanda abin ya shafa, Malam Surajo Shehu, ya miƙa godiya ga Sufeto Janar da kwamishinan ‘yan sanda na Jigawa bisa wannan kulawa da jinƙai da suka nuna, tare da alƙawarin amfani da kuɗaɗen domin karrama jaruman jami’an da suka rasu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda iyalai Jihar Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jigawa Ta Nemi Kotuna Su Daina Jan Kafa Wajen Aiwatar da Shari’a
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Jigawa ta bayyana damuwa kan jinkirin shari’a wajen gurfanar da masu laifin rashawa, inda ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 479 da suka shafi cin hanci, amana da sauran laifuka makamanta a wannan shekarar ta 2025.
Shugaban Hukumar, Barista Salisu Abdul ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai kan nasarorin da hukumar ta samu da ƙalubalen da ta fuskanta a shekarar
Taron manema labaran wani ɓangare ne na shirye-shiryen hukumar na bikin Ranar Yaƙi da Cin Hanci ta Duniya.
Barista Salisu Abdul ya ƙara da cewa, cin hanci babban abin da ke janyo koma-baya ne ga Najeriya a fannoni daban-daban na rayuwar jama’a da tattalin arzikin ƙasa.
A cewarsa, babban burin hukumar wacce aka kafa a watan Fabrairun 2024 shi ne ƙarfafa yaƙi da cin hanci da rashawa a jihar, tare da inganta gaskiya, ɗabi’a, da amana a harkokin gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu, da al’amuran zamantakewa da tattalin arziki.
Shugaban ya ce, a wannan shekarar hukumar ta shirya horo ga manyan ma’aikatan gwamnati da jami’anta, tare da wayar da kan jama’a kan rawar da kowa ya kamata ya taka wajen yaƙi da cin hanci.
“Yayin da muke ci gaba da wayar da kai sosai, za mu ƙara haɗa kai da sauran hukumomin yaƙi da cin hanci, da hukumomin gwamnati da masu zaman kansu, da jama’a domin mu fi mai da hankali wajen dakile cin hanci fiye da magance shi bayan ya faru,” in ji shi.
Ya kuma ce, hukumar za ta rungumi fasahar zamani a ayyukanta don samun ingantaccen sakamako.
Barista Salisu Abdul ya bayyana cewa, daga cikin shari’o’in 479, guda 110 sun shafi cin hanci da damfarar kuɗi, yayin da 375 suka shafi rikicin kadarori, sabanin iyali, da ma’amalar kasuwanci da ta ci tura, inda aka warware shari’o’i 107 cikin sulhu.
Ya kara da cewa an dawo da fiye da Naira miliyan 385 da kadarorin da darajarsu ta kai daruruwan miliyoyi, aka kuma mika su ga masu su.
Sai dai ya nuna damuwa kan yadda alkalai ke tafiyar da shari’o’in a hankali, wanda ya bayyana a matsayin babban ƙalubale da ke kawo cikas ga yaƙi da cin hanci a jihar.
Shugaban Hukumar ya kuma nemi goyon bayan kafafen yaɗa labarai a yaƙin da ake yi da cin hanci, tare da yabawa Gwamna Umar Namadi bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar na yin aiki bisa cikakken ‘yanci ba tare da tsoma baki ba.