An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka
Published: 28th, October 2025 GMT
An kira wani taron musamman a Amurka na tattaunawa tsakanin kasa da kasa mai taken “Kirkire-kirkire da budadden kasuwanci, da more damammakin ci gaba” a birnin Washington na Amurka. Babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG da ofishin jakadancin Sin dake Amurka ne suka gabatar da taron cikin hadin gwiwa.
Kusan baki 100 daga Amurka da Sin, ciki har da masana kan harkokin kasa da kasa, malamai, da wakilan matasan Amurka, sun tattauna batutuwa kamar yadda Sin ke amfani da karfin kimiyya da fasaha mai dorago da kai don karfafa kirkire-kirkire a duniya, da fadada budadden kasuwancinta mai zurfi, da more damammaki ga sauran kasashe. Da wannan taron ne aka fara gudanar da jerin tarurrukan tattaunawar kasa da kasa bisa taken taron.
A cikin jawabinsa ta kafar bidiyo, shugaban CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, CMG za ta ci gaba da hadin gwiwa tare da abokan huldarta don kafa dandalin tattaunawa na duniya, da aiwatar da “shawarar ziri daya da hanya daya,” kana da tabbatar da shawarwari 4 a duniya da shugaban kasar Sin ya gabatar, ta yadda Sin za ta samar da moriyar dabarar kasar a bangaren inganta tsarin shugabancin duniya da kuma makomar Sin ta zamanantar da al’ummarta ga kasashen duniya, har kuma ta samar da moriyar karfin kirkire-kirkirenta na zamani ga duk fadin duniya. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya
A baya bayan nan, kundin da aka amince da shi yayin cikakken zama na hudu na kwamitin kolin JKS na 20, ya tanadi tsare-tsaren musamman na fadada bude kofofin kasar ga sassan waje, da dora muhimmancin gaske ga samar da sabon yanayin hadin gwiwar cimma moriyar juna.
A halin yanzu, a hannu guda ana ganin zurfafar sabon zagayen juyin-juya-halin fasahohi, da sauyi a ci gaban masana’antu, a gabar da duniya ke bukatar bude kofa da rarraba gajiya sama da duk wani lokaci a baya. A daya hannun kuma, tsarin daukar matakan kashin kai da kariyar cinikayya na dada kamari, kuma duniya na fuskantar yanayin rashin daidaiton ci gaba da gibi a fannin jagoranci.
A wannan yanayi mai sarkakiya da duniya ke ciki, Sin ta nacewa kara fadada bude kofofinta, tana kuma ci gaba da karkata akalar nasarorinta kan turbar zamanantarwa ta Sin zuwa tsarin samar da gajiya ga ci gaban duniya na bai daya.
Shaida ta hakika ta nuna cewa, ba zai yiwu a raba tsakanin ci gaban Sin da na duniya baki daya ba, kana ba za a iya raba ci gaban duniya da na kasar Sin ba. Don haka, jigon samar da karin gudummawar Sin ga ci gaban tattalin arzikin duniya na da nasaba da babban tsarin bude kofofi daga mabanbantan sassa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA