An kammala bikin bayar da Kyautar Jaruman Indomie karo na 17, inda aka karrama matasan da suka nuna hazaƙa da jarumtaka, kuma suka zama jakadun Najeriya a fannoni daban-daban.

Wannan gagarumin biki ya gudana a birnin Legas a ranar 16 ga Oktoba, 2025, ƙarƙashin shirye-shiryen kamfanin Dufil Prima Foods, masu samar da Indomie Instant Noodles, a wani ɓangare na shirin kamfanin na kyautata dangantaka da al’umma (CSR).

Kamfanin ya tabbatar da bayar da kyaututtuka ga Jaruman Indomie — wani girmamawa na musamman ga matasan da suka nuna jarumta da Ƙirƙire-ƙirƙire a faɗin ƙasar.

Taken bikin na bana shi ne “Jaruman da Ba a San Su ba”, inda fitattun matasa uku daga sassan Najeriya suka fito a matsayin zakaru, bayan sun nuna bajinta, halin kirki, da jarumta.

Daga ranar 11 zuwa 13 ga Oktoba, 2025, miliyoyin ’yan Najeriya suka bibiyi shirye-shiryen talabijin na ƙasa domin jin labaran waɗannan matasa masu ban mamaki, waɗanda suka motsa zukata tare da ƙarfafa gwiwar al’umma.

Bayan wani dogon tsarin tantancewa da aka gudanar a duk faɗin ƙasar — wanda ya haɗa da hirarraki da makarantu da al’umma — an zaɓi zakaru uku daga rukuni daban-daban:

Abraham Umoren, mai shekaru 9 daga Jihar Akwa Ibom, ya lashe gasar Physical Bravery — jarumta ta zahiri.

Ismail Muhammad, mai shekaru 13 daga Jihar Kwara, ya lashe gasar Social Bravery — jarumta ta zamantakewa.

Hassan Adamu, mai shekaru 15 daga Jihar Yobe, ya lashe gasar Intellectual Bravery — jarumta ta basira.

An zaɓi waɗannan jarumai ne daga dubban matasa da aka gabatar daga sassa daban-daban na ƙasar, bayan watanni na bincike da tantancewa daga kwamitin masu zaman kansu da Dufil Prima Foods ta amince da su.

Da yake jawabi a ƙarshen bikin, Manajan Sadarwa na Rukunin Kamfanoni na Dufil Prima Foods, Temitope Ashiwaju, ya ce: “Kowace shekara muna ganin zurfin jarumta, fasaha, da baiwar da yaran Najeriya ke nunawa. Wannan shiri ne da muke alfahari da shi domin tallafa wa matasa wajen ciyar da ƙasa gaba.”

Ya ƙara da cewa: “Kyautar Jaruman Indomie ba kawai biki ba ne, amma madubi ne da ke nuna makomar Najeriya. Labaran waɗannan yara suna tunatar da mu cewa jarumta ba ta takaitu ga shekaru ko matsayi ba, sai dai a cikin ayyukan da ke ɗaga darajar wasu.”

Zakarun matasan sun nuna farin ciki da godiya bisa wannan dama, inda kowannensu ya gode wa Indomie saboda wannan girmamawa, tare da yin alƙawarin ci gaba da yin abin alheri a cikin al’ummominsu.

“Ba mu taɓa tsammanin za a yi irin wannan biki ba,” in ji Abraham Umoren, yana ƙara da cewa: “Na gode Indomie. Zan ci gaba da taimaka wa wasu gwargwadon iyawata.”

A bana, an gudanar da wannan biki na farko a matakin jihohi, inda aka girmama matasa daga kowanne rukuni, tare da faɗaɗa damar da aka samu don karrama ƙarin matasa masu kawo sauyi a Najeriya.

Tun daga lokacin da aka fara wannan shiri a shekarar 2008, matasa 59 suka riga sun amfana da tallafin karatu na miliyoyin naira — a matsayin yabo da ƙarfafa gwiwarsu don ci-gaban al’umma.

Bikin na bana ya bai wa iyalai, malamai, da shugabanni damar jin labaran da ke ci gaba da karfafa bege da juriya a cikin al’ummomi.

Kyautar Jaruman Indomie ta ci gaba da zama shaida ga jajircewar kamfanin Dufil Prima Foods, wanda ya daɗe yana ƙoƙarin haɓaka shugabanci, nuna tausayi, da kishin ƙasa a cikin manufofinsa na cigaban Najeriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: jarunta Kyautar Jaruman Indomie

এছাড়াও পড়ুন:

An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke shirin halartar taron shugabannin kungiyar bunkasa tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pacific (APEC) karo na 32 a Koriya ta Kudu da kuma ziyarar aiki a kasar Koriya ta Kudu, an kaddamar da nuna muhimman shirye-shiryen talabijin da fina-finai na rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) a membobin APEC. Za a watsa shirye-shiryen fiye da goma a manyan kafofin watsa labarai 22 a kasashe 14 na yankin Asiya da tekun Pacific, ciki har da Australia, Kanada, Chile, Indonesia, Koriya ta Kudu, Peru, Rasha, Thailand, da Amurka.

 

Babban darektan CMG Shen Haixiong, ya fada a cikin wani sakon bidiyo cewa, ana fatan wadannan shirye-shiryen talabijin da fina-finai za su iya taimaka wa masu kallo da sauraro a yankin Asiya da tekun Pacific wajen fahimtar hikimar shugaba Xi a fannin shugabanci, da ci gaban kasar Sin a sabon zamani, da al’adun kasar Sin, da kuma bunkasa ci gaban zaman lafiya, da hadin gwiwa mai amfanarwa ga dukkan bangarori, da kuma samun wadata a tsakanin kasashen Asiya da tekun Pacific. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take October 24, 2025 Daga Birnin Sin An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan October 24, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa October 24, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An rufe makarantu saboda ƙarancin man fetur a Mali
  • Ƙaddamar da Kyautar Jaruman Indomie Karo Na 17 Yayin Da Zakarun Matasa Suka fafata daga karshe an samu zakaru
  • NAJERIYA A YAU: Shin Ko Sauya Hafsoshin Tsaro Zai Kawo Karshen Aikin Ta’dda A Najeriya?
  • Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa
  • Ja’afari: Iran Tana Da Isassun Makamai Masu Linzami Masu Cin Zangogi Daban-Daban
  • Sojoji sun daƙile harin ISWAP a Borno
  • Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki
  • Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD
  • An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC