Ya ƙara da cewa shirin ya dace da shirin jihar, inda zai mayar da hankali kan bunƙasa samar da abinci a gida da karfafa matan gida wajen kula da abinci mai gina jiki.

Gwamnan ya bayyana cewa majalisar kula da abinci ta jihar za ta jagoranci tsara manufofi, haɗin kai da kuma kula da aiwatar da shirin a dukkanin kananan hukumomin jihar.

“Mun ƙuduri aniyar tabbatar da cewa wannan shiri ya ɗore tare da haɗin kan gwamnati da abokan hulɗa,” in ji shi.

A nasa ɓangaren, kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsare, Hon. Abdulmalik Gajam, ya ce gwamnatin Gwamna Lawal na taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkar lafiya da abinci mai gina jiki ga yara ƙanana.

Haka kuma, Misis Uju Rochas Anwukah, babbar mataimakiyar shugaban ƙasa kan harkokin kiwon lafiya, ta yaba da yadda gwamnatin Zamfara ke gudanar da ayyukan lafiya, inda ta bayyana cewa shirin zai taimaka wajen gina Nijeriya mai wadataccen abinci mai gina jiki.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe October 22, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas October 22, 2025 Manyan Labarai Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja October 22, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Aikin Hanya Akan Kudi Sama Da Naira Biliyan 4

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da aikin gina hanyar Babban Sara zuwa Malam Bako zuwa Shabaru zuwa Kirgi zuwa Albasu, mai tsawon kilomita 28.2, a Karamar Hukumar Sule Tankarkar,wanda kudinsa ya kakaNaira Biliyan 4.47, a ci gaba da shirin Gwamnati da Jama’a.

Aikin hanyar zai hada fiye da kauyuka 60 tare da karfafa harkokin kasuwanci da zamantakewa a yankin.

Haka kuma, gwamnan ya bude sabuwar cibiyar kula da lafiya ta farko, da makarantar Tsangaya ta zamani, da kuma rukunin samar da ruwa a yankin.

Gwamna Namadi ya bayyana cewa shirin Gwamnati da Jama’a hanya ce ta karfafa gaskiya, bayyana ayyuka da kuma baiwa jama’a damar fadin  ra’ayoyinsu.

“Mun zo ne mu nuna abin da muka cimma cikin shekara biyu, mu kuma saurari jama’a domin mu kara gyara inda ya kamata,” in ji shi, yana mai jaddada cewa hakikanin gwamnati ita ce wadda ke bautar al’umma.

Ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa gyare-gyaren da ke karfafa tattalin arzikin jihohi da kananan hukumomi, inda ya bayyana cewa Jihar Jigawa na daga cikin jihohi shida da aka zaba don fara shirin ciyar da dalibai na National Home-Grown School Feeding Programme da aka farfado da shi.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yaba da shirin, yana mai cewa ya zama abin koyi ga sauran jihohi wajen aiwatar da mulki tare da jama’a.

A nata jawabin, Minista a ma’aikatar  Ilimi, Farfesa Suwaiba Said Ahmad, ta jinjinawa Gwamna Namadi bisa manyan ayyukan cigaba da ke canza rayuwar jama’a.

 

Usman Mohammed Zaria

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Labarin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya ƙarya ne – Sarkin Musulmi
  • Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 
  • Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447
  • HKI Tana Ci Gaba Da Hana Wa Falasdinawa Abinci
  • Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Aikin Hanya Akan Kudi Sama Da Naira Biliyan 4
  • Muna Samun Gagarumin Cigaba Wajen Dawo Da Zaman Lafiya A Zamfara-Gwamna Lawal
  • Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro
  • Talauci ne babban maƙiyin ɗan Adam — Atiku