Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika
Published: 28th, October 2025 GMT
Idan muka kwatanta da kasar Sin, sabanin yawan albarkatun da Afrika ke da su kamar na kasar noma, ita Sin kasa da kaso 9 kadai take da shi, amma kuma tana bayar da gagagrumar gudunmawa a duniya, inda take tsaye da kafarta wajen ciyar da al’ummarta, har ma ta bayar da gudunmawa ga kasashe mabukata.
To mene ne dalilin nasarar Sin a wannan bangare?
Gaggarumar nasarar da Sin ta samu a bangaren aikin gona, ba wani abu ba ne illa jajircewar gwamnatin kasar da dabaru da fasahohin aikin gona da kullum ake lalubowa.
La’akari da yawan jama’a da yadda ta kasance koma baya, tabbas nahiyar Afrika na bukatar fasahohin Sin domin fitar da al’ummominta daga kangin talauci tare da wadatar da su da abinci. Dabaru da fasahohin Sin, za su yi wa bangaren aikin gona a nahiyar gagarumin garambawul, domin idan aka tabbatar da hada fasahohin da tarin albarkatun da nahiyar take da su, to kasashen Afrika za su iya tsayawa da kafarsu, su kuma fatattaki yunwa da talauci, da karfafa gwiwar matasa ta yadda za su rika ganin aikin gona a matsayin wata sana’a mai riba. Tabbas ingantattun fasahohin aikin gona na Sin, za su taka rawar gani wajen kyautata makomar nahiyar Afrika. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Mahajjata 2,235 Ne Suka Yi Rijistar Aikin Hajjin 2026 A Sokoto
A cewar Musa, shirye-shiryen sun hada da jigilar kayayyakin tafiya, masaukai da kammala yarjejeniyar ciyarwa da hukumomin da suka dace a Kasar ta Saudiyya.
A cewarsa, adadin mahajjatan da suka yi rajistar ya hada har da jami’an gwamnati.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA