Aminiya:
2025-10-28@14:46:45 GMT

Jami’an tsaro sun harbi matar aure sun lakaɗa wa jama’a duka a Katsina 

Published: 28th, October 2025 GMT

Al’ummar Unguwar Filin Samji da ke garin Katsina sun buƙaci hukumomi su tabbatar da adalci, bisan zargin da ake wa jami’an Hisbah da na Rundunar Tsaron Al’umma na gwamnatin jihar (C-Watch) da harbin mutane da kuma lakaɗa musu duka ba tare da dalili ba.

Wata matar aure mai suna Khadija Hamisu Wada ta samu raunuka sakamakon harbin bindiga, yayin da wasu mutane da dama suka ji raunuka bayan an kai musu hari da adduna, wuƙaƙe da sanduna.

A cewar mazauna yankin, aƙalla mutane bakwai ne suka ji munanan raunuka a lokacin da abin ya faru.

An ruwaito cewa Khadija na dauke da harsasai biyu a ƙugu, kuma likitoci sun gargadi cewa cire su da gaggawa na iya jawo mata matsalar laka.

Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 80 a Kebbi Rikicin ADC: Sanata Nenadi ta zama shugaba a Kaduna

Harsashi guda da ya shiga ƙafarta an cire shi, sai dai tana roƙon hukumomi su taimaka mata da magani da shari’a domin ceto rayuwarta.

Khadija ta shaida wa manema labarai cewa, “Na fita neman ɗana ƙarami Baba Aliyu ne, sai jami’an C-Watch suka harbe ni sau uku — sau biyu a ƙugu, da sau ɗaya a ƙafa. Har yanzu ina ɗauke da harsasai biyu a jikina.

“Likitoci sun ce sai sun matsa kafin a cire su, don kada a lalata ƙashin baya. Allah ne Kaɗai Ya san azabar da nake ciki.”

Khadija, uwa mai yara bakwai, ta fito ne daga gida mai ƙaramin karfi, kuma mijinta tsohon ma’aikaci ne da ke karɓar fansho.

Ta ce ba su da halin biyan kudin aikin tiyata da magunguna, don haka ta roƙi Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa da ya shiga lamarin don ceton rayuwarta.

Ta ce, “Tun bayan harin nake zuwa asibiti kullum amma babu mafita. Likitoci suna ce min in koma gida kawai. Ka yi tunanin rayuwa da harsasai a jikinka tsawon kwanaki tara zuwa goma, jikina yana ƙara lalacewa, ba na iya bacci ko kwanciyar hankali ba.”

’Yarta kaɗai da ke da aure, Maryam Hamisu Wada, ta dawo daga gidan mijinta don kula da ita da sauran ’yan gida. Ta bayyana cewa tun bayan harin ba ta samun nutsuwa ko barci, tana roƙon hukumomi su taimaka wajen ceton mahaifiyarta.

Maryam ta roƙi Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Katsina da gwamnatin jihar su ba da umarnin a karɓi mahaifiyarta a Asibitin Janar Amadi Rimi, don fara aikin tiyata na cire sauran harsasai biyu da ke jikinta.

‘’Yan Hisbah da C-Watch sun kawo mana hari’

Wani mazaunin yankin, Muhammad Shafiu, ya ce: “Ina zaune gaban gidan su budurwata muna hira sai jami’an Hisba da C-Watch suka zo da bindigogi da sanduna suka fara duka ba tare da wani bayani ba. Sun yi min rauni sosai har na suma. Ina rokon gwamnati ta tabbatar da adalci.”

Wani mutum mai suna Tijjani Abubakar shi ma ya shaida cewa, “Ina zaune bakin ƙofa sai jami’an Hisba da C-Watch suka iso. Ba tare da wani dalili ba suka fara dukan mu da sanduna har na ji raunuka da dama a jiki.

“Ina kira ga Gwamna Raɗɗa da ya ba da umarnin bincike don kauce wa maimaituwar wannan mummunan lamari.”

A nasa bangaren, Rabi’u Idris, ya ce shi baƙo ne da ya je yankin don sayen rago, amma aka doke shi har ya suma.

“Na yi ƙoƙarin bayyana musu cewa ba mazaunin yankin ba ne, amma suka ƙi sauraro. Sun doke ni har na fita daga hayyacina. Yanzu ina neman haƙƙina ta kotu har sai an tabbatar da adalci.”

Wani shaida da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, jami’an C-Watch sun kutsa gidan iyayensa suna zargin kanensa da rashin tarbiya.

“Sun razana iyayena, suka bugi iyayenmu, suka wulaƙanta mu ba tare da wani hujja ba. Muna neman adalci.”

Yanzu haka akwai fargaba a yankin, inda wasu mazauna ke barazanar ɗaukar doka a hannunsu, yayin da wasu ke roƙon gwamnati ta shiga tsakani.

Sun bayyana lamarin a matsayin cin zarafi da amfani da ƙarfi fiye da ƙima kan fararen hula.

Shaidu sun bayyana cewa jami’an Hisba aka fara kiran don sulhunta faɗa tsakanin wasu samari a yankin, amma lamarin ya rikiɗe zuwa tashin hankali bayan jami’an Hisba suka nemi taimakon jami’an C-Watch, wanda hakan ya janyo harbe-harben da dukan mutane.

Da yake mayar da martani, Kwamandan Ayyuka na Hukumar Hisba ta Jihar Katsina, Muhammad Musa, ya musanta zargin cewa jami’ansa ne suka harbi mutane, yana mai cewa jami’an Hisba ba su riƙe bindigogi.

Ya ce maimakon haka, ’yan daba na Filin Samji ne suka kai hari suka lalata ofishin Hisba da ke yankin.

Duk da irin kalubalen tsaro da ke addabar al’ummomin Katsina, mazauna jihar suna kira ga gwamnatin jihar da ta gudanar da cikakken bincike, ta ɗauki matakin gaggawa don dawo da aminci da amincewar jama’a a cikin birnin Katsina.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: C Watch Tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

Ɗalibi ya kashe abokinsa, ya binne gawarsa a rami a Filato

Wani ɗalibin Jami’ar Jos da ke Jihar Filato, ya kashe abokinsa, wanda shi ma ɗalibi ne a jami’ar, sannan ya binne gawarsa a bayan gidansu.

Wanda aka kashe mai suna Peter Mafuyai, ɗalibi ne da ke shekara ta uku a sashen hada-hadar kuɗaɗen banki.

Dangote na shirin faɗaɗa matatarsa don zama mafi girma a duniya Ba zan sake tsayawa takara ba, zan bai wa matasa dama — Dasuki

Ana zargin Nanpon Timnan da ke ajin shekara ta biyu daga sashen karatun harkar noma, da kashe shi sannan ya binne shi a rami.

Rahotanni sun bayyana cewar ɗaliban abokan juna ne sosai.

An ruwaito sun fita ƙwallon ƙafa, daga nan suka wuce wani waje sannan suka dawo gida.

“Da suka dawo Nanpon ya ɗauko adda. Abokansa da suke zaune tare a cikin gidan suka tambaye shi me zai yi da addar, sai ya ce yana son amfani da ita ne,” in ji wata majiya.

“Bayan haka sai ya sari abokinsa Peter da addar. Sauran abokan suka fara ihu suna tambayar dalilin da ya sa ya yi hakan, amma bai ba su amsa ba. Suka fita neman taimako, amma kafin su dawo, tuni ya binne gawar a bayan gidan.”

’Yan sanda sun riga sun gayyaci sauran abokan don yi musu tambayoyi, kuma ana ci gaba da bincike.

Zuwa yanzu dai babu cikakken bayani kan dalilin da ya sa ya yi kisan, sai dai wata majiya ta ce wataƙila sun sama saɓani.

Sakamakon yajin aikin ASUU da ake yi a jami’ar, babu ɗalibai ya bare a samu cikakken bayani ba.

Da aka tuntuɓi Shugabar riƙon ƙwarya ta Sashen Watsa Labarai na jami’ar, Tongdyen Dachung, ta ce ba za ta iya yin magana kan lamarin ba tukunna, domin tana buƙatar tabbatar da wasu bayanai.

Ita kuwa Shugabar Ƙungiyar Ɗaliban Jami’ar (SUG), Jane Pwajok, ta ce lamarin yana hannun ’yan sanda.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Filato, Alfred Alabo, bai yi nasara ba, domin ba ya ɗaga waya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rikicin adawa da cin zaben Shugaba Paul Biya ya bazu a Kamaru
  • Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 80 a Kebbi
  • Ɗalibi ya kashe abokinsa, ya binne gawarsa a rami a Filato
  • Ɗalibi ya kashe abokinsa, ya binne shi a rami a Filato
  • Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai
  • Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano
  • An ba da tallafin N2m ga iyalan jami’in NSCDC da aka kashe a Jigawa 
  • Farfesa Muhammed Khalid Othman Ya Zama Sabon Shugaban Jami’ar Tarayya Ta Dutsinma
  • ABU ta musanta zargin ƙera makamin nukiliya a ɓoye