An bukaci masu hannu da shuni da ‘yan kasuwa da ma daidaikun jama’a su rika tallafawa mata da matasa da dukkanin abin da Allah ya hore mu domin ganin sun iya dogara da kansu.

Kogunan Kasar Hausa Alhaji Aliyu Da’u Abubakar ne yayi wannan kiran a wajen bada tallafi ga mata da matasa fiye da dari hudu da Kungiyar Matasan Abban Gandun Albasa Kano ta shirya a Kano.

Kogunan Kasar Hausa ya bayyana cewa irin wannan tallafi zai taimaka matukar gaske wajen karfafa mata da matasa su tsaye da kafafun su.

Yayi bayanin cewa babu shakka wadannan matasan zasu dogara da kansu kana da daukar dawainiyar iyalansu da wannan tallafi.

Taron da aka gudanar a asabar ta karshen mako ya shedi yadda mata da matasa suka sami tallafi kudi daga Naira dubu goma zuwa ashirin dai dai da yadda Allah ya tsaga da rabon mutum.

Wannan tallafin da aka ba masu kananan sana’o’i zai taimaka matukar gaske a cewa Uban Taron kuma Kogunan Kasar Hausa Alhaji Aliyu Da’u Abubakar lokacin da yake magana da Radiyo Nijeriya Kaduna.

Daga cikin wadanda suka amfani da wannan tallafin wacce tayi magana a madadin dukkanin wadanda suka amfana Zainab Adamu tayi godiya ga Kungiyar Matasan Matasan Abban Gandun Albashi da wannan jinkai da ya musu.
Cov/Zainab Adamu

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: wannan tallafi

এছাড়াও পড়ুন:

Sheikh Ibrahim Zakzaky Ya Taya JMI Murnar Nasara A Kan Mikiyanta

Shugaban Kungiyar Harka Islamia a tarayyar Najeriya Sheikh Irahim Zakzaky ya taya mutanen kasar murna saboda nasarar da suka samu kan HKI da kuma Amurka a yakin kwanaki 12 a cikin watan da ya gabata.

Ya ce wannan nasarar bata takaita da mutanen kasar Iran kadai ba , hada har da al-ummar Musulmi da kuma da kuma masu sun yenci a ko ina suke.

Ya kuma yaba da yadda gikuwan nmalamai na kasar Iran suka sami nasarar kare kasar daga mafi yawan hare-haren  HKI a kan kasar.

Ya bayyana cewa Iran ta sami nasara a kan kasashen yamma da makamai wadanda suka fi nasu karfi da inganci, har’ila yau sun sami nasara a kan ma;aikatan yahudawan da suke taimaka masu a cikin kasar. Daga karshe yace kasashen yamma sun yo kokarin boye wannan shan kayen da suka yi a hannun Iraniyawa tare da taimakon All.. ya kuma ji dadi yadda wannan yakin ya kara hada kan mutanen kasar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilin da matan karkara a Kano suka fi son haihuwa a gida
  • Bidiyon tsiraici: Babiana ta sake jawo ce-ce-ku-ce
  • Mutane 21 Suka Mutu A Hatsarin Mota A Hanyar Zaria Zuwa Kano
  • Sheikh Ibrahim Zakzaky Ya Taya JMI Murnar Nasara A Kan Mikiyanta
  • Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Tunisiya Da Ci 3-0 A Moroko
  • Xi Ya Ba Da Amsar Wasikar Matasan Amurka ’Yan Wasan Kwallon Pickle Bisa Ziyartar Sin
  • Muhimman Kamfanonin Jiragen Sama A Duniya Sun Farfado Da Zirga-Zirgaf Zuwa Iran
  • Gobe Za A Fara Wasannin Kofin Afirka Na Mata
  • Gonakin Koko: Mata sun yi barazanar zanga-zanga tsirara a Kuros Riba