’Yan kasuwar duwatsu masu daraja na ɗaukar nauyin ta’addanci —EFCC
Published: 28th, October 2025 GMT
Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan Najeriya.
Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci ta kowace hanya, tana mai jan hankalinsu da su daina harkokin da ke hana ci gaban tattalin arziki da tsaro a ƙasar.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya faɗi haka a Ibadan, hedikwatar Jihar Oyo, yayin taron wayar da kai da horaswa na rana ɗaya da aka shirya domin masu haƙar ma’adinai da ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a jihar.
Taron ya samu haɗin gwiwa tsakanin EFCC da Hukumar Bayar da Bayanai kan Harkokin Kuɗi (NFIU) tare da tallafin GIZ, wata cibiyar haɗin gwiwar Jamus.
Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 80 a Kebbi Rikicin ADC: Sanata Nenadi ta zama shugaba a KadunaOlukoyede, wanda ya bayyana takaicinsa kan halayen wasu ’yan kasuwar, ya ce akwai “ tsananin rashin kula” daga ɓangaren masu haƙar ma’adinai da ’yan kasuwar duwatsu masu tsada, musamman wajen bin dokar sanin abokin hulɗa (KYC).
Ya koka kan yadda ake kin bayar da rahoton mu’amaloli masu alamun shakku, yana mai cewa hakan na kawo cikas ga yunkurin EFCC wajen yaƙi da safarar kuɗaɗen haram da kuma tallafin ta’addanci a Najeriya.
Shugaban EFCC ya yi wannan jawabi ne ta bakin Toyin Ehindero-Benson, Kwamandan Ofishin Kula da Safarar Kuɗaɗen Haram (SCUML) na shiyyar Ibadan, inda ta buƙaci mahalarta taron su koyi cikakkun ƙa’idojin da ke jagorantar ayyukan SCUML.
Ta ce hakan zai taimaka musu wajen fahimtar nauyin da ke kansu da kuma bin ƙa’idojin yaƙi da safarar kuɗaɗe da kuma hana ɗaukar nauyin ta’addanci, musamman ma a matsayinsu na manyan masu ruwa da tsaki a fannin haƙar ma’adinai.
A cewar sanarwar da kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya fitar, Olukoyede ya bayyana cewa: “Halin wannan fanni na haƙar ma’adinai yana sanya shi zama muhimmin ɓangare a yaƙi da laifukan kuɗi.
“Wannan taro kuma wata dama ce ta musayar ra’ayoyi, faɗakarwa, da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da masu ruwa da tsaki.”
A nasa jawabin, Michael Etuk, Mataimakin Shugaban Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Duwatsu Masu Tsada ta Ojoo, Jihar Oyo, ya tabbatar wa EFCC cewa ’yan kasuwa da masu haƙar duwatsu a jihar za su yi duk abin da doka ta tanada domin taimaka wa gwamnati wajen ƙarfafa yaƙi da safarar kuɗaɗen haram da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: duwatsu masu daraja yan kasuwar duwatsu masu haƙar ma adinai
এছাড়াও পড়ুন:
Tanka ta kife yayin da man fetur ya zube a kan titi a Neja
Wata tanka ɗauke da man fetur ta kife a kan hanyar Lambata zuwa Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja, lamarin da ya haifar da tsoro da fargaba a tsakanin mazauna yankin.
An gano cewa tankar, wadda ta taso daga Legas tana kan hanyarta na zuwa Kano, ta kife ne da sassafe a garin Takalafiya da ke Ƙaramar Hukumar Lapai ta Jihar Neja.
Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a Najeriya Matsalar kashe-kashe a Nijeriya ba ta da alaƙa da addini — Femi KayodeWani mazaunin garin Lapai, Mallam Mahmud Abubakar, ya shaida wa Aminiya cews lamarin ya faru kimanin kilomita biyu daga garin Lapai.
Ya ce kwanan nan aka gyara hanyar NNPCL, amma hanyar ta fara lalacewa cikin ƙanƙanin lokaci.
Wani ganau mai suna Mohammed Hassan Sonmaji ya ce, saurin zuwan jami’an kashe gobara na Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBUL) tare da na Hukumar Tsaro ta NSCDC ne ya taimaka wajen kauce wa mummunan hatsari a hanyar.
Ya ƙara da cewa jami’an ƙungiyar NUPENG reshen Lapai, sun isa waje don taimakawa wajen shawo kan lamarin.
An zagaye wani ɓangare da man ya zube domin gujewa aukuwar hatsari.
Da aka tuntubi Daraktan Sashen Bayani da Harkoki na Musamman na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Dokta Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da cewa babu abin zai auku.
Ya bayyana cewa tankar ba ta kama da wuta ba, kuma motocin kashe gobara na jami’ar IBBUL suna tsaye a wajen don shirin ko-ta-kwana.