Juventus ta kori kocinta Igor Tudor
Published: 28th, October 2025 GMT
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta kori kocinta, Igor Tudor, bayan da ta sha kashi da ci 1-0 a hannun Lazio, lamarin da ya ba ta damar haɗa maki biyar kacal a wasanni biyar da ta buga a baya-bayan nan.
A cewar wata sanarwar da kulob ɗin ya fitar a ranar Litinin, Massimiliano Brambilla, wanda shi ne kocin tawagar maza ta farko, zai jagoranci Juventus a wasan da za ta kara da Udinese a ranar Laraba.
“Juventus FC na sanar da cewa ta sallami Igor Tudor daga matsayin kocin tawagar maza ta farko, tare da sauran jami’ansa da suke taimaka masa a aikin horarswa — Ivan Javorcic, Tomislav Rogic da Riccardo Ragnacci,” in ji sanarwar.
Kulob ɗin ya gode wa Tudor da tawagarsa bisa kwazon da suka nuna a watannin da suka jagoranci kungiyar, yana yi musu fatan alheri kan duk lamuransu a nan gaba.
Yanzu haka Juventus tana mataki na takwas a teburin Serie A, da tazarar maki shida tsakaninta da Napoli wadda ke jan ragamar gasar.
A kofin Zakarun Turai na Champions League kuwa, Juve na matsayi na 25 cikin ƙungiyoyi 36 bayan ta yi canjaras ɗaya da kuma shan kashi a wasanni biyu na farko.
Tudor, tsohon ɗan wasan tsakiya na Croatia mai shekara 47, ya buga wasa da Juventus a lokacin yana murza leda, inda a watan Maris na bana kuma ya karɓi ragamar kulob ɗin daga hannun Thiago Motta.
Tun daga ranar 10 ga Satumban bana, Juventus ta buga wasanni takwas ba tare da samun nasara ba, ciki har da wasanni huɗu na bayan nan da ba ta zura ƙwallo ko ɗaya ba.
Alƙalumma sun nuna cewa Tudor ya samu nasara a wasanni 10 da ya jagoranci Juventus, sannan ya yi canjaras 8, da shan kashi sau shida.
Rahotanni na cewa wannan dai shi ne yanayi mafi muni da kulob ɗin ya fuskanta a baya-bayan nan, duk da cewa ya kashe euro miliyan 130 wajen cefanen ’yan wasa.
Daga cikin sabbin ’yan wasan da Juventus ta saya akwai Francisco Conceição, Nico González, Edon Zhegrova, da masu tsaron baya — Lloyd Kelly da Piere Kalu. Sai kuma Loïs Openda da ta ɗauko aro da Jonathan David da kulob ɗin ya ɗauko kyauta.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba
Shugaba Tinubu, a cikin wasikarsa, ya ce, an yi nadin ne bisa tanadin Sashe na 18(1) na Dokar Sojojin Kasa, Cap A20, ta Dokokin Tarayyar Nijeriya, 2004.
Ya bukaci Majalisar Dattawa da ta yi la’akari da wannan bukatar don gaggawa kan tabbatar da daidaito mai inganci a cikin tsarin tsaron kasar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA