Tinubu ya gana da sabbin hafsoshin tsaro
Published: 27th, October 2025 GMT
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da sabbin hafsoshin tsaron Najeriya a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Sai dai babu wani cikakken bayani kan dalilin ko maudu’in wannan taron, wanda shi ne karo na farko bayan sauya manyan hafsoshin tsaron Najeriya da shugaban ƙasar ya yi.
An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi Zanga-zanga ta ɓarke a KamaruSai dai wata majiya daga fadar shugaban kasar ta ce taron ba zai nasaba da ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa tsarin tsaro da inganta aikin rundunar sojoji a ƙasar nan ba.
Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne Shugaba Tinubu ya tuɓe hafsan hafsoshin Najeriya, Janaral Christopher Musa da sauran hafsoshin tsaron ƙasar, a wani sauyi a tsarin jagorancin sojin ƙasar domin inganta da ƙarfafa sha’anin tsaro a Najeriya.
Wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta ce Tinubu ya yi musu fatan alkairi tare da bayyana sunayen sabbin hafsoshin da za su maye gurbin waɗanda aka sauke ɗin.
Sabbin hafsoshin tsaron da Tinubu ya nada sun hada da Janar Olufemi Oluyede — Hafsan Hafsoshi da Manjo Janar W Sha’aibu — Hafsan sojojin ƙasa da Air Vice Marshall S.K Aneke — Hafsan sojin sama.
Akwai kuma Rear Admiral I. Abbas — Hafsan sojin ruwa da Manjo Janar E.A.P Undiendeye — Shugaba sashen tattara bayan sirri na soji.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hafsoshin tsaro sabbin hafsoshin tsaro hafsoshin tsaron
এছাড়াও পড়ুন:
Zanga-zanga ta ɓarke a Kamaru
Rahotonni sun bayyana ɓarkewar zanga-zanga a birnin Douala, cibiyar kasuwancin Kamaru jim kadan bayan sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar.
Wasu bidiyoyi da aka yaɗa a dandalan sada zumunta sun nuna gomman mutane sun fantsama kan titunan birnin, tare da rera waƙoƙin goyon bayan Issa Tchiroma Bakary, jagoran adawar ƙasar.
An rufe makarantu saboda ƙarancin man fetur a Mali Paul Biya mai shekara 92 ya lashe zaɓen KamaruKamfanin dillancin labaran Kamaru, ya wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda aka lalata wani ginin majalisar birnin, bayan da masu zanga-zangar suka far masa.
BBC ya ruwaito cewa, a yayin da ake ci gaba da zaman ɗar-ɗar kan abin da ka iya faruwa bayan sanar da sakamakon zaɓen Kamaru, makarantu da shaguna sun kasance a rufe a Yaoundé, babban birnin ƙasar.
Hatta ma’aikatan gwamnati da dama sun ƙi fita wuraren ayyukansu saboda fargabar abin da ka iya biyo bayan sanar da sakamakon zaɓen.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa girke jami’an tsaro masu yawa a manyan birane, musamman Yaoundé, Douala da kuma Garoua, mahaifar jagoran adawa Tchiroma Bakary, ya taƙaita zanga-zangar da aka fara gudanarwa.
Kawo yanzu, yawancin ‘yan ƙasar sun ci gaba da kasancewa a cikin gidajensu bayan da aka bayyana Shugaba Paul Biya a matsayin wanda ya lashe zaɓen, wanda hakan ke tabbatar masa da wa’adin mulki na takwas.
Shugaba Paul Biya shi aka sanar a hukumance a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa karo na takwas a cewar Kotun Tsarin Mulkin Kamaru, yayin da tun farko jagoran ’yan adawa Issa Tchiroma Bakary ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara.