A nasa bangare kuwa, ministan kimiyya da kirkira na Afirka ta Kudu, Dr. Blade Nzimande, ya bayyana ta kafar bidiyo cewa, ya gamsu da babban nasarar da Sin ta samu a wa’adin shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 14. Ya ce, duk da kalubalen da duniya ke fuskanta, tattalin arzikin Sin ya samu ci gaba mai karfi ba tare da tangarda ba, kuma yana karawa tattalin arzikin duniya kwarin gwiwa.

 

Ya ce Afirka ta Kudu tana fatan koyi daga sabon tsarin ci gaban Sin, don karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannonin da suka shafi sauyin yanayi, da tattalin arzikin dijital, da fasahar sararin samaniya da sauransu. (Amina Xu)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona October 28, 2025 Daga Birnin Sin Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin October 28, 2025 Daga Birnin Sin An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas October 28, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Babbar Kasuwar Fim Ta Sin Babbar Damar Nollywood Ce

Zuwa karfe 5:41 na daren ranar 7 ga watan Disamba, fim din Amurka “Zootopia 2” wanda aka fara nuna wa kwanaki 12 da suka wuce (tun daga ranar 26 ga Nuwamba), ya samu kudaden shiga a cikin kasar Sin da yawansa ya wuce yuan biliyan 30 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 424.8, adadin da ya zarce kudaden shiga da ya samu a kasashen Arewacin Amurka, har ya sa kasar Sin ta zama kasa mafi taka rawa wajen samar da kudin shiga ga wannan fim a duniya. Hakan kuma ya nuna yadda Sin ke da babbar kasuwar fina-finai.

Ibrahim Akopari Ahmed, jami’in kula da harkokin cinikayya a Najeriya, a zantawarsa da dan jarida a baya, ya taba bayyana cewa, “Najeriya na daya daga cikin manyan kasashe mafiya karfin tattalin arziki a Afirka, kuma sana’o’i masu alaka da samar da hidimomi ne ke ba da gudunmawa mafi yawa ga GDPn kasar, wanda ya zarce kashi 50 cikin 100 na GDP. Saboda haka, Najeriya tana da karfi a bangaren sana’o’in samar da hidimomi, musamman a fagen nishadantarwa, kamar masana’antun samar da fina-finai ta Najeriya (Nollywood). A wannan fage, muna kan gaba a Afirka.”

Najeriya babbar kasa ce ta samar da fina-finai a Afirka, yayin da Sin ke da babbar kasuwar kallon fina-finai. Hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta fannin fina-finai yana da makoma mai haske, kuma a hakika Sin da Najeriya na karfafa hadin gwiwa a wannan fanni. Alal misali, an gudanar da bikin fina-finai na kasa da kasa na Zuma karo na 15 a farkon wannan watan a babban birnin Najeriya Abuja, inda aka nuna fina-finai biyu daga Sin: wato “Rooting” da “Shen Zhou 13”. Babban manajan kamfanin samar da fina-finai ta Najeriya Ali Nuhu ya bayyana cewa, yana fatan ta wannan taron, za a kara zurfafa hadin gwiwar sana’o’in samar da fina-finai tsakanin Sin da Najeriya. Muna fatan a karkashin tsarin “dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka” da ma sauran irin dandalin hadin gwiwa, Sin da Najeriya za su kara karfafa huldar al’adunsu, ta yadda a nan gaba za a samu karuwar shigowar kyawawan fina-finai daga Najeriya zuwa nan kasar Sin, don baiwa masu kallo na kasar Sin karin damammaki na fahimtar Afirka, musamman Najeriya.(Mai zane da rubutu: MINA)

ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Ya Kamata Amurka Ta Daina Sa Hannu Cikin Harkokin Najeriya December 4, 2025 Ra'ayi Riga Duniya Za Ta Kara Kyau In Ba A Nuna Fin Karfi December 4, 2025 Ra'ayi Riga Layin Dogon Da Zai Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Wajen Zamanantar Da Kansu November 29, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Taron Abuja kan Tattaunawakan Tattalin Arziki Kasa- “Akwai yiyuwar tattalin arzikin kasa zai murmure a shekarar 2026”
  • Kamfanin CRCC Ya Kammala Shimfida Hanyar Jirgin Kasa A Gadar Layin Dogo Mafi Tsawo A Afrika Dake Algeria
  • Yadda Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samar Da Karin Damammaki Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Kamfanonin Sin Sun Kera Tare Da Sayar Da Motoci Sama Da Miliyan 31 Tsakanin Janairu Zuwa Nuwamban Bana
  • Bankin Duniya Ya Daga Hasashen Ci Gaban Tattalin Arzikin Sin Na 2025 Da Maki Kaso 0.4
  • Nazarin CGTN: Fahimtar Matsayin Sin Cikin Yanayin Tattalin Arzikin Duniya Na Da Muhimmanci
  • Shugabannin Sin Sun Yi Taron Koli Na Tattauna Aikin Raya Tattalin Arziki Don Tsara Abubuwan Da Za A Aiwatar A 2026
  • Gwamnatin Jigawa Ta Kara Samar da Shirye-shiryen Inganta Rayuwar Masu Buƙata ta Musamman
  • Babbar Kasuwar Fim Ta Sin Babbar Damar Nollywood Ce
  • Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Sha Alwashin Wadata Al’ummarsa da Tsaftataccen Ruwan Sha