Aminiya:
2025-12-13@17:53:13 GMT

Rikicin ADC: Sanata Nenadi ta zama shugaba a Kaduna

Published: 28th, October 2025 GMT

Rikicin Jam’iyyar ADC na Jihar Kaduna ya ɗauki sabon salo, bayan da uwar jam’iyyar ta nada tsohuwar Ministar Kuɗi, Sanata Nenadi Usman, a matsayin Shugabar Hadakar Jam’iyyar a jihar.

Haka kuma jam’iyyar ta nada tsohon Kwamishinan Kudi na Jihar Kaduna, Bashir Sa’idu, na hannun daman tsohon gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufa’i, a matsayin Mataimakin Shugaban Haɗakar.

Da yake jawabi yayin taron manema labarai, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa (Arewa maso Yamma), Ja’afaru Sani, ya bayyana cewa manufar ADC ita ce haɗa kan shugabannin jam’iyyun adawa a Kaduna domin ƙarfafa dimokuradiyya da shigar kowa cikin harkokin siyasa.

Ya ce shugabannin Haɗakar sun ƙuduri aniyar sake farfaɗo da jam’iyyar da kuma haɗa kan jama’a don kawo ƙarshen abin da ya kira “mulkin danniya na Jam’iyyar APC a jihar da ƙasa baki ɗaya.”

Tinubu ya gana da sabbin hafsoshin tsaro Alassane Ouattara ya lashe zaɓen Ivory Coast karo na huɗu

“A bisa wannan tsari na sake gina jam’iyyar da samar da shugabanci mai tsari, mun tabbatar da naɗin Sanata Nenadi Usman a matsayin Shugabar Hadakar ADC a Jihar Kaduna, tare da Alhaji Bashir Sa’idu a matsayin Mataimakinta.

“Da wannan mataki, ita ce za ta zama ginshiƙin hada kai da shirya ayyukan Haɗakar jam’iyyar a jihar,” in ji shi.

Ja’afaru Sani ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da ƙoƙarin raba kawunan shugabannin jam’iyyun adawa a jihar, amma ya ce ADC za ta tsaya tsayin daka wajen kare haɗin kanta.

“Mun lura cewa a ƙoƙarinsu na kawo rabuwar kai, wasu ’yan siyasa da ake amfani da su sun ɗauki nauyin wasu mutane don kai ƙara kotu a kan wasu shugabannin Haɗakar, ciki har da Mallam Nasir El-Rufa’i da ni kaina,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, shugabannin Haɗakar sun cimma matsaya ɗaya ta kora da hana shiga ayyukan jam’iyya ga dukkan mambobin da ke da hannu ƙarar da aka shigar a kotu kan El-Rufa’i da sauran shugabannin jam’iyyar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Haɗakar jam iyya Jam iyyar a jam iyyar a

এছাড়াও পড়ুন:

Shugabannin Sin Sun Yi Taron Koli Na Tattauna Aikin Raya Tattalin Arziki Don Tsara Abubuwan Da Za A Aiwatar A 2026

Mahukuntan kasar Sin sun gudanar da taron koli, na tattauna aikin raya tattalin arzikin kasar, don tsara abubuwan da za a aiwatar a shekarar 2026 dake tafe. An gudanar da taron ne a jiya Laraba da yau Alhamis, inda shugabannin kasar suka tantance abubuwa mafiya muhimmanci, wadanda za a aiwatar, dangane da raya tattalin arzikin kasar a shekara mai kamawa.

Cikin muhimmin jawabi da ya gabatar yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya waiwayi aikin raya tattalin arziki da Sin ta aiwatar a shekarar nan ta 2025, tare da fayyace halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, da ma aikin da aka tsara gudanarwa a shekara mai zuwa.

Yayin taron, an yi amannar cewa shekarar 2025 ta fita daban, kuma za a kai ga cimma nasarar muradun raya tattalin arziki, da zamantakewar al’ummar kasar Sin na shekarar ta bana.

ADVERTISEMENT

Taron ya kuma tabbatar da cewa, aikin raya tattalin arzikin Sin na shekara mai zuwa, zai karkata ne ga ayyuka irinsu bunkasa sayayya a cikin gida, da ci gaba wanda kirkire-kirkire ke ingizawa, da kara bude kofar kasar Sin ga sassan waje, da cikakken salon sauyi zuwa ci gaba marar dumama yanayi, da kyautata rayuwar al’umma. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kamfanin CRCC Ya Kammala Shimfida Hanyar Jirgin Kasa A Gadar Layin Dogo Mafi Tsawo A Afrika Dake Algeria December 11, 2025 Daga Birnin Sin Yadda Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samar Da Karin Damammaki Ga Kasashe Masu Tasowa December 11, 2025 Daga Birnin Sin Kamfanonin Sin Sun Kera Tare Da Sayar Da Motoci Sama Da Miliyan 31 Tsakanin Janairu Zuwa Nuwamban Bana December 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • EFCC na ƙoƙarin daƙile muradin Malami na yin takarar gwamna — ADC
  • Shugaba Tinubu Ya Karrama Shugaban NPA Da Lambar Yabo Ta Musamman
  • 2027: Jam’iyyar NNPP ta rantsar da sabbin shugabanni a Gombe
  • Zaɓen 2027 ya hana ni korar wasu ma’aikata – Bago
  • Yadda APC Da ADC Ke Amfana Da Rikicin Jam’iyyar PDP
  • Nazarin CGTN: Fahimtar Matsayin Sin Cikin Yanayin Tattalin Arzikin Duniya Na Da Muhimmanci
  • Shugabannin Sin Sun Yi Taron Koli Na Tattauna Aikin Raya Tattalin Arziki Don Tsara Abubuwan Da Za A Aiwatar A 2026
  • Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin Gwamnan Bayelsa
  • Kremlin: Putin Ya Bayyana Wa Shugaba Maduro  Na Venezuela Goyon Bayansa
  • Gwamnan Kano ya naɗa mace ta farko a matsayin shugabar Jami’ar Northwest