Amurka ta soke bizar Wole Soyinka
Published: 28th, October 2025 GMT
Fitaccen marubucin nan ɗan Nijeriya wanda ya taɓa lashe kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya ce gwamnatin Amurka ta soke bizarsa tana mai haramta masa shiga ƙasar.
Farfesa Soyinka ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da ya kira a Legas a ranar Talatar nan.
Netanyahu ya ba da umarnin kai mummunan farmaki a Gaza Juventus ta kori kocinta Igor TudorYa bayyana cewa Ofishin Jakadancin Amurka ne ya sanar da shi batun ƙwace bizar a wata wasiƙa da ya aike masa.
Sai dai ya sanar da cewa ba shi da masaniya kan wani mummunan laifi da ya aikata da har zai sa Amurkan ta soke bizar da ta ba shi.
“Ya zama dole ne na kira wannan taron saboda mutanen Amurka da ke tsammanin zuwana wasu taruka da cewa kar su ɓata lokacinsu.
“Ba ni da biza; an haramta min shiga Amurka. Saboda haka idan kuna son ganina, kun san inda za ku same ni,” in ji Soyinka.
“Har yanzu ina bibiyar tarihina na baya… Ba ni da wani tarihin aikata laifuka a baya ko ma babban laifi ko rashin ɗa’a da zai sa in cancanci a soke min biza.
“Na fara waiwayen baya—shin na taɓa yi wa Amurka wani rashin adalci? Shin ina da wani mugun tarihi? An yanke min hukunci? Shin na saɓawa wata doka a ko’ina?”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Farfesa Wole Soyinka
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗaliban Jami’ar Unijos 8 sun mutu a hatsarin mota
Aƙalla ɗalibai takwas na Jami’ar Jos ne aka ruwaito sun mutu, yayin da wasu uku suka samu munanan raunuka, a wani mummunan hatsarin da ya rutsa da wata tirela da wata motar bas.
Hatsarin ya faru ne a hanyar Zariya, cikin ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.
NAFDAC ta lalata kayayyakin Naira biliyan 5 a Jihar Nasarawa Zanga-zanga ta ɓarke bayan haɗarin tirela ta kashe mutum a YobeLamarin ya faru ne da misalin ƙarfe biyu na tsakar daren ranar Alhamis lokacin da ɗaliban ke dawowa daga wani biki.
Jami’in kula da wayar da kan jama’a na hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) Peter Yakubu Longsan ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa motar bas ɗin na ɗauke da ɗalibai 11 na Jami’ar.
A cewar Hukumar ta FRSC, shaidun gani da ido sun danganta hatsarin da tsananin gudu na direban motar yake yi na wuce gona da iri.
Da yake bayar da cikakken bayani kan lamarin, Longsan ya bayyana cewa, “A yau 11 ga Disamba, 2025, Hukumar FRSC reshen Jihar Filato ta samu kiran waya da misalin ƙarfe 02:30 na tsakar dare, inda aka ba da rahoton wani haɗarin mota da ya afku a kusa da hanyar Zariya wajen Unity Bank, a Jos.
“Hatsarin ya haɗa da motoci biyu, tirela da bas, mutum 11 ne a cikin motar kuma an ce ɗaliban jami’ar Jos ne. Da faruwar lamarin ne mutum bakwai ake zargin nan take sun mutu, domin daga ƙarshe likita ya tabbatar da cewa sun mutu, sai kuma wani da ya mutu a asibitin wanda ya kawo adadin waɗanda suka mutu zuwa takwas.
“A yanzu haka wasu uku suna karɓar magani a asibitin, dukkan waɗanda abin ya rutsa da su maza ne, kamar yadda wani ganau ya shaida cewar motar bas ɗin na cikin tsananin gudu, lamarin da ya kai ga rasa natsuwa daga bisani kuma lamarin ya faru. A halin yanzu dai ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike,” in ji shi.