Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja
Published: 22nd, October 2025 GMT
Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin cikinta game da gobarar tankar mai da ta tashi a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja, inda mutane 38 suka rasa rayukansu.
A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta jajanta wa jama’a da gwamnatin Jihar Neja, musamman iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma Gwamna Mohammed Umar Bago.
“Tunaninmu yana tare da iyalan da wannan mummunan lamari ya shafa. Muna godiya ga ma’aikatan agajin gaggawa bisa taimakon da suka bai wa waɗanda abin ya rutsa da su,” in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta kuma yi kira da a ƙara kulawa da tsaro, musamman wajen adanawa da jigilar kayan da ke iya kamawa da wuta cikin sauƙi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Dan Wasan Barkwanci A Finafinan Indiya, Asrani Ya Rasu
Fitaccen jarumin barkwancin finafinan Indiyan nan Asrani ra rasu.
Asrani, wanda asalin sunansa shi ne Govardhan Asrani, ya rasu yana mai shekaru 84, kuma ya shafe sama da shekara 50 yana fitowa a finafinan Indiya, inda ya fito a finafinai sama da 350.
Dan wasan finafinan, ya shahara wajen taka rawar barkwanci da kuma ƙaramin jarumi wanda ake kira da mai taimaka wa jarumi wato supporting actor. Daga cikin fina-finansa da suka yi fice akwai Sholay, inda ya fito a matsayin ɗansand da Bawarchi da Chupke-Chupke da Hera Pheri da Muqabla da Dhamaal da Yamla Pagla Deewana da Dillagi da Welcome da Bhool Bhulaiya da Garam Masala da Baghban da The Burning Train da Ajnabee da Seeta aur Geeta da Sargam da dai sauransu.
Ya karbi lambobin yabo da dama da suka hada da jarumin da yafi kowa iya barkwanci wanda kamfanin Film Fare ya ba shi.
Ya mutu ya bar matarsa wadda ita ma jaruma ce wato Manju Asrani da kuma ɗansa Naveen Asrani.
Ya yi fina-finai da jarumai da dama da suka hada Amita Bachchan da Dharamendra da Jeetandra da Shatugan Sinha da Rajesh Khanna da Rishi Kapoor da Vinod Khanna da Akshay Kumar, da Shahrukh Khan da Aamir Khan da Salman Khan da Ajay Devgan da Sanjay Dutt da dai sauransu.
Bbc