Aminiya:
2025-12-12@15:51:30 GMT

Rikicin adawa da cin zaben Shugaba Paul Biya ya bazu a Kamaru

Published: 28th, October 2025 GMT

Rikici na kara bazuwa a Jamhuriyar Kamaru kwana guda bayan Kotun Kolin  ta tabbatar da Shugaba Paul Biya a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa mai cike da takaddama.

Dan takarar jam’iyyar adawa, Issa Tchiroma Bakary, ta sake bayyana cewa ba zai amince da sakamakon zaben ba, yana mai cewa “zaben ba sahihi ba ne” yana mai yin fatali da nasarar Shugaba Biya.

Sanarwar sakamkon ta janyo zanga-zanga, kone-kone da fada a tsakanin jama’a da jami’an tsaro a biranen Douala da Mbouda da Bertoua da Batouri, inda ake ci gaba da samun rikice-rikice lalata dukiyoyi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ana ci gaba da kona gine-gine da farfasa abubuwa, da satar kaya a wasu manyan birane ciki har da Douala Mbouda da Bertoua.

’Yan bindiga sun sa harajin N15m kan al’ummar Mazabar Sanata Tambuwal Jami’an tsaro sun harbi matar aure sun lakaɗa wa jama’a duka a Katsina 

Bayanai sun nuna cewa ofishin ’yan sanda na tsakiya a Bertoua na cikin barazana, yayin da masu zanga-zanga suka mamaye tituna a Batouri da ke yankin gabas, lamarin da ya haddasa tashin hankali mai tsanani.

A yankunan Mbanga da Njombé da Souza, jita-jitar zuwan ’yan tawayen Ambazonian ta sanya malamai sun rufe makarantu, suka sallami ɗalibai gida, abin da ya ƙara haifar da fargaba da rudani a tsakanin al’umma.

Jami’an tsaro sun mayar da martani ta hanyar harbe-harbe da hayake mai sanya hawaye da kuma ruwan zafi, domin tarwatsa masu zanga-zanga, wadda aka fara cikin lumana, kafin ta rikide zuwa tarzoma a sassan ƙasar.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun kwato buhunan shinkafa da aka sata yayin tarzomar da ta faru a Douala.

Wani ɗan jarida ya bayyana cewa halin da ake ciki yana sauyawa , inda ake sa ran wasu yankuna za su iya shiga cikin hatsaniya nan gaba kadan.

A halin yanzu, ƙungiyar Amnesty International Africa ta roƙi hukumomin Kamaru su girmama haƙƙin jama’a na gudanar da zanga-zanga cikin lumana, tare da yin bincike mai zaman kansa cikin gaskiya kan mutuwar da aka samu a yayin tarzomar.

Haka kuma, rahotanni daga yankin Yamma, musamman a garin Bafoussam, sun nuna cewa ana jin sautin harbe-harbe da ke ƙara tayar da hankalin jama’a.

A Souza da Njombe na yankin Littoral, jama’a sun shiga rudani bayan jita-jitar cewa ’yan tawayen Ambazonia sun kutsa garuruwan, abin da ya sa iyaye suka yi tururuwa don kwashe ’ya’yansu daga makarantu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Issa Tchiroma Bakary Kamaru Paul Biya tarzoma

এছাড়াও পড়ুন:

Sakamkon Jin Ra’ayi: Yawancin Amurkawa suna adawa da yunkurin kai hari kan Venezuela

Galibin Amurkawa na adawa da yunkurin gwamnatin kasar na neman kai harin soji kan Venezuela da sunan murkushe safarar miyagun kwayoyi.

Ayyukan sojin Amurka a yankin ya zuwa yanzu sun sanadiyar mutuwar mutane 87, sanann kuma  ana gudanar da su ne ba tare da izini daga alkali ko kotuko kuma majalisar dokoki  ba.

Binciken ya nuna cewa kashi 48 cikin 100 na wadanda aka ji ra’ayoyinsu sun nuna adawa da da harin, yayin da kashi 34% ke nuna goyon bayansu, kuma kashi 18% ba su da ra’ayi.

Masu adawa da Shirin sun fi yawa a tsakanin ‘yan jam’iyyar Democrat, inda kashi 80% na ‘yan jami’iyar na adawa da wadanna ayyukan  kashi 9% cikinsu ne kawai ke nuna goyon baya. A cikin ‘yan Republican, 67% sun goyi bayan harin, kuma 19% na adawa dashi.

Jin ra’ayin jama’ar na kwanaki shida, na zuwa ne a daidai lokacin da takun-saka ke kara ta’azzara tsakanin Washington da Caracas, kuma a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ke la’akari da karin wasu hanyoyin soji da suka hada da kai hare-hare kan kasar, a daidai lokacin da Amurka ke zargin shugaban Venezuela Nicolas Maduro na da hannu a safarar miyagun kwayoyi. Maduro ya yi watsi da zargin baki daya, tare da bayyana shi a matsayin batu na siyasa zalla.

Hare-haren na baya-bayan nan da sojojin Amurka suka kai a kusa da Venezuela, wanda aka kaddamar a ranar 2 ga Satumba, 2025, karkashin Operation Southern Spear, ya haifar da cece-kuce bayan da aka kashe mutane 87 ba bisa ka’ida ba. Inda masana kan harkokin shari’a na kasa da kasa da kuma kungioyin kare hakkin bil adama suka bukaci da a gudanar da bincike kan lamarin.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Kasashen Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5  December 10, 2025 Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa December 10, 2025 Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD December 10, 2025 Borkina Faso Ta Saki Sojojin Sama Na Najeriya 11 Da ta Kama Bayan Jirginsu Yayi Saukar Gaggawa. December 10, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Iran Tana Daukar Bakwancin Taron BRICS Na Binciken Kimiya Da Kuma Ci Gaban Ilmi December 10, 2025 Nasarar Da Iran Ta Samu A Yakin Kwanaki 12 Kan HKI Yana Jawo Hankalin Kasashen Duniya December 10, 2025 ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hare-Hare Kan Sojojin Pakistan Sun Kuma Kashe 6 Daga Cikinsu December 10, 2025 Najeriya: Majalisar Dattawa Ta Bawa Tunubu Damar Kai Sojoji Zuwa Kasar Benin December 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kotu Ta Umarci EFCC Ta Biya Wani Ƴan Kasuwar Kano Miliyan 5, Ta Nemi Afuwar Su
  • NLC Ta Shirya Zanga-Zangar Rashin Tsaro A Faɗin Ƙasa Ranar 17 Ga Disamba
  • Yadda APC Da ADC Ke Amfana Da Rikicin Jam’iyyar PDP
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Rawar Gani A Kafa Gidauniyar Fuskantar Matsalar Tsaro
  • Kremlin: Putin Ya Bayyana Wa Shugaba Maduro  Na Venezuela Goyon Bayansa
  • Zanga-zanga ta ɓarke bayan haɗarin tirela ta kashe mutum a Yobe
  • Ma’aikatar Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudinta a Gaban Majalisa
  • Sakamkon Jin Ra’ayi: Yawancin Amurkawa suna adawa da yunkurin kai hari kan Venezuela
  • Karamar Hukumar Agwara ta Jinjinawa Gwamnati Bisa Tabbatar da Tsaron Rayuka da Dukiyoyin Jama’a
  • Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa