Aminiya:
2025-12-13@11:01:22 GMT

Majalisar Dattawa za ta tantance sabbin hafsoshin tsaro ranar Laraba

Published: 28th, October 2025 GMT

Majalisar Dattawa za ta gudanar da zaman tantance manyan hafsoshin tsaron ƙasar a gobe Laraba waɗanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa kwanan nan.

Shugaba Tinubu ya aike da sunayen sabbin hafsoshin zuwa majalisar ne domin tantancewa da amincewa da su, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.

Rikicin adawa da cin zaben Shugaba Paul Biya ya bazu a Kamaru ’Yan bindiga sun sa harajin N15m kan al’ummar Mazabar Sanata Tambuwal

A wata wasiƙar fadar shugaban ƙasa da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta yayin zaman da aka gudanar a wannan Talatar, ya ce kwamitin da ke kula da harkokin tsaro zai zauna gobe domin tantance waɗanda aka naɗa.

A makon jiya ne Shugaba Tinubu ya aiwatar da sauye-sauye a bangaren tsaro, inda ya ɗaga likafar Laftanar Janar Oluyede Olupemi daga babban hafsan sojin ƙasa zuwa babban hafsan tsaron ƙasa, don maye gurbin Janar Christopher Musa da aka cire daga muƙaminsa.

Haka kuma, shugaban ƙasar ya naɗa sababbin hafsoshin sojin sama, ruwa da ƙasa, yayin da ya bar Manjo Janar E.A.P. Undiendeye a matsayinsa na babban hafsan sashen tattara bayanan sirri na sojin ƙasa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Majalisar Dattawa Manyan Hafsoshin Tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda

Kotun Kolin Najeriya ta soke afuwar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, inda ta ce shugaban ya wuce makadi da rawa ta hanyar yin afuwa ga wacce har yanzu kararta ke gaban kotu.

A hukuncin da aka yanke ranar Juma’a, kotun ta yanke hukunci da rinjayen alƙalai huɗu cikin biyar, inda ta tabbatar da hukuncin kisa da Babban Kotun Abuja ta yanke, kuma Kotun Daukaka Kara ta tabbatar.

‘Haduwata da masu garkuwa da ɗan uwana a dajin Zamfara’ Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin Gwamnan Bayelsa

An yanke wa Sanda hukunci ne a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, a lokacin rikicin cikin gida a gidansu da ke Abuja.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da ta shigar, tana mai cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin kisan kai ba tare da wata shakka ba.

A hukuncin jagoran alkalan, Mai Shari’a Moore Adumein ya ce Kotun Daukaka Kara ta yi daidai wajen tabbatar da hukuncin kotun farko.

Ya ce shiga tsakani na shugaban ƙasa bai dace ba a irin wannan yanayi.

Mai Shari’a Adumein ya ce: “Ba daidai ba ne ga bangaren zartarwa ya yi ƙoƙarin amfani da ikon afuwa kan laifin kisan kai, wanda har yanzu kararsa na gaban kotu.”

A watan Oktoba, an rage hukuncin Maryam zuwa shekaru 12 a kurkuku bayan Shugaba Tinubu ya amince da jerin sunayen wadanda ya yi wa afuwa.

Wannan mataki ya biyo bayan nazari da ya fara da sunaye 175, kafin daga baya a cire wasu saboda irin laifukan da suka aikata.

A lokacin, Mai Ba da Shawara na Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce rage hukuncin Sanda “ya dogara ne da tausayi saboda amfanin ’ya’yanta da kuma kyakkyawan halinta,” sannan ya ce ta nuna “nadama.”

Wannan mataki ya janyo suka a fadin Najeriya, ciki har da adawa daga dangin marigayi Bello.

Hukuncin na Kotun Kolin yanzu dai ya soke afuwar ta Shugaban Ƙasa.

Maryam Sanda ta shafe kusan shekaru shida a kurkuku, kuma hukuncin da aka rage zai bar ta da kusan shekaru shida nan gaba. Amma da hukuncin na ranar Juma’a, an dawo da hukuncin kisa da aka yanke mata tun farko.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zan yi amfani da Salah a wasan Liverpool da Brighton — Arn Slot
  • Majalisar Dinkin Duniya Za ta Yi Zama Da Bangarorin Da ke Yaki A Sudan
  • Tinubu Ya Yaba Wa Jami’an Tsaro Kan Ceto Dalibai 100 Da Aka Sace A Neja
  • Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda
  • NLC Ta Shirya Zanga-Zangar Rashin Tsaro A Faɗin Ƙasa Ranar 17 Ga Disamba
  • Yadda APC Da ADC Ke Amfana Da Rikicin Jam’iyyar PDP
  • ‘Yan Siyasa Ne Ke Zagon Ƙasa Ga Ci Gaban Nijeriya — Sarki Sanusi II
  • Kremlin: Putin Ya Bayyana Wa Shugaba Maduro  Na Venezuela Goyon Bayansa
  • Gwamnan Kano ya naɗa mace ta farko a matsayin shugabar Jami’ar Northwest
  • Shugaban Iran Ya Isa Astana Babban Birnin Kazakhstan