Da Ɗumi-Ɗumi: Osimhen Ya Amince Da Komawa Galatasaray Na Dindindin
Published: 8th, July 2025 GMT
Ɗan wasan gaban Napoli, Victor Osimhen, ya amince da komawa Galatasaray na dindindin, wani ɗan jarida a Nijeriya kuma makusancin Osimhen, Buchi Laba ne ya bayyana hakan.
Ya ce “Osimhen ya bayyana cewa yana son komawa Galatasaray daga Napoli, duk da cewar ƙungiyar ta ƙasar Italiya na fatan ci gaba da kasancewa da tsohon ɗan wasan na Lille, Bula ya rubuta a shafinsa na X.
Yayin da yake zaman aro a Galatasaray, Osimhen ya taimakawa ƙungiyar ta lashe gasar Super Lig ta Turkiyya, ɗan wasan na Super Eagles ya zura ƙwallaye 25 a wasanni 36 da ya buga, hakan yasa kungiyar ta lashe gasar karo na 25, kuma karo na farko tun shekarar 2019.
Ƙwallon da ya buga a wasan ƙarshe na gasar cin kofin Turkiyya ta sanya ya karya tarihin da Mario Jardel ya kafa a baya, wanda hakan ya sa ya zama ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a kakar wasa ɗaya a tarihin gasar ta ƙasar Turkiyya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Nijeriya Tunisiya a Galatasaray
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴan Arewa Za Su Yi Murna Idan Na Zama Shugaban Ƙasa — Peter Obi
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp