Aminiya:
2025-10-22@11:39:46 GMT

Labarin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya ƙarya ne – Sarkin Musulmi

Published: 22nd, October 2025 GMT

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya karyata zargin kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya, yana mai cewa wannan ikirari ƙarya ne kuma bai kamata a ci gaba da yada shi ba.

Sarkin ya bayyana hakan ne a taron Babban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Arewa na shekarar 2025, wanda aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, a ranar Talata, da taken: “Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Al’umma Domin Samun Zaman Lafiya da Tsaro Mai Dorewa a Arewa.

Masu kwacen waya sun kashe ma’aikaciyar lafiya a Zariya Majalisa ta soma binciken yadda aka kashe $4.6bn na tallafin kiwon lafiya

Ya ce: “Sun dade suna cewa ana kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya daga ƙasashen Yamma kamar Amurka, Kanada da sauransu. A ina? Yaushe? Wannan labari ne na ƙarya.”

Sarkin, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Arewacin Najeriya ya ce ba zai yiwu a ce ana irin wannan kisa a wani yanki na Najeriya ba, kuma sarakunan gargajiya ba su sani ba.

Ya roƙi shugabannin ƙasa da su sanya dokoki kan amfani da kafafen sada zumunta saboda illar da suke haifarwa da kuma abubuwan batanci da ake wallafawa game da ƙasa da mutane a cikinsu.

Sarkin ya kuma buƙaci ‘yan Najeriya da su daina zagin sojoji, yana mai jaddada cewa da babu sadaukarwarsu, da ƙasa ba za ta ci gaba da kasancewa ƙasa ɗaya mai zaman lafiya ba.

Sai dai ya amince cewa sojoji na fama da ƙalubale da gazawa, amma ya soki maganganun da ake yi a kafafen sada zumunta da ke zargin jami’an tsaro da haɗin gwiwa da ‘yan ta’adda, yana mai cewa hakan rashin tausayi ne kuma bai dace ba.

Sarkin ya sake jaddada goyon bayan sarakunan gargajiya ga ci gaban dimokuraɗiyya da biyayya ga dukkan shugabannin da aka zaɓa, ciki har da Shugaban Ƙasa, Majalisun Tarayya da na Jihohi, da Gwamnoni.

Ya kuma buƙaci sarakunan da suka halarci taron da su haɗa kai domin fuskantar ƙalubalen da ƙasa ke ciki, yana mai cewa za a mika shawarwarin da suka bayar ga Gwamnonin Arewa domin ɗaukar matakin da ya dace.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a taron ya ce sarakunan gargajiya na da muhimmiyar rawa wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya ce suna da ƙwarewa wajen rage tashin hankali, warware rikice-rikice, da kawo zaman lafiya a lokacin ƙalubale.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kisan Kiyasahi Sarkin Musulmi

এছাড়াও পড়ুন:

NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 

NLC ta kuma buƙaci gwamnati ta bi shawarar UNESCO wacce ta ke cewa ya kamata a ware aƙalla kashi 25 cikin 100 na kasafin kuɗi na kowace shekara ga ilimi.

Ajaero, ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin cikin makonni huɗu, NLC za ta haɗa dukkanin ma’aikata na ƙasa don gudanar da yajin aiki na ƙasa baki ɗaya.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu October 21, 2025 Manyan Labarai Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara October 20, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a October 20, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal
  • Sayyed al-Houthi: Mun shirya dawowa fagen daga idan Isra’ila ta ci gaba da kisan kiyashi a Gaza
  • Majalisa ta soma binciken yadda aka kashe $4.6bn na tallafin kiwon lafiya
  • Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya
  • NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 
  • Muna Samun Gagarumin Cigaba Wajen Dawo Da Zaman Lafiya A Zamfara-Gwamna Lawal
  • Juyin mulki: Ana zargin tsohon gwamnan da ɗaukar nauyin sojojin Najeriya
  • NAJERIYA A YAU: Shin Ya Kamata A Saki Shugaban IPOB Nnamdi Kanu?
  • Talauci ne babban maƙiyin ɗan Adam — Atiku