Sun ce wadanda suka mutu yawancinsu wadanda suka je kwaso man fetur ne a lokacin da tankar ta yi hatsari kafin fashewar.

 

Shugabannin Direbobin Tankar Mai na Jihar Neja (PTD) da Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas ta Nijeriya (NUPENG) ta kasa, Kwamared Farouk Mohammed Kawo, sun tabbatar wa LEADERSHIP faruwar lamarin.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba October 21, 2025 Manyan Labarai NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi  October 21, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu October 21, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, tare da haɗin gwiwar maharba, sun samu nasarar tarwatsa gungun masu garkuwa da mutane, tare da kama mutum bakwai da ake zargi da aikata laifuka a Jihohin Gombe, Bauchi, Yobe da Adamawa.

Rundunar ta samu nasarar ne bayan kama Abdullahi Ibrahim, mai shekaru 40 daga ƙauyen Tilde a Funakaye, a ranar 23 ga watan Nuwamba 2025.

An harbe manomi saboda rikici kan filin kiwo a Borno DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan Kwara

An kama shi ne bayan samun bayanan sirri kan hulɗa da masu satar shanu.

Abdullahi, ya amsa cewa yana da hannu a garkuwa da mutane tare da bayyana sunayen waɗanda suke aikata laifin tare.

A cewar kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, jami’an Operation Hattara tare da maharba ne suka kai samame maɓoyarsu a ranar 28 ga watan Nuwamba 2025, inda suka kama mutum shida bayan yin artabu.

Waɗanda aka kama sun haɗa da; Usman Mohammed, Hussain Idris, Adamu Tukur,  Ya’u Abdullahi, Ali Umar, Hassan Usman da Abdullahi Ibrahim.

Rundunar ta ce waɗanda ake zargin sun amsa cewa suna da hannu a garkuwa da mutane tare karɓar kuɗin fansa kusan Naira miliyan 150.

Jami’an sun shiga dajin Gadam, inda suka samu bindiga ƙirar GPMG mai jigida guda ɗaya da harsasai takwas bayan wata musayar wuta da suka yi wasu ’yan ta’adda da suka tsere.

Haka kuma an gano suna da hannu wajen garkuwa da wani mutum a ƙauyen Barderi a Akko, a ranar 15 ga watan Janairun 2025.

Sun tsare mutumin na tsawon makonni biyu kafin karɓar Naira miliyan 15 a matsayin kuɗin fansa.

DSP Buhari, ya ce ana cigaba da bincike, kuma za a gurfanar da su a kotu.

Ya roƙi jama’a da su ci gaba da bai wa rundunar sahihan bayanai domin inganta harkokin tsaro.

Rundunar ‘Yan Sandan Gombe ta ce za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike
  • Gwamnatin Gombe da UNICEF sun tallafa wa yara masu fama ƙarancin abinci mai gina jiki
  • Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe
  • Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na tiriliyan 12.8 cikin watanni 15
  •  An Kira Yi Gwamnatin Canada Da Ta Kama Olmert Da Livini Na “Isra’ila
  • MDD ta bukaci a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma janyewa daga Tuddan Golan na Siriya
  • NAJERIYA A YAU: Abun Da Masu Ruwa Da Tsaki Ke Yi Na Dakile Laifuka A Wurin Matasa
  • ’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a Yobe
  • MDD Ta Amince Da Kudurori Biyu Masu Yin Tir Da HKI
  • Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sabon Shugaban Hukumar Kidaya, Kwamishinoni da Manyan Sakatarori