Amurka ta tsare wani dan jarida musulmi saboda sukar Isra’ila
Published: 27th, October 2025 GMT
Wata hukumar shige da fice da kwastam ta Amurka (ICE) ta tsare wani dan jarida mai sharhi kan harkokin siyasa, Sami Hamdi, a filin jirgin sama na San Francisco saboda sukar da ya yi wa Isra’ila a yayin wani rangadin jawabai da ya yi a Amurka.
A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar CAIR ta ce an tsare Hamdi ne a filin jirgi sama na San Francisco.
A ranar Lahadi CAIR ta yi kira da sake shi kuma ta zargi Trump da tsare shi saboda sukar da yake yi wa Isra’ila.
Masu goyon baya da masu fafutukar kare hakkin jama’a sun ce tsare Hamdi wani lamari ne na ramuwar gayya ta siyasa ga masu sukar Isra’ila, wadanda ake hukunta su a kan iyaka kafin ma su sami damar yin magana.
Tun lokacin da Isra’ila ta fara kai hari kan Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, akalla Falasdinawa 68,000 ne suka mutu yayin da wasu 170,000 suka jikkata, yawancinsu mata da yara.
Kwararru sun yi gargadin cewa adadin wadanda suka mutu na iya kaiwa daruruwan dubbai da zarar an gano wadanda suka bata ko kuma aka binne a karkashin baraguzan ginin.
A baya bayan nan dai Trump ya tsaurara matakan shige da fice, ciki har da shirye-shiryen na kafofin sada zumunta, akan masu nuna goyan Falasdinawa da kuma dawa da hare-haren Isra’ila kan Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kashi 84% na ‘yan Faransa ba su gamsu da Macron ba a matsayin Shugaba October 27, 2025 Iran ta bukaci MDD ta nisanci nuna bangaranci game da masu keta dokokin duniya October 27, 2025 Kamaru : Paul Biya, ya lashe zaben shugaban kasa a karo na takwas October 27, 2025 An Nada Birgediya Janar Qarshi A Matsayin Mataimakin Babban Kwamandan Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci October 27, 2025 Hamas Ta Ce: Kungiyar Ta Ba Da ‘Yanci Ga Masu Shiga Tsakani Zabar Membobin Kwamitin Gudanar Da Gaza October 27, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe ‘Yan kasar Lebanon Biyu Tare Da Jikkatan Wasu Biyu Na Daban October 27, 2025 Amnesty International Ta Bukaci Bayyana Makomar Masu Fafutukar Kare Hakkin Bil’Adama Da Suka Bace A Uganda October 27, 2025 Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sun Yi Da’awar Kwace Karin Wasu Garuruwa A Sudan October 27, 2025 Qalibaf: Sakon Iran, Rasha da China ga MDD manuniya ce ta hadin gwiwa mai karfi October 27, 2025 Sheikh Naim: Hezbollah a shirye take ta fuskanci Isra’ila idan yaki ya barke October 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Talauci Yana Karuwa A “Isra’ila” Bayan 7 Ga Watan Oktoba
A wani rahoton da jaridar Jerissalam Post” ta buga ta ambaci cewa; Tun bayan farmakin 7 ga watan Oktoba 2023, ana kara samun matalauta da talauci.
Rahoton ya yi nuni da cewa karuwar talaucin yana da alaka ne da yadda farmakin 7 ga watan Oktoba ya yi tasiri a cikin tattalin arziki “Isra’ila”.
Haka nan kuma rahoton ya ce, da akwai dubban iyalai yahudawa wadanda gabanin yaki, suke rayuwa cikin yanayi mai kyau ta fuskar tattalin arziki, yanzu sun zama matalauta. A dalilin haka cibiyar da ta shirya rahoton ta “ Latit” tana yin gargadi akan cewa; za a iya samun ci gaba da yaduwar talaucin, domin iyalai da dama suna gogoriyon yadda za su iya biyan bukatar yau da kullum, duk da cewa suna da cikakken aiki.
Ita dai kungiyar “Latit” ta ‘yan sahayoniya ce wacce aka kafa a 1996 domin fada da talauci da kuma rashin abinci.
Haka nan kuma rahoton ya bayyana cewa; Adadin iyalan da suke fama da talauci a cikin ‘yan sahayoniyar sun kai 867,000, saboda ba su da lamunin abinci. Adadin daidaikun wadannan iyalan sun kai miliyan 2.8, daga cikinsu da akwai kananan yara miliyan 1.18.
Haka nan kuma wani sashen na rahoton ya ce, talaucin yana karuwa ne da kaso 27-29%.
Da dama daga cikin iyalan ‘yan sahayoniyar suna rayuwa ne ta hanyar samun taimako da tallafi na abinci,domin suna amfani da kudaden da suke samu na aikin yi, domin biyan kudaden wuta da sayen magunguna.
Kaso 40% na tsofaffi suna fama da matsalar tabarbarewar rashin lafiya, da ya faro tun daga farkon yaki.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka AU Ta yi Tir Da Harin RSF A Makarantar Kananan Yara Da Ya Kashe Mutane 80 December 8, 2025 MِِِِDD: Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya December 8, 2025 Iran Da Azarbaijan Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna Domin Warware Matsaloli December 8, 2025 Iran Da Kasashen Afrika Sun Daura Dammarar Karfafa Alakar Kimiyya Tsakaninsu December 8, 2025 Ecowas Ta Tura Sojoji Zuwa Jamhuriyar Benin Don Dakile Juyin Mulki December 8, 2025 IRGC: Makaman Iran Sun Fada Kan Matatan Man Haifa Har Sau Biyu A Yakin Kwanaki 12 December 8, 2025 Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Sanarwan Kubutar Da Yan Makaranta 100 Da Aka Sace December 8, 2025 Iraki Ta Musanta Cewa Ta Tushe Asusun Hizbullah Da Ansarallah December 8, 2025 Sabon Fada Ya Barke A Tsakanin Thailand Da Cambodia December 8, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da Kisan Fararen Hula A Kasar Sudan December 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci