Netanyahu ya ba da umarnin kai mummunan farmaki a Gaza
Published: 28th, October 2025 GMT
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya umarci rundunar sojin ƙasar da ta kai mummunan farmaki a Zirin Gaza, bayan ya zargi ƙungiyar Hamas da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
Wata sanarwa da ofishin firaministan ya fitar, ta ce: “Bayan tattaunawar tsaro, Firaminista Netanyahu ya umurci rundunar soji da ta gaggauta kai hare-hare masu ƙarfi a Zirin Gaza.
Sanarwar na zuwa ne bayan Isra’ila ta zargi Hamas ta karya sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma kwanakin baya domin ba da damar kai agaji ga fararen hula da ke yankin.
Tun da farko dai Netanyahu ya sha alwashin mayar da martani kan abin da ya kira saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta, inda ya ce Hamas ta gaza tabbatar da sharuɗɗan yarjejeniyar da suka haɗa da miƙa dukkan mutanen da ta yi garkuwa da su waɗanda suka haɗa rayayyu da matattu.
Duk da gwamnatin Isra’ila ta tabbatar da cewa ƙungiyar Hamas ta miƙa waɗanda suka raye, amma har yanzu ba ta ƙarasa miƙa gawarwakin matattun ba, abin da ya janyo zargin cewa tana ƙoƙarin saɓa yarjejeniyar.
A nata ɓangaren kuwa, Hamas ta bayyana cewa nemo gawarwakin na da wahalar gaske ne, saboda baraguzan gine-ginen da Isra’ila ta rusa da ke kawo cikas wajen lalubo gawarwakin.
A bayan nan ne Isra’ila ta tabbatar da cewa gawar mutumin da Hamas ta miƙa mata a ranar Litinin ba ta cikin gawarwakin da ƙungiyar ta yi garkuwa da su da aka tsara za ta mayar da su.
Har yanzu dai ana neman gawarwaki 13 daga cikin waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su, waɗanda ake tunanin za ta miƙa domin cika sharuɗan yarjejeniyar tsagaita wuta da Shugaba Trump ya tsara domin kawo ƙarshen yaƙin Gaza.
Hukumomin Isra’ila sun ɗauki hakan a matsayin yunƙurin Hamas na karya alƙawarin da aka shiga domin kawo ƙarshen yaƙin.
Mun jinkirta miƙa gawa a yau Talata —HamasƘungiyar Hamas ta sanar da cewa ta jinkirta miƙa gawar wani wanda aka tsara za ta miƙa da yammacin Talatar nan, saboda abin da ta kira saƙonin karya yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ta yi.
A sanarwar da sashen yaƙin ƙungiyar, Ezzedine Al-Qassam Brigades, suka fitar, ƙungiyar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon abin da ta bayyana a matsayin “saɓa yarjejeniyar tsagaita tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani wajen tsara ta.”
“Za mu jinkirta miƙa gawar da aka tsara a yau [Talata] saboda take haƙƙin da Isra’ila ta yi.
Duk wani sabon farmaki daga Isra’ila zai iya kawo cikas wajen aikin bincike, tono, da ceto gawarwakin,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta fito ne ‘yan mintuna kaɗan bayan Firaminista Netanyahu ya umurci sojojinsa da su kai mummunan farmaki a Zirin Gaza, yana zargin Hamas da karya sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Benjamin Netanyahu Falasɗinawa yarjejeniyar tsagaita wuta da Netanyahu ya Isra ila ta
এছাড়াও পড়ুন:
Turkiya A Shirye Take Ta Aike Da Sojoji Zuwa Yankin Gaza
Ministan harkokin wajen Turkiya Hakan Faidan ne ya bayyana cewa; kasarsa za ta iya daukar nauyin wararen matsalar Falasdinu, kuma a shirye take ta aike da sojoji zuwa yankin na Gaza idan bukatar hakan ta taso.
Fidan ya fada wa kamfafen watsa labaru cewa; Tukriya a shirye take ta yi duk abinda za ta iya yi, ta kuma dauki nauyin da ya dace akan batun Falasdinu.
A can Amurka kuwa, manzon musamman na Amurka akan harkokin yammacin Asiya, Barrack ya fada wa jaridar “Jerrusalem Post” cewa: Kasar Turkiya tana da sojoji masu karfi, kuma tana hulda da Hamas, a dalilin hakan shigarta cikin rundunar da za a aike Gaza, zai yi amfani.”
A ranar 18 ga watan Nuwamba ne dai kwamitin tsaro na MDd ya amince da rinjaye akan wani kuduri da Amurka ta gabatar domin kawo karshen yakin Gaza. A karkashin wannan kudurin zai a kuma aike da sojojin kasa da kasa daga nan zuwa karshen 2027.
Kudurin ya kuma tanadi cewa za a kafa gwamnati a yankin na Gaza ta kwararru wacce kwamijin tsaro ne zai rika kula da tafiyar da ita.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kremlin: Putin Ya Bayyana Wa Shugaba Maduro Na Venezuela Goyon Bayansa December 12, 2025 Ben Gafir Ya Yi Sha Alwashin Rushe Kabarin Sheikh Izzuddin Alkassam December 12, 2025 Maduro: Amurka Ta Bude Sabon Salon Fashi AkanDoron Ruwa December 12, 2025 Ayatollah Khamenei : Iran na samun ci gaba duk da kalubale da dama December 11, 2025 Kyaftin Traoré : Yau Burkina ta zama misali a duniya December 11, 2025 Iran da Kazakhstan Sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama December 11, 2025 Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta December 11, 2025 Kasashen ECOWAS sun rage kudin sufirin jiragan sama a tsakaninsu December 11, 2025 Dakarun IRGC 3 Sun Yi Shahada A wani Harin Ta’addanci A Kudancin Kasar Iran December 11, 2025 Hamas: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Bangaren Farko Na Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza December 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci