Rasha ta gargadi Faransa game da tura sojoji Ukraine
Published: 28th, October 2025 GMT
Kasar Rasha ta gargadi Faransa game da tura sojoji zuwa Ukraine don taimakawa Kyiv.
Hukumar leken asiri ta Rasha (SVR) ta bankado cewa Faransa ta shirya aika Sojoji 2,000 zuwa Ukraine.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta kira wannan yiwuwar “abin da ba za a yarda da shi ba,” tana mai gargadin hadarin dake tattare da shi.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta shawarci Paris da ta yi amfani da wadannan sojojin don kare gidajen tarihi na Faransa maimakon tura su a Ukraine.
Dama a baya ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta bayyana cewa duk wani yanayi da ya shafi tura sojojin NATO a Ukraine ba abin yarda ba ne ga Rasha kuma yana iya fuskantar barazanar karuwar ta’addanci.
Ma’aikatar ta bayyana kalaman da kasashen Turai suka yi game da yiwuwar tura rundunar NATO zuwa Ukraine a matsayin abin da ke tunzura ci gaba da yaki.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Pezeshkian: Hadin Kai A Tsakanin Kasashen Gabas Ta Tsakiya Ba Zabi Ba Ne, Amma Dole Ne October 28, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Waje Kan Harkokin Siyasa Na Iran Ya Ce: Iran Ba Ta Kula Da Matsin Lamba October 28, 2025 Baqa’i: Dokar Majalisar Shawarar Musulunci Ce Ke Jagorantar Hadin Kan Iran Da Hukumar IAEA October 28, 2025 Sojojin Isra’ila Sun Kai Hare-Hare Kan Yankin Gaza A Matsayin Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta October 28, 2025 Al-Burhan: Sojojin Sudan Sun Janye Daga El-Fasher Saboda Kare Rayukan Fararen Hula October 28, 2025 Baqaei: Iran ta daɗe tana aiki don haɓaka zaman lafiya a duniya October 28, 2025 An Yi Girgizar Kasa Mai Karfi A Kasar Turkiya October 28, 2025 Ouattara Na Kasar Ivory Coast Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa October 28, 2025 MDD Ta Yi Kira Da Abude Kafar Shigar Da Kayan Agaji Zuwa Garin El-Fashar October 28, 2025 Wilayati: Kasashen Ian, China Da Rasha Suna Taka Rawa A Fagen Kafa Sabon Tsarin Duniya October 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
ECOWAS ta bukaci waware batutuwa na siyasa ta hanyoyin lumana a yammacin Afirka
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta nuna damuwa kan rudanin siyasa a yankin, kamar yadda kafafen yada labaran Najeriya suka ruwaito.
Shugaban Hukumar ECOWAS Omar Touray ya shaida wa taron ministoci a Abuja babban birnin Najeriya cewa, “Abubuwan da suka faru a ‘yan makonnin da suka gabata sun nuna bukatar yin tunani sosai kan makomar dimokuradiyyar yankin da kuma bukatar saka hannun jari cikin gaggawa a harkokin kasuwanci da tsaro.”
Sanarwar ta zo ne bayan wani yunkurin juyin mulki a kasar Benin a karshen makon da ya gabata, wanda ya biyo bayan nasarar juyin mulkin da aka yi a Guinea-Bissau.
Touray ya ce akwai manyan hadura da dama da suka hada da rashin bin ka’idojin mika mulki a Guinea, da gurgujewar Shirin zabe, da kuma kalubale ga diflomasiyya da hadin kan kasashe mambobin kungiyar ECOWAS.
Toray ya kuma yi kira da a kara yawan tarurruka tare da yin kira ga kungiyar da ta hada kai don tunkarar barazanar ta’addanci wadanda ke a matsayin babban kalubale ga duniya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Reuters: Amurka na matsa lamba kan kotun ICC don janye bincike kan yakin Gaza da Afghanistan December 11, 2025 Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila December 11, 2025 Sakamkon Jin Ra’ayi: Yawancin Amurkawa na adawa da kai hari kan Venezuela December 11, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Kasashen Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5 December 10, 2025 Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa December 10, 2025 Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD December 10, 2025 Borkina Faso Ta Saki Sojojin Sama Na Najeriya 11 Da ta Kama Bayan Jirginsu Yayi Saukar Gaggawa. December 10, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Iran Tana Daukar Bakwancin Taron BRICS Na Binciken Kimiya Da Kuma Ci Gaban Ilmi December 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci