Ya ce, an ɗauki wannan matakin ne don bai wa masu zaɓe a faɗin jihar damar gudanar da zaɓen da ke tafe a jihar.

 

Ya ƙara da bayyana cewa, Gwamna Bago ya umarci dukkan hukumomin tsaro a Jihar da su tabbatar an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da tsari, yana mai sake tabbatar da alƙawarin gwamnatin Jihar na tabbatar da tsarin zaɓe mai aminci da kwanciyar hankali.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba October 28, 2025 Ra'ayi Riga Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani October 28, 2025 Labarai Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100 October 28, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Mangal ya bayar da tallafin N257m don yi wa marasa galihu aikin ido kyauta a Katsina

Fitaccen attajirin nan Alhaji Dahiru Mangal, ya ɗauki nauyin yi wa marasa galihu a Jihar Katsina aikin ido kyauta, inda ɗaruruwan mutane ke samun kulawar likitoci ba tare da biyan ko sisi ba.

A yayin da wakilin Aminiya, ya ziyarci Asibitin Ido da ke birnin Katsina, marasa lafiya da dama da suka ci gajiyar aikin sun bayyana farin cikinsu da godiya kan tallafin na sama da Naira miliyan 257.

Matatar man Dangote ta rage farashin fetur zuwa N699 Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda

Malama Indo, wadda ta fito daga garin Dankama da ke Ƙaramar Hukumar Kaita, ta bayyana farin cikinta da samun tallafin.

Ta ce: “Na kwashe kusan shekara guda ina fama da ciwon ido. Da zarar yamma ta fara yi, sai na kasa fitowa saboda duhu. Amma yanzu ina gani lafiya lau, babu wata matsala.

“Mun kwana uku a nan asibiti, ba mu rasa komai ba, har abinci ake ba mu. Wallahi ba zan iya cewa na kashe komai ba sai kuɗin mota kawai.

“Muna roƙon Allah Ya saka wa wanda ya ɗauki nauyin wannan aiki da alheri,” in ji ta.

Shi ma wani dattijo mai suna Malam Khalha Jibiya, ya bayyana jin daɗinsa game da aikin.

Ya ce an masa aiki, an kuma ba shi tabarau, sannan yanzu yana gani ba tare da wata matsala ba.

“Idan waɗanda Allah Ya hore musu dukiya za su riƙa taimaka wa gajiyayyu kamar haka, da matsalolinmu da dama sun ragu.

“Muna addu’a Allah Ya saka wa mai ɗaukar nauyin wannan shiri da alheri.” inji Malam Khalha.

Dukkanin marasa lafiyan da Aminiya ta zanta da su, sun yi godiya, musamman ganin cewa aikin ido da magungunan da ake ba su kyauta ne baki ɗaya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince da Sama da Naira Biliyan 2.6 Domin Aikin Hajjin 2026
  • Gwamnatin Kano ta haramta kafa hukumar Hisbah mai zaman kanta
  • Zaɓen 2027 ya hana ni korar wasu ma’aikata – Bago
  • Mangal ya bayar da tallafin N257m don yi wa marasa galihu aikin ido kyauta a Katsina
  • Duniyarmu A Yau: Iran Da Amurka A Yakin Kwanaki 12 Wa Ya Sami Nasara
  • Yadda APC Da ADC Ke Amfana Da Rikicin Jam’iyyar PDP
  • Hukumomin Ilimi a Jihar Jigawa Sun Kare Kasafin Kudinsu a Gaban Majalisa
  • Gwamnatin Jigawa Ta Kara Samar da Shirye-shiryen Inganta Rayuwar Masu Buƙata ta Musamman
  • Katsina Ta Amince Da Bayar Da Alawus Na Naira 30,000 Duk Wata Ga Malaman Karkara
  • Karamar Hukumar Agwara ta Jinjinawa Gwamnati Bisa Tabbatar da Tsaron Rayuka da Dukiyoyin Jama’a