An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba
Published: 21st, October 2025 GMT
DSS ta gurfanar da su bisa tuhumar laifuka 32 da suka shafi ta’addanci.
Usman ya amsa laifi ɗaya kacal na haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, amma ya musanta sauran.
Abba kuwa ya ƙi amsa dukkanin laifukan da ake tuhumar sa da su.
An zarge su da kai hari sansanin soja na Wawa da ke Jihar Neja, sace mutane, samar da kuɗin ta’addanci, da kuma samun horo a ƙasar Mali daga wata ƙungiyar ta’addanci ta waje.
Haka kuma DSS ta ce sun sace jami’in Kwastam da wani jami’in Shige da Fice wanda ya mutu a hannunsu, tare da karɓar kuɗin fansa na miliyoyin Naira daga iyalan waɗanda suka sace kafin a kama su.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Wasu jiga-jigan ADC za su dawo jam’iyyarmu — Shugaban APC
Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC, za su koma APC a mako mai zuwa.
A makonnin da suka gabata, ’yan siyasa da dama daga jam’iyyun adawa suna sauya sheƙa zuwa APC, yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
HOTUNA: Al’ummar Jihar Neja sun yi addu’o’in neman zaman lafiya Ta’addanci: An fi kashe Musulmi a kan Kiristoci a Najeriya — Jakadan AmurkaIdan ba a manta ba, Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya koma APC, sannan Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, shi ma ana sa ran zai sanar da sauya sheƙarsa a hukumance nan ba da jimawa ba.
Yilwatda, yayin ganawarsa da mambobin APC a Jos, Jihar Filato, ya ce: “A mako mai zuwa zan karɓi wasu fitattun mutane daga ADC. Wasu daga cikinsu sun bar PDP sun koma ADC, amma yanzu za su dawo APC.”
Ya ƙara da cewa, yawancin waɗanda za su koma jam’iyyar “sun riga sun kammala gwajin lafiyarsu” kuma za a tarbe su a hukumance a mako mai zuwa.
“A cikin makonni biyu masu zuwa, za mu kuma bayyana wani babban ɗan siyasa da ya kammala gwajin lafiyarsa. Za mu karɓe shi a hukumance nan gaba kaɗan,” in ji shi.
Shugaban jam’iyyar ya bayyana APC a matsayin “amaryar siyasa ta yanzu”, inda ya ce ’yan siyasa da yawa na rubibin shiga jam’iyyar.
Ya ce akwai sanatoci, gwamnoni, da ’yan majalisa da dama da ke shirin komawa APC.
“APC jam’iyya ce mai maraba da kowa,” in ji shi.
“Ba sai ka kasance daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar ba kafin ka samu ci gaba a cikinta. Ni shaida ne a kan hakan. Da zarar ka shiga, kana da cikakken haƙƙi da damar da kowa yake da ita. Wannan shi ne tsarin jam’iyyarmu.”