2025-10-29@02:34:14 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2094
«yarjejeniyar tsagaita wuta da»:
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya umarci rundunar sojin ƙasar da ta kai mummunan farmaki a Zirin Gaza, bayan ya zargi ƙungiyar Hamas da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma. Wata sanarwa da ofishin firaministan ya fitar, ta ce: “Bayan tattaunawar tsaro, Firaminista Netanyahu ya umurci rundunar soji da ta gaggauta kai hare-hare masu ƙarfi a Zirin Gaza.” Juventus ta kori kocinta Igor Tudor An raba wa iyalan ’yan sandan da suka mutu tallafin N31m a Jigawa Sanarwar na zuwa ne bayan Isra’ila ta zargi Hamas ta karya sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma kwanakin baya domin ba da damar kai agaji ga fararen hula da ke yankin. Tun da farko dai Netanyahu ya sha alwashin mayar da martani...
Ya ce, an ɗauki wannan matakin ne don bai wa masu zaɓe a faɗin jihar damar gudanar da zaɓen da ke tafe a jihar. Ya ƙara da bayyana cewa, Gwamna Bago ya umarci dukkan hukumomin tsaro a Jihar da su tabbatar an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da tsari, yana mai sake tabbatar da alƙawarin gwamnatin Jihar na tabbatar da tsarin zaɓe mai aminci da kwanciyar hankali. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba October 28, 2025 Ra'ayi Riga Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani October 28, 2025 Labarai Tsohon Kwamishina...
An bude taron ministocin cikin gida na kasashen kungiyar hadin kan tattalin arziki ta ECO a birnin Tehran. Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Massoud Pezeshkian ne ya jagoranci bude taron wanda shi ne karo na hudu. Ministoci da manyan jami’ai daga Pakistan, Tajikistan, Turkmenistan, Jamhuriyar Azerbaijan, Afghanistan, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Turkiyya, Uzbekistan, da Jamhuriyar Musulunci ta Iran na halartar taron, tare da Sakatare Janar na ECO, Ministan Cikin Gida na Oman, da Mataimakin Ministan Cikin Gida na Iraki a matsayin baki. Mahalarta taron na tattauna batutuwan tsaro, sa ido kan iyakoki, tattalin arziki, da alaka tsakanin birane. Ya yi kira ga kasashen Tsakiyar Asiya, na Caucasus, Kudancin Asiya, Yammacin Asiya da Tekun Farisa, gami da kasashe membobin OCE, da su “yi...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa duk da jajircewar kungiyar na mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da ita, firaministan gwamnatin Isra’ila yana kokarin karya sharuddanta. Hazem Qassem, kakakin kungiyar, ya ce “Mun yi wa masu shiga tsakani bayani kan cikas din da ke hana neman gawarwakin fursunonin Isra’ila kuma mun nemi su samar mana da karin kayan aiki.” Mai magana da yawun Hamas ya kuma bayyana cewa: “Mun sanar da Alkahira game da ayyukan bincike na ‘yan Isra’ila, kuma muna ci gaba da sanar da masu shiga tsakani game da ci gaban binciken. Duk da tsagaita wuta da aka yi tsakanin gwamnatin Tel Aviv da kungiyar Hamas, sojojin Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare. Na...
Idan muka kwatanta da kasar Sin, sabanin yawan albarkatun da Afrika ke da su kamar na kasar noma, ita Sin kasa da kaso 9 kadai take da shi, amma kuma tana bayar da gagagrumar gudunmawa a duniya, inda take tsaye da kafarta wajen ciyar da al’ummarta, har ma ta bayar da gudunmawa ga kasashe mabukata. To mene ne dalilin nasarar Sin a wannan bangare? Gaggarumar nasarar da Sin ta samu a bangaren aikin gona, ba wani abu ba ne illa jajircewar gwamnatin kasar da dabaru da fasahohin aikin gona da kullum ake lalubowa. Misali, ko a cikin hamada, kasar Sin ta lalubo dabarun da suka dace, inda ake noman tsirrai masu juriya dake iya ciyar da mutane da...
Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani
Bugu da kari, an shata wasu manyan manufofi game da shirin shekaru biyar-biyar na 15 da suka hada da gagarumar zurfafawa wajen samun ci gaba mai inganci, da ingantacciyar habaka dogaro da kai da karfin ci gaban kimiyya da fasaha, da cimma sabbin nasarori a cikin kara zurfafa gyare-gyare a gida gaba daya, da samun ci gaban al’adu da dabi’a a cikin al’umma a zahirance, da kara inganta jin dadin rayuwa, da samun manyan sabbin ci gaba wajen zurfafa shirin samar da kyakkyawar kasar Sin, da kuma kara samun ci gaba wajen karfafa garkuwar tsaron kasa. A cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 (2021-2025), an kiyasta cewa, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin zai zarce yuan...
Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hare-haren bama-bamai da dama a gabashin Zirin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila sun yi rusa bama-bamai kan gidaje da dama a gabashin Zirin Gaza da safiyar yau Talata, tare da harba manyan bindigogi a yankuna daban-daban, a matsayin ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta. Cibiyar Bayanai ta Falasdinawa ta ruwaito cewa: Tun daga wayewar gari a yau Talata, sojojin mamayar Isra’ila sun rusa gidaje da gine-gine akalla guda huɗu a gabashin birnin Gaza, Al-Bureij, da Khan Younis, inda aka ji ƙarar fashewar abubuwa masu karfi . Cibiyar ta ƙara da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun buɗe wuta, ba tare da wani dalili ba a yankuna da dama na gabas da arewacin Zirin Gaza. Share 0...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka? October 27, 2025 Labarai Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote October 27, 2025 Labarai An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga October 27, 2025
Shugaban ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya bayyana cewa: Sun bai wa masu shiga tsakani cikakken ‘yanci na zaɓar membobin Kwamitin Gudanar da Gaza Khalil al-Hayya, shugaban ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya ce: ƙungiyar ta Hamas ta bai wa masu shiga tsakani ‘yancin zaɓar membobin kwamitin da za su gudanar da mulkin Gaza, wanda zai sami cikakken iko a yankin. A wata hira da aka watsa a gidan talabijin na Al- Jazeera a yammacin Lahadi, al-Hayya ya jaddada cewa; Akwai batutuwan ƙasa waɗanda ba wai Hamas kaɗai ke da alhakinsu ba, amma alhakin dukkan ƙungiyoyin ƙasa ne. Ya bayyana cewa ƙungiyar ta gudanar da tarurruka da dama da ƙungiyoyi, ciki har da Fatah. Ya ƙara da cewa abin da...
Tsohon gwamnan, wanda ya dade yana cikin jam’iyyar PDP kuma fitaccen mai fada a ji a cikin jam’iyyar, yana neman jagorantar jam’iyyar yayin da take shirin yin babban taronta na kasa. Ana sa ran jam’iyyar PDP, wacce ta mulki Nijeriya daga 1999 zuwa 2015, za ta zabi sabon Shugabanta na kasa da sauran shugabannin jam’iyyar a lokacin babban taron jam’iyyar da za a yi a Ibadan a jihar Oyo a watan gobe. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno October 27, 2025 Labarai Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe October 27, 2025 Manyan Labarai Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga...
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Kebbe/Tambuwal, Abdussamad Dasuki, ya ce ba zai tsaya takara a zaɓen 2027 ba. Dasuki, ya ce ya ɗauki wannan mataki ne domin bai wa matasan Najeriya damar shiga harkokin mulki. El-Clasico: Real Madrid ta doke Barcelona da ci 2 Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a Najeriya Ya bayyana cewa tun daga shekarar 2011 yake majalisar dokoki, kuma yana ganin zai fi dacewa idan aka bai wa matasa dama a dimokuraɗiyya. “Najeriyar da muke mafarki za ta tabbata ne kawai idan mun yi sadaukarwa,” in ji shi. Ya ƙara da cewa bayan tuntuɓar iyalansa da jagororinsa, ya yanke shawarar bai zai sake tsayawa takara ba don ya gaji ba, sai don bai...
Wata tanka ɗauke da man fetur ta kife a kan hanyar Lambata zuwa Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja, lamarin da ya haifar da tsoro da fargaba a tsakanin mazauna yankin. An gano cewa tankar, wadda ta taso daga Legas tana kan hanyarta na zuwa Kano, ta kife ne da sassafe a garin Takalafiya da ke Ƙaramar Hukumar Lapai ta Jihar Neja. Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a Najeriya Matsalar kashe-kashe a Nijeriya ba ta da alaƙa da addini — Femi Kayode Wani mazaunin garin Lapai, Mallam Mahmud Abubakar, ya shaida wa Aminiya cews lamarin ya faru kimanin kilomita biyu daga garin Lapai. Ya ce kwanan nan aka gyara hanyar NNPCL, amma hanyar ta fara lalacewa...
Kungiyar Kurdawa ‘yan tawaye ta PKK ta sanar da janye dukkan dakarunta daga Türkiyya zuwa arewacin Iraki Kungiyar kurdawa ‘yan tawaye ta PKK ta sanar da janye dukkan dakarunta daga cikin kasar Turkiyya zuwa arewacin Iraki a yau Lahadi. Kafafen yada labarai sun ambato wata sanarwa daga kungiyar ‘yan tawayen kurdawar tana cewa: “Ta janye dukkan mayakanta daga cikin kasar Turkiyya zuwa yankunan arewacin kasar Iraki. A watan Fabrairun da ya gabata ne, Abdullah Ojalan, wanda ya kafa kungiyar Ma’aikata ta Kurdistan (PKK) a Turkiyya, ya yi kira da a rusa kungiyar, yana mai kira ga mayakan kungiyar da su ajiye makamansu su koma ga daukar matakin siyasa. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up...
A gobe Litinin ne za a bude taron kungiyar tattalin arziki ta “Eco” a nan birnin Tehran,kamar yadda mataimakin ministan harkokin cikin gida na Iran Ali Zaini Wand ya sanar. Taron dai za a yi shi ne a matakin ministocin harkokin cikin gida domin Shata hanyoyin aiki a tare a tsakaninsu, bayan da aka dauki shekaru 15, ba a gudanar da shi ba. Ali Zaidani ya kuma yi ishara da cewa taron na wannan karon zai mayar da hankali ne akan hanyoyin bunkasa alaka da kasashen makwabta,musamma bisa la’akari da cewa gundumomin Iran da suke aka iyaka suna da kyakkyawar alaka da kasashen makwabta. Bugu da kari taron na kungiyar “Eco” zai yi kokarin kawar da kalubalen da ake fuskata...
Wannan shi ne daya daga cikin martanin NASENI da abokan huldarta don samar da CNG, wannan kuma na daga shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na daƙile tasirin cire tallafin man fetur ta hanyar samar da iskar gas mai rahusa. Manufar ita ce a rage dogaro da na’urorin lantarki da ake shigowa da su daga waje, da inganta dogaro da kai a ɓangaren fasaha, da samar da ayyukan yi. NASENI tana ba da ababen more rayuwa da tallafin manufofin, yayin da ɓangaren da ke kula da masana’antu, yana mai da hankali kan haɗin gwiwa, ƙirƙira da kasuwanci don kafa Nijeriya a matsayin cibiyar fasahar Afirka. Wannan dabarar da NASENI ta yi ya tabbatar da cewa ba a bar kasar a baya...
“Ban taba tunanin zan zama taurariya a duniya ba.” Daga Yobe Zuwa Fagen Duniya An haife ta a Jihar Kano kuma ta tashi a Yobe, labarin Nafisa ba shi da wuya kamar yadda yake da ban sha’awa. Mahaifinta ya rasu tun tana jaririya, kuma mijin mahaifiyarta mai suna Alhaji Yusuf Umar Kaigama ya rene ta, wanda ya dasa mata dabi’u na tarbiyya da azama. Tana kuma ɗauke da tsatson sarautar zuriyar sarakuna biyu masu daraja ta masarautar Kano, wato Sarkin Kano Ibrahim Dabo da Sarki Abdullahi Maje Karofi. Amma bayan jinin sarautar da take ɗauke dasu, yunwar ta na neman ilimi ya sa ta zama daban. A yanki da matsalar staro ta yi katutu wanda kuma yake dakushe duk wani...
Wannan shi ne daya daga cikin martanin NASENI da abokan huldarta don samar da CNG, wannan kuma na daga shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na daƙile tasirin cire tallafin man fetur ta hanyar samar da iskar gas mai rahusa. Manufar ita ce a rage dogaro da na’urorin lantarki da ake shigowa da su daga waje, da inganta dogaro da kai a ɓangaren fasaha, da samar da ayyukan yi. NASENI tana ba da ababen more rayuwa da tallafin manufofin, yayin da ɓangaren da ke kula da masana’antu, yana mai da hankali kan haɗin gwiwa, ƙirƙira da kasuwanci don kafa Nijeriya a matsayin cibiyar fasahar Afirka. Wannan dabarar da NASENI ta yi ya tabbatar da cewa ba a bar kasar a baya...
Matakatin shugaban Amurka Donald Trump na nada tsohon fira ministan birtaniya Tony Blair a matsayin mai ruwa da tsaki cikin alamuran gaza bayan dakatar da bude wuta ya fuskancin turjiya daga kasashen larabawa da kuma na musulmi, Balair shi ne mutum daya da aka ayyana sunansa daga cikin mambobin kwamitin tabbatar da sulhu da trump ya bada shawara na sanya ido bayan kawo karshen yaki tsakanin bangarorin biyu. Akwai damuwa sosai da shakku kan kasancewar Blair daga cikin masu ruwa da tsaki a alamuran yankin, musamman bayan goyon bayan da ya nuna wajen kai wa iraki hari tare da tsohon shugaban Amurka na wancan lokacin a shekara ta 2003 ,a gefe daya kuma yana kare Isra’ila, jamai’an diplomasiyan larabawa sun...
Rahotanni sun bayyana cewa Tehran za ta karbi bakunci taron ministocin cikin gida na kungiyar Eco a karon farko a cikin shekaru 15 da nufin karfafa tsaro da kuma kara fadada yin aiki tare a bangarorin tattalin arzik,i aladu, da kuma harkokin diplomasiya a yankin. Jami’an iran sun tsinkayi irin alfanu da taron kwanaki 2 zai kawo da zai kunshi jerin tattaunawa tsakanin kasashen da sauran bangarori daban –daban. Wannan taron yana zuwa ne lokacin da kasashen dake mambobi a kungiyar suke fuskantar kalubale , da suka hada da rashin tsaro a iyakoki, da aikata muggan laifuffuka da aka tsara, da kuma rashin zaman tabbas a yankin, iran na nufin fadada ajendar ta hanyar yada aladu da amfani da diplomasiya...
Ana haka ne Gwamna Babagana Umara Zulum ya kai ziyara ƙaramar hukumar, inda ya gana da Misis Duaka a cibiyar lafiya da misalin ƙarfe 8 na dare, lokacin da sauran ma’aikatan duk sun tashi. Wannan aiki na sadaukarwa, juriya da biyayya ga aikinta, ya sa Gwamna Zulum ya fahimci cewa ta himmatu wajen kula da lafiyar mutanen Mafa, mahaifar sa. Gwamnan dai a wasu ziyarce-ziyarcen da ya kai har sau biyu, ya ware ta, ya kuma yaba wa sadaukarwar da ta yi, tare da yaba mata kan yadda ta tsaya tare da jama’arsa duk kuwa it aba ‘yar asalin yankin ba ne. Kyautar kwazo da rikon amana da ta samu ya zo ne a lokacin da Gwamna Zulum, wanda ya...
A gun cikakken zaman taro na hudu na kwamitin kolin JKS na 20 da aka gudanar tun daga ranar 20 zuwa 23 ga wannan wata a nan birnin Beijing, an yi bincike da zartas da shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15, inda aka gabatar da jagora da burika kan yadda za a raya kasar a wannan lokaci, kana an tsara taswirar bunkasa kasar Sin a shekaru 5 mazu zuwa. Ga duk duniya, shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar ba shiri na kasar Sin kawai ba ne, kuma ba kasar Sin ba ce wadda ta fara tsara shirin, amma kasar Sin ita kadai ta kiyaye aiwatar da irin shirin. Sirrin tafiyar da harkokin kasar...
Ba wai nasara kawai ba ce; saƙo ne, cewa masu horarwa na Nijeriya na iya kai wa matakan duniya, kuma ƙwarewar gida har yanzu tana da muhimmanci. Hanyar Da Ba A Yawanta Binta Labarin Madugu ba na nasara cikin dare ɗaya ba ne, yana yi ne sannu a hankali da ƙwarewa mai ɗorewa. Daga farkon ayyukansa na horarwa ya fara da Adamawa United da ƙungiyar mini-football ta Nijeriya, zuwa aiki a matsayin mataimakin mai horarwa a gasar WAFCON huɗu (2012, 2014, 2018, 2022), ya gina suna saboda natsuwa, sassaucin dabaru, da basira. Lokacin da ya karɓi cikakken jagorancin Super Falcons a shekarar 2024, da yawa sun yi shakku kan iya cika takardun zama wasu ƙwararrun masu horarwar na ƙetare da...
Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, wanda Kwamishinan Ruwa, Alhaji Aminu Dodo Iya, ya wakilta, ya jaddada cewa sarautun gargajiya su ne ginshiƙin zaman lafiya da ci-gaban al’umma. Ya ce shugabannin gargajiya na taka rawa wajen haɗa kan jama’a da gwamnati, tare da tabbatar da ɗorewar cigaba a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales October 25, 2025 Manyan Labarai Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce October 25, 2025 Labarai Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa October 25, 2025
Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA Gwamna Yusuf Ya Buƙaci Hukumar NBC Da Ta Sa Ido Kan Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Yanar Gizo Wannan inganci ba wai alama kawai ba ce. Tun daga shekarar 2023, hukumar ta sauƙaƙa sama da Naira biliyan 10 na mayar da kuɗin masu amfani don sulhu kai tsaye, mai iya bin sawu wanda ke nuna cewa dawainiya da gaskiya za a iya auna ta da kuɗi, ba wai da alkawari kawai ba. Jarumta a Zamanin Intanet Wataƙila mafi girman ƙarfin gwiwar FCCPC ya bayyana ne a shekarar 2025 lokacin da ta ɗora tarar Dalar Amurka miliyan 22 kan Meta Platforms saboda ayyukan amfani da bayanai ta...
Kungiyar kwallon kafa ta “Futsal” ta matan Iran ta zura kwallaye 14-0 a wasan da ya hada ta da takwararta ta kasar Bahrain mai masaukin baki. A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai aka bude wasannin nahiyar Asiya na kwallon kafar Futsal a kasar Bahrain. A wasan farkon, kungiyar ta Iran ta sami nasara akan takwararta ta Hong kong ta hanyar zura kwallaye shida. Wasa na biyu da Iran din ta yi shi ne da kungiyar kasar Bahrain, da ta sami galaba da kwallaye 14 da 0. ‘Yan wasan na Iran sun kunshi Fatima Shukrani, Niyayash Rahmani, Dhanaz Bakiri, Haidis Yari da kuma Narjis Amir Muhsini. Ya zuwa yanzu dai kungiyar kwallon Futsal ta Iran tana da maki...
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Kasashen Yamma sun taka dokokin kasa da kasa a batun Iran Mataimakin Ministan Harkokin Wajen kasar Rasha Sergei Ryabkov ya soki matakan ƙasashen Yamma, ciki har da harin soji da suka kai wa Iran da kuma ƙoƙarinsu na sake Sanya mata takunkumi, yana mai cewa, “A wannan yanayin, ƙasashen Yamma sun taka dokokin ƙasa da ƙasa.” Jaridar Kommersant ta ruwaito cewa: Ryabkov ya yi waɗannan kalaman ne a lokacin wani shirin yanar gizo mai taken “Tarihi da Siyasar Yanzu na Manufofin Nukiliya na Rasha da Diflomasiyyar Jama’a a Bangaren Nukiliya,” wanda Cibiyar Makamashi da Tsaro ta shirya. Yayi nuni da cewa: “Yanayin Iran, ƙasashen Yamma sun taka dokokin ƙasa da ƙasa...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Me Ake Fatan Gani A Shirin Sin Na Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar Na Gaba October 23, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Karyata Rahoto Na Zuki-ta-malle Da Wata Cibiyar Binciken Amurka Ta Fitar Game Da Hadin Gwiwar Sin Da Yammacin Afirka October 23, 2025 Daga Birnin Sin An Kammala Taron JKS Inda Aka Amince Da Shawarwari Kan Shirin Ci Gaban Kasar Sin Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 15 October 23, 2025
Yanzu haka kuwa, hankula na kara karkata ga shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 da Sin za ta aiwatar tsakanin shekarar 2026 dake tafe zuwa shekarar 2030, kuma masharhanta na ganin a karon gaba, Sin za ta fadada manufofinta na samar da ci gaba domin dorar da nasarorin da ta riga ta cimma. Muhimman fannonin da ake ganin shirin na iya mayar da hankali a kansu, sun hada da tunkarar kalubalen karuwar kason al’ummar kasar masu tsayin shekaru, da kokarin warware tarnakin kasashen yamma dangane da harkokin cudanyar fasaha, yayin da Sin din ke fafada kirkire-kirkire a cikin gida. Kamar yadda Sin ta riga ta dora dan-ba a fannonin zuba jari don cin gajiyar...
Fadar mulkin kasar Rasha Krimlne ta sanar da cewa, shugaban kasar Valdmir Putin ne ya sa ido akan yadda rundunar dake kula da makaman Nukiliya ta gudanar da rawar daji a sansnain “Blisitiks”. Sanarwar ta kara da cewa, rundunar dake kula da muhimman makakan Nukiliyar kasar ta Rasha ta yi amfani da makamai masu linzami samfurori mabanbanta. Haka nan kuma fadar gwamnatin Rashan ta ce, an gudanar da dukkanin gwaje-gwajen cikin nasara, an kuma yi ne domin tabbatar da cewa rundunar tana cikin shirin ko-ta-kwana. A wani labari mai alaka da Rasha, ma’aikatar harkokin waje ta gargadi kasashen turai akan kokarin bai wa Ukiraniya kudadenta da suke a cikin bankunansu. MA’aikatar harkokin wajen Rasha ya fadawa kasashen turai din cewa...
Kasar Sin Ta Karyata Rahoto Na Zuki-ta-malle Da Wata Cibiyar Binciken Amurka Ta Fitar Game Da Hadin Gwiwar Sin Da Yammacin Afirka
A yau Alhamis 23 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya karyata wani rahoto na zuki-ta-malle da wata cibiyar bincike ta Amurka ta bayar kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ta Yamma. Ya yi nuni da cewa, rahoton ya kawo rudani ga ra’ayoyi na kaifin basira, sannan daga bangare guda kawai aka tattaro shi, kuma har ma ya ruwaito wasu bayanan da ba a tantance ba, tare da shafa kashin kaji da kuma muzanta hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen yammacin Afirka. Wannan ya kasance wani bakon abu a fili kuma abin kyama. An ba da rahoton cewa, cibiyar nazarin al’amura ta Amurka ta Atlantic Council, ta fitar...
An Kammala Taron JKS Inda Aka Amince Da Shawarwari Kan Shirin Ci Gaban Kasar Sin Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 15
A wurin taron, kwamitin tsakiya na JKS ya kafa wasu tsare-tsare da za su zama jagora kan bunkasa harkokin tattalin arziki da walwalar al’umma a cikin shirin na shekaru biyar-biyar na 15 wadanda suka hada da sake tabbatar da shugabancin jam’iyyar baki daya, da sanya kula da mutane a gaba da komai, da neman samun ingantaccen ci gaba, da cikakkiyar zurfafa gyare-gyare a gida, da karfafa cudanya tsakanin kasuwa mai albarka da gwamnati mai kwazon aiki, da kuma tabbatar da samun ci gaba da inganta tsaro. Har ila yau, kwamitin tsakiya na JKS ya shata wasu manyan manufofi game da shirin shekaru biyar-biyar na 15 da suka hada da gagarumar zurfafawa wajen samun ci gaba mai inganci, da ingantacciyar habaka...
A cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, sakamakon matakan takunkumi da kasar Amurka ta dauka kan kamfanonin fasahohin zamani na kasar Sin, kasar Sin ta kara saurin yin kirkire-kirkire a matsayin mai zaman kanta, wanda ya haifar da karuwar sabbin nasarori a fannonin da suka hada da fasahohin kere-kere, da na’urar mutum-mutumi, har ma ta zarce sauran kasashe a wasu muhimman fasahohin zamani. Sa’an nan, dangane da takunkumin da wasu kasashen yammacin duniya suka kakaba mata, kasar Sin ta yi kokarin inganta karfin jure wahalhalu da tabbatar da kiyaye bangaren masana’antu da samar da kayayyaki, tare da rage tasirin matsalolin da kan taso daga waje yadda ya kamata. Wadannan ingantattun hanyoyin mayar da martani ga matsin lamba daga ketare sun nuna...
Masu Tasiri a Kafafen Sada Zumunta sun samu horo kan RMNCAH+N, Tsarin Iyali da Rigakafin Cin Zarafin Mata
Ƙungiyar Centre for Communication and Social Impact (CCSI) tare da haɗin gwiwar abokan aikin ta na EngenderHealth Consortium sun shirya taron horo na yini ɗaya a Kano domin ƙarfafa ƙwarewar ’yan jarida da masu tasiri a kafafen sada zumunta (social media influencers) wajen yada sahihan bayanai da tallafawa manufofin kiwon lafiya da daidaito tsakanin jinsi. Taron, mai taken “Daga Masu Bi zuwa Masu Faɗa Aji: Amfani da Kafafen Sada Zumunta wajen Yaɗa Sawun Lafiya da Daidaito”, ya mayar da hankali ne kan batutuwan Reproductive, Maternal, Newborn, Child, and Adolescent Health plus Nutrition (RMNCAH+N), Family Planning (FP), da Gender, Youth, and Social Inclusion (GYSI). Manufar wannan horo ita ce canza masu tasiri a kafafen sada zumunta zuwa ƙwararrun masu...
Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta bai wa ƙungiyar kwallon ƙafa ta Kano Pillars Football Club sabbin motoci uku domin sauƙaƙa musu matsalolin sufuri a yayin gasar Premier ta shekarar 2025/2026 da ke gudana. Motocin sun haɗa da babbar motar Marcopolo mai kujeru 29 don ɗaukar ’yan wasa, motar samfurin Hummer, da kuma Sharon da za a yi amfani da ita wajen harkokin gudanarwa da sufuri. A lokacin da yake mika makullai da takardun motocin a madadin Gwamnan, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Malam Ibrahim Umar Farouk, ya roƙi matasan jihar masu son wasanni da su ci gaba da zama masu bin doka da oda tare da guje wa duk wani abu da zai...
Gwamnatin Tarayya ta koka da cewa, duk da wayar da kan jama’a da kuma gargadin da ake ci gaba da yi, wasu mutane har yanzu suna kasada da rayukansu ta hanyar yunƙurin ɗibar mai yayin da tankunan dakon mai suka faɗi. Ya jaddada cewa, kowace rai ta ɗan Nijeriya tana da daraja kuma irin wadannan bala’o’in da za a iya rigakafin su, na nuna bukatar kara wayar da kan jama’a game da haɗurran da ke tattare da hakan cikin gaggawa. Ya ce, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), an umurce ta da ta hada karfi ga kokarin Gwamnatin Jihar ta hanyar samar da kayan agaji da taimakon magunguna ga wadanda abin ya shafa da iyalansu. ShareTweetSendShare...
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya tabbatar da aniyarsa ta inganta daidaito tsakanin maza da mata da kuma karfafa jagorancin mata a fannin ilimi a Jihar Jigawa. Shugabar Ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Mohammed, ya bayyana hakan a wani taron da HiLWA ta shirya tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai (EU) a Dakin Taro na Manpower Development Institute. Ya ce bincike ya nuna cewa ko da yake mata su ne mafi rinjaye a aikin koyarwa a Jigawa, suna da kaso 14 bisa 100 ne kacal a mukaman shugabanci, kamar shugabar makaranta ko mataimakiya. Wannan, a cewarsa, yana takaita gudunmawar mata wajen tsara manufofi da ci gaban ilimi. Rahama Ya bayyana cewa matsalolin al’adu, tsarin...
Majalisar dokokin jihar Yobe, ta yi kira ga bangaren zartarwa na gwamnatin jihar da ta dauki matakan gaggawa domin magance yawaitar haduran ababen hawa a garuruwan Ngelzarma, Damagum da Dogon Kuka da ke kan hanyar Damaturu zuwa Potiskum. Majalisar ta yi wannan kiran ne bayan gabatar da kudiri da dan majalisa mai wakiltar mazabar Damagum, Maina Digma Gana, ya yi kan yawaitar hadura a wadannan garuruwa. Waɗanda ke son rusa Kano ba za su yi nasara ba — Sanusi II MTN zai rufe ofisoshi 101 a Kano, Borno da Adamawa saboda gyare-gyare Gana, ya bayyana cewa yawaitar haduran ababen hawa a yankin abun damuwa ne, don haka ya zama wajibi gwamnati ta dauki mataki don kare rayukan jama’a. Ya kara...
Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da shirin gudanar da aikin gyare-gyare a cibiyoyin sadarwa a ranar Asabar, 25 ga watan Oktoba mai zuwa. Ana sa ran aikin zai kawo tsaiko na ɗan lokaci ga sadarwa a wasu sassan jihohin Adamawa, Borno da Kano. Labarin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya ƙarya ne – Sarkin Musulmi Masu kwacen waya sun kashe ma’aikaciyar lafiya a Zariya MTN ya ce aikin zai ɗauki tsawon sa’o’i biyu, daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 8:00 na safe, inda zai shafi ofisoshi 101 na cibiyar sadarwa a cikin ƙananan hukumomi 15 a jihohi ukun. Kamfanin ya ce aikin yana cikin wani dogon shiri na inganta ayyuka da ƙarfafa tsarin sadarwa a Arewacin Najeriya. Aikin...
Babaganaru, ya taɓa jagorantar ƙungiyar inda ya lashe kofunan gasar NPFL guda biyu a shekarun 2011/12 da 2012/13 a lokacin da ya yi aiki a baya. Ana sa ran zai kawo gogewa da a wannan sabon babi na horar da ƙungiyar. A halin yanzu Pillars tana matsayi na 18 a kan teburin gasar bayan wasanni takwas, inda ta samu nasara biyu kacal, ta yi canjaras biyu da kuma rashin nasara huɗu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta October 20, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara October 20, 2025 Wasanni Kano Derby: Barau FC...
Rahotanni su bayyana cewa gwamnatin birtaniya ta sanar a hukumance cire kungiyar tahrirush shams HTS daga cikin jerin kungiyoyin yan ta’adda a wani yunkuri na ganin ta kara kusantar sabuwar gwamnatin siriya bayan faduwar gwamantin Bashar Al-Asad. Gwamnatin birtaniya ta bayyana cewa wannan mataki zai sanya su kara kusanci da gwamnatin siriya da Abu mohammad Al-Jolani ke jagoranta wanda aka fi sani da Ahmed sharaa wanda shi ne shugaban kungiyar Al-Qaida kuma kwamandan Daesh. Wannan sanarwar ta zo ne bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen birtaniya David lammy ya kai kasar siriya a watan yuli, wanda ya sanya ya zama shi ne babban jami’in diplomasiya da ya kai ziyara kasar a tsawon shekaru. Kuma mataki yazo ne duk da hujjoji...
Kasar Sin ta kammala ginin wata cibiyar adana bayanai, irinta ta farko dake karkashin teku kuma mai amfani da lantarki daga karfin iska wato (UDC), wanda aka samar a birnin Shanghai na gabashin kasar. Cibiyar ta zama wani maunin inganci ta fuskar samar da kayayyakin sarrafa bayanai. Cibiyar UDC wadda ke da mazauni a yankin Lingang na Shanghai, wanda yanki ne na kulla cinikayya cikin ‘yanci, ta samu jarin yuan biliyan 1.6, kwatankwacin kimanin dala miliyan 226, kuma tana da karfin lantarki da ya kai megawatt 24. A cewar kwamitin gudanar da harkokin yankin Lingang, kammala aikin wata babbar nasara ce ga aikin samar da cibiyar UDC da kuma makamashi mai tsafta dake cikin teku. Ya kuma nuna yadda aka...
Ya ƙara da cewa shirin ya dace da shirin jihar, inda zai mayar da hankali kan bunƙasa samar da abinci a gida da karfafa matan gida wajen kula da abinci mai gina jiki. Gwamnan ya bayyana cewa majalisar kula da abinci ta jihar za ta jagoranci tsara manufofi, haɗin kai da kuma kula da aiwatar da shirin a dukkanin kananan hukumomin jihar. “Mun ƙuduri aniyar tabbatar da cewa wannan shiri ya ɗore tare da haɗin kan gwamnati da abokan hulɗa,” in ji shi. A nasa ɓangaren, kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsare, Hon. Abdulmalik Gajam, ya ce gwamnatin Gwamna Lawal na taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkar lafiya da abinci mai gina jiki ga yara ƙanana. Haka kuma, Misis Uju Rochas...
Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin cikinta game da gobarar tankar mai da ta tashi a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja, inda mutane 38 suka rasa rayukansu. A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta jajanta wa jama’a da gwamnatin Jihar Neja, musamman iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma Gwamna Mohammed Umar Bago. Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya “Tunaninmu yana tare da iyalan da wannan mummunan lamari ya shafa. Muna godiya ga ma’aikatan agajin gaggawa bisa taimakon da suka bai wa waɗanda abin ya rutsa da su,”...
Wasu da ake zargin masu kwacen waya ne sun kashe ma’aikaciyar jinya a Asibitin Gambo Sawaba da ke Zariya a jihar Kaduna mai suna Hadiza Musa. Bayanai sun ce marigayiyar it ace mataimakiyar shugabar sashen haihuwa a asibitin. Majalisa ta soma binciken yadda aka kashe $4.6bn na tallafin kiwon lafiya Gwamna Bala Mohammed ya ƙirƙiri sabbin masarautu 13 a Bauchi Mijinta, Hamza Ibrahim Idris, wanda ke aiki a Abuja, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kashe matarsa ne a ranar Asabar yayin da take dawowa daga aiki. “A ranar Asabar, ta kira ni ta ce za ta je wajen gyaran gashi sannan ta ziyarci wani shagon masu magani a Filin Mallawa, Tudun Wada Zariya, kuma na amince.”...
A ranar 30 ga watan Mayun bana, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci bikin sanya hannu kan yarjejeniyar da ta tabbatar da kafuwar kungiyar IOMed, kuma a madadin kasar Sin, ya sanya hannu kan yarjejeniyar aikinta a yankin musamman na Hong Kong. Tun daga watan Agustan bana, kasashe 37 sun sanya hannu kan yarjejeniyar kafuwar kungiyar, kana takwas daga cikinsu sun amince da fara aiwatar da ita. A matsayin wadda ta gabatar da shawarar kafa IOMed, kuma mai masaukinta, kasar Sin na kira ga karin kasashe da su gaggauta shiga kungiyar, su kuma shiga a dama da su cikin hadin gwiwar kut-da-kut na ayyukanta, kana su samar da sabuwar gudunmawa ga wanzuwar zaman lafiya da...
Kasar Sin ta kammala ginin wata cibiyar adana bayanai, irinta ta farko dake karkashin teku kuma mai amfani da lantarki daga karfin iska wato (UDC), wanda aka samar a birnin Shanghai na gabashin kasar. Cibiyar ta zama wani mizanin inganci ta fuskar samar da kayayyakin sarrafa bayanai. Cibiyar UDC wadda ke da mazauni a yankin Lingang na Shanghai, wanda yanki ne na gwajin cinikayya cikin ‘yanci, ta samu jarin yuan biliyan 1.6, kwatankwacin kimanin dala miliyan 226, kuma tana da karfin lantarki da ya kai megawatt 24. A cewar kwamitin gudanar da harkokin yankin Lingang, kammala aikin wata babbar nasara ce ga hadadden aikin samar da cibiyar UDC da kuma makamashi mai tsafta dake cikin teku. Ya kuma nuna yadda...
Ana fargabar cewa aƙalla mutum 30 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon fashewar wata tankar man fetur a ƙauyen Essa da ke hanyar Agaei zuwa Bida a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja. Aminiya ta ruwaito cewa, akwai kuma kimanin mutum 40 da suka jikkata wadanda suka wawason kwalfar man fetur bayan kifewar tankar. Bayanai sun ce da misalin karfe 11 na safiyar wannan Talatar ce tankar ta kife a titin Essan da aka bayyana cewa lalacewar hanyar ce ta haddasa hatsarin.
Tsohon shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya fara zaman gidan yari na shekara biyar a gidan yarin La Santé da ke tsakiyar birnin Paris. An same shi da aikata laifin hada baki wajen samun kudaden yakin neman zabensa na shekarar 2007 daga tsohon shugaban Libiya, Muammar Gaddafi. Sarkozy ya musanta aikata laifin, kuma ya nemi a sake shi daga gidan yari yayin da yake neman daukaka kara. Wannan dai shi ne karo na farko a tarihin jamhuriya ta biyar da wani tsohon shugaban kasar zai kwana a gidan yari. Magoya bayansa sun taru da sanyin safiyar yau a wajen gidansa na Paris. A shafin sa na sada zumunta ya yi wa magoya bayansa alkawarin cewa .gaskiya za ta yi nasara....
Bayanai daga Falasdinu na cewa a kalla Falasdinawa 97 ne sojojin Isra’ila suka kashe tare da jikkata wasu 230 tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta fara aiki a Gaza a ranar 10 ga watan Oktoba. A cikin wata sanarwa da ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya fitar, ya ce ‘yan mamayar sun aikata laifuka 80 tun bayan ayyana tsagaita bude wuta, wanda hakan ya saba wa dokokin jin kai na kasa da kasa. Laifukan sun hada da harbin bindiga kai tsaye kan fararen hula da gangan, da kama fararen hula. A cewar sanarwar, sojojin na Isra’ila sun yi amfani da motocin soji, tankunan yaki da aka jibge a gefuna da wuraren zama, da jirage marasa, lamarin da...
DSS ta gurfanar da su bisa tuhumar laifuka 32 da suka shafi ta’addanci. Usman ya amsa laifi ɗaya kacal na haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, amma ya musanta sauran. Abba kuwa ya ƙi amsa dukkanin laifukan da ake tuhumar sa da su. An zarge su da kai hari sansanin soja na Wawa da ke Jihar Neja, sace mutane, samar da kuɗin ta’addanci, da kuma samun horo a ƙasar Mali daga wata ƙungiyar ta’addanci ta waje. Haka kuma DSS ta ce sun sace jami’in Kwastam da wani jami’in Shige da Fice wanda ya mutu a hannunsu, tare da karɓar kuɗin fansa na miliyoyin Naira daga iyalan waɗanda suka sace kafin a kama su. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai NLC...
Sinawa kan ce, bisa mataki mataki ake yin tafiya tsawo. Lallai nasarorin da kasar Sin ta cimma, sun faru ne sakamakon yadda al’ummomin kasar suka hada karfi da karfe a karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma suka yi ta yin kokari ba tare da kasala ba bisa shirye-shiryen raya kasa da gwamnati ta tsara na shekaru biyar biyar. Shirye-shiryen cike suke da burikan da kasar Sin ke neman cimmawa, wadanda kuma suka shaida kokarin da al’ummar kasar suka yi da ma wahalhalun da suka sha. Idan aka fara wani sabon shirin, to, an bude sabon babi na bunkasa kasar ke nan. Ma iya cewa, tarihin shirye-shiryen raya tattalin arziki da zaman al’umma na kasar Sin na shekaru...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira October 20, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing October 20, 2025 Daga Birnin Sin Alkaluman GDP Na Sin Sun Fadada Zuwa Kaso 5.2 A Watanni 9 Na Farkon Bana October 20, 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara October 20, 2025 Labarai Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro October 20, 2025 Labarai Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta October 20, 2025
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Tana tabbatar da yin riko da hakkokin kasarta na kare hakkin mallakar makamashin nukiliya na zaman lafiya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa, a yayin shawarwarin da aka yi a birnin New York da kuma fahimtar da mahukuntan birnin Alkahira suka yi da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, jami’an yammacin duniya da ke bin Amurka, sun bukaci a maido da kudurorin takunkumin da kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya kakaba kan Iran a shekarar 2006 zuwa 2010, to amma kasashen China da Rasha sun fito fili suna adawa da wannan gurguwar tunani tare da jaddada rashin amince da shi. A farkon taron manema labarai...
Kungiyar kare hakkin dan Adama ta Amnesty International ta ce: Gwamnatin Tanzaniya ta wurga yanayin tsoro tare da tsananta danniya gabanin babban zaben kasar Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi mahukuntan Tanzaniya da haifar da yanayin tsoro da kuma tsananta danniya gabanin babban zaben da aka shirya yi a ranar 29 ga watan Oktoba, tare da yin amfani da dabarun yaki da ‘yan adawa, ‘yan jarida, kungiyoyin farar hula, da masu kare hakkin bil’adama. Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin shugaba Samia Hassan na ci gaba da ayyukanta na danniya da suka hada da kama mutane ba bisa ka’ida ba, tilasta bacewar mutane, da kuma kashe-kashen ba bisa ka’ida ba, ba tare da hukunta wadanda suka...
Gwamnan ya kuma buƙaci mambobin majalisar da su kasance masu aiki da faɗakarwa, su kasance kusa da jama’ar yankunansu da kuma shugabannin ƙananan hukumomi. Ya umarce su da su riƙa isar da rahotanni na yau da kullum ga Kwamishinan Tsaro, tare da yin addu’a ga waɗanda suka rasa rayukansu wajen kare al’umma da zaunar da zaman lafiya a jihar. Bugu da ƙari, Gwamna Lawal ya ƙarfafa mambobin majalisar su ƙara haɗin kai da sauran jami’an gwamnati domin tabbatar da ingantacciyar tafiyar da al’amuran mulki da gudanar da ayyukan ci gaba cikin nasara. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta October 20, 2025 Ra'ayi...
Zakaran kyautar Ballon d’Or ta bana, Ousmane Dembele, ya shiga cikin sahun ’yan wasan ƙungiyar Paris Saint-Germain (PSG) da za ta kece raini da Bayer Leverkusen a gasar Champions League, bayan ya shafe makonni shida a jinya. Dembele, wanda ya samu rauni a cinya yayin da yake wakiltar ƙasar Faransa a farkon watan Satumba, ya shafe makonni yana jinya a cibiyar lafiya ta musamman da ke Qatar, kafin komarwarsa atisaye a makon da ya gabata. Gwamnonin Kano, Katsina da Jigawa sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa wutar lantarki Yadda Morocco ta kafa tarihin ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20 Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewa, kociyan PSG, Luis Enrique, zai yi farin ciki da dawowar Dembele, la’akari da yadda...
Gwamnonin Kano da Katsina da na Jigawa sun shiga wata yarjejeniyar haɗin gwiwa kan bunƙasa kasuwar wutar lantarkin jihohin uku. Wannan na zuwa ne bayan gwamnonin sun zuba hannun jari a kamfanin Future Energies Africa (FEA), babban mai zuba jari a kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano wato KEDCO. Kano Pillars ta dakatar da Kocinta An kama ɗan uwan Nnamdi Kanu da lauyansa —Sowore A cewar wata sanarwa da Kwamishinan Wutar Lantarki da Makamashi na Jihar Kano, Dokta Gaddafi Sani Shehu, ya fitar, an cimma yarjejeniyar ne a yayin taron bunƙasa wutar lantarki da aka gudanar a birnin Marrakech, Morocco, daga ranar 16 zuwa 19 ga Oktoba, 2025. Dokta Gaddafi ya bayyana cewa jihohin uku za su yi aiki tare...
Hukumar gudanarwar Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars ta dakatar da Babban Kocinta Ahmed Garba Yaro Yaro da bai ba da shawara ga Kocin, Ogenyi Evans, nan take. Ta kuma nada tsohon kyaftin kuma Mataimakin Koci, Gambo Muhammad nan take, ya jagoranci lamuran fasaha na ƙungiyar. Mai horar da masu tsaron raga, Suleiman Shuaibu, zai taimaka masa, yayin da Koci Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai ba da ƙarin goyon baya har sai an fitar da sabbin umarni. Kungiyar ta dauki wannan mataki ne bayan abin da ta kira “rashin tagomashinta” a Gasar Firimiyar Najeriya (NPFL) ta 2025/2026 da ake ci gaba da yi. Sanarwa da kulob ɗin ta fitar, hukumar gudanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bayan...
Hukumar gudanarwa ta ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sanar da dakatar da Mai Ba da Shawara a harkokin koyarwa na ƙungiyar, Ogenyi Evans, da Babban Koci, Ahmed Garba (Yaro Yaro), saboda rashin gamsasshen sakamako da ƙungiyar ke samu a farkon kakar wasa ta 2025/2026 Nigeria Premier Football League (NPFL). A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne sakamakon jerin sakamakon wasanni marasa kyau da suka gaza cika tsammanin masoya da masu ruwa da tsaki a ƙungiyar. Ya yanzu dai, kungiyar ta Sai Masu Gida ta buga wasanni takwas, inda ta samu nasara a biyu kacal, ta kuma tashi kunnen doki a wasanni 2, sannan suka sha kaye a...
Don haka, an nada “tsohon kaftin din kungiyar kuma mataimakin koci, Gambo Muhammad, tare da mai horar da masu tsaron gida, Suleiman Shuaibu, su maye gurbin wadanda aka sallama na dan wucin gadi. Bugu da kari, Koci Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai taimakawa wadanda aka nada na dan wucin gadin”. LEADERSHIP ta ruwaito cewa, kungiyar mai taken ‘Sai Masu Gida’ tana fama a ‘yan makonnin nan. Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya ta kuma ci tarar kungiyar tarar kudi sama da Naira miliyan 9 biyo bayan rikicin da ya ɓarke a yayin da suke karawa da wata kungiya a filin wasa na Sani Abacha. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A...
Rahotanni da gwamnatin Gaza ta fitar ya nuna cewa sojojin Isra’ila sun keta yarjejeniyar da aka cimma tsakani, har sau 80 wanda haka ya jawo mutuwar falasdinawa 97 da kuma jikkata wasu guda 230 na daban kuma tana ci gaba da cin zarafin wasu a yankunan da ta mamaye. Duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakanin Hamas da Isra’ila a Gaza a kasar Masar, amma isra’ila ta dawo da ci gaba da kai hare harenta , lamari da ya jawo suke daga bangaren jami’an gwamnatin faladinu. Tun bayan da aka sanar da dakatar da bude wuta a gaza sau 80 ke nan isra’ila tana keta yarjeejniyar da sandiyar haka mutane 97 suka mutu wasu guda 230...
Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi ya bayyana kwarin gwiwar cewa, za a iya warware takkadama kan shirin Iran na makamashin nukiliya ne ta hanyar diflomasiyya kadai. Grossi ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Neue Zeitung ta kasar Switzerland a jiya Lahadi. Shugaban hukumar ta IAEA ya ce, masu binciken ba su sami wata shaida da ke nuna cewa Iran ta boye wani adadi na sinadarin uranium da aka inganta ba. Ya kara da cewa, “Yawancin abubuwan da aka samu na Iran an adana su ne a wuraren da aka sani a Isfahan da Fordow, da kuma wani lokaci a Natanz.” in ji shi. Grossi ya bayyana kwarin gwiwa cewa “za a...
Falasdinawa da dama ne su ka yi shahada, yayin da wasu kuma su ka jikkata sanadiyyar hare-haren keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza. Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; An sam shahidai 5 da kuma jikkatar wasu da dama a wani hari da ‘yan sahayoniya su ka kai a wani wurin shan shayi dake yammacin birnin “Deir-Balah” dake tsakiyar yankin Gaza. Haka nan kuma tashar talabijin din ta ce sojojin mamayar sun kai wani harin a garin Zuwaidah, dake tsakiyar zirin Gaza da ya jikkata mutane da dama.Wasu Karin hare-haren na ‘yan sahayoniya sun shafi binin Rafah, da Jabaliya. Kafafen watsa labarun HKI sun sanar da cewa sojojinsu sun kai wasu hare-hare har 20 a Gaza. A...
Sunana Aisha Isah Abubakar (Mai Waka) Gama: A gaskiya bawa yara kanana kudi wannan ba dabi’a ce mai kyau ba, saboda wata rana idan babu wannan kudi da aka sabawa yaro da shi wallahi illa ce babba. Sabida yau da gobe sai Allah idan suka rasa wannan kudi komai zai iya faruwa za su iya saka hannu su diba ako’ina, saboda su biya wa kansu bukatar su. Shawara ya kamata masu dabi’ar aiken yara su basu kudi dan Allah su daina, gara ku siyi ‘sweet’ idan yaro ya dawo a bashi ya fi a dauki kudi a bashi. Allah ya sa mu dace. Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa: To magana ta gaskiya sam-sam hakan bai dace...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da Isra’ila kan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta, tare da yin Allah wadai da ci gaba da rufe mashigar Rafah a matsayin wani mataki na karan tsaye ga sulhun. A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta yi Allah wadai da matakin da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dauka na jinkirta bude mashigar Rafah tare da bayyana hakan a matsayin karya sharuddan tsagaita bude wuta da kuma kaucewa alkawurran da aka dauka ga masu shiga tsakani da masu bada garantin. Kungiyar ta yi gargadin cewa rufewar yana kuma kawo cikas ga zuwan tawagogi na musamman domin zakulo gawarwakin da ke karkashin baraguzan gine gine da kuma gano wadanda suka mutu,...
Yanzu kuma za a ci gaba da tattaunawa kan yadda za a aiwatar da sauran sharuddan da ke ke kunshe a yarjejeniyar. Masu sanya ido na ganin cewa aikin sake ginan yankin Gaza wanda aka rushe kusan daukacinsa a yakin da aka yi na shekara biyu, zai zama babban kalubale. Wannan ce ranar da kowa ke jira -Trump A lokacin da Donald Trump ya yi jawabi, ya bayyana yau a matsayin “ranar da kowa ya yi ta hankoro da addu’ar ganin zuwan ta.” Shugaban na Amurka ya ce “Wannan yarjejeniya mai matukar tarihi” wadda gungun shugabannin duniya suka sanya wa hannu, na nuna cewa “addu’ar miliyoyin al’umma ta karbu”. Daga nan sai ya ce shugabannin sun samu nasarar...
A ta bakin shugaban bikin, kuma gwamnan Jihar Tillabery Maina Boukar, taron na wannan karo ya shaida aniyar gwamnatin Nijar, ta bai wa wadanda suka rungumi shirin ajiye makamai damar sauya rayuwarsu, da taimaka musu wajen cimma nasarar komawa cikin al’umma cikin mutunci. Boukar ya ce, “Wannan muhimmin zabi, ya nuna aniyar gwamnatin Nijar ta kare ikon mulkin kai, da wanzar da tsaro, da tabbatar da zaman lafiya karkashin kyawawan manufofin kasa, ba tare da dogaro ga wasu ajandoji daga ketare ba.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi October 19, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki October 18, 2025...
Ya bayyana cewa a ‘yan watannin da suka gabata, rundunar ta kara kaimi wajen kai samame a wuraren da ake zargin yin laifuka a fadin jihar, a wani bangare na kokarinta na rage yawan shan miyagun kwayoyi da laifukan da suka shafi hakan, wadanda hukumomi ke cewa sau da dama su kan zama sanadin tashin hankali da aikata laifuka musamman tsakanin matasa. “Lokacin da barayin suka hango tawagar sintiri na kusantowa, sai suka tsere, suka bar tarin miyagun kwayoyi da wasu haramtattun abubuwa a wurin,” in ji Abdullahi. Mai magana da yawun rundunar ya lissafa abubuwan da aka kwato da suka hada da kwayoyin “Suck and Die,” Tramadol da Diazepam, inda ya ce an kwashe su gaba daya...
Ya ce “Daga wancan lokacin zuwa yanzu, mun rasa Farsesoshi 309,wasu sun je Jami’oi masu zaman kansu a Nijeriya, sauran wasu sun je London, Saudi Arebiya, Kameroon da kuma wasu kasashe.Kwarrunmu wadanda babban jari ne suna barin aiki saboda sharuddan aikinsu babu wani abin jin dadin da zai sasu ci gaba da kasancewa wuraren aikinsu na koyarwa kamar yadda ya ce,”. Sabo ya bayyana cewa kungiyar za ta fara yajin aikin mako biyu daga ranar Litinin, idan har gwamnatin tarayya ta ci gaba watsi da maganar bukatunta da kuma inganta masu sharuddan aiki. “Mun yi shiru har abin ya wuce misali.Hakkin mune nu ceto jami’oin gwamnati. Idan har gwamnati ta ci gaba da yin biris da mu, ba...
Georgieba ta kuma gargadi duniya kan barazanar da fitar da kudade ta haramtacciyar hanya (IFFs) ke yi, inda ta ce wannan matsala ta zama babbar abin da ke lalata tattalin arziki da tsarin kudi na kasashe a fadin duniya. A cewarta, fitar da kudade ta haramtacciyar hanya wacce ta hada da satar kudaden gwamnati, kudaden da suka fito daga ayyukan laifi, da mu’amalolin dijital da ba a iya bibiyarsu na ci gaba da lalata tsarin mulki, rage kudaden gwamnati, da durkusar da kokarin ci gaba, musamman a kasashe masu tasowa. A cikin wani jawabin manufofi na baya-bayan nan, jami’an IMF sun bayyana cewa IFFs yanzu suna zuwa ta fannoni da dama. Wannan ya hada da karkatar da kudaden...
An gudanar da bikin bayar da lambar yabo ta wasan kwallon kafa na Asiya da Futsal na shekarar 2025 a birnin Riyadh na kasar Saudiyya. A bangaren mata kuwa, Marzieh Jafari, shugabar kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Iran, ita ce babbar mai horar da mata, yayin da Salar Aghapour ta lashe kyautar ‘yar wasa mafi nuna kwazo a wasan Futsal a wannan shekara. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran: Kudurin Kwamitin Tsaro Kan Yarjeniyar JCPOA Ya Kawo Karshe A Yau...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fidda bayani kan cewa daga yau Asabar 18 ga watan Octoban shekara ta 2025, kudurin kwamitin tsaro na MDD wanda aka samar don goyon bayan aiwatar da yarjeniyar Nukliyar kasar Iran wacce aka fi sani da JCPOA ya kawo karshe. Don haka daga yau shirin Nukliyar kasar Iran ta koma karkashen yarjeniyar NPT, kuma za’a yi mu’amala da shirin kamar sauran kasashen karkashin kula na hukumar IAEA. Tsahar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na bada wannan sanarwan a safiyar Asabar ta kara da cewa dama kudurin na tsawon shekaru goma ne daga yau ta gama aiki. Daga yau shirin Nukliyar JMI zai ci gab aba tare da wani karin ka’idojin...
Abokan Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya Sun Ce: Sake Dawo Da Takunkumin Da Aka Kakaba Kan Iran Baya Kan Doka
Abokan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa: Sake dawo da takunkumi bayan karewarsa baya da wani tushe na doka ko tsari Kungiyar aminan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wata sanarwa game da cikar kudiri mai lamba 2231 kan yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran a ranar 18 ga watan Oktoba, inda ta bayyana cewa matakin da Amurka da Turai suka dauka na sake daukar matakin kakaba takunkumin da ya kare kan wata kasa tsari ne da baya ya kan wani tushe na doka ko yarjejeniyar kasa da kasa. Kungiyar aminan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wata sanarwa a ranar Alhamis da ke nuna cikar kuduri mai lamba 2231 na kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya...
Kungiyar Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani da su matsa wa haramtacciyar kasar Isra’ila lamba kan aiwatar da sharuddan yarjejeniyar Gaza Kungiyar Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani da su ci gaba da taka rawa wajen bin diddigin aiwatar da sauran tanade-tanaden yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, musamman ma wadanda suka shafi shigar da adadin taimakon da ake bukata. A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta jaddada bukatar gaggauta fara kafa kwamitin tallafawa al’umma domin fara gudanar da ayyukansa na gudanar da harkokin yankin zirin Gaza. Kungiyar Hamas ta bayyana jin dadin ta ga kokarin da masu shiga tsakani a Masar, Qatar, da Turkiyya suka yi na cimma yarjejeniyar dakatar da yakin wuce...
Dantsoho ya sanar da haka ne, bayan kaddamar dashi a matsayin Mataimakin Shugaban Kungiyar a kwanan baya a wani taro kan harkokin Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya da aka gudanar. Kazalika, Dantsoho ya ci gaba da cewa, zai mayar da hankali ne, kan wanzar da tsarin da NPA, ta sanya a gaba da kara karfafa hadaka, musaman domin a habaka samar da sauki a fannin gudanar da hada-hadar Tashohin Jiragen Ruwa da ke a Afrika ta Yamma. Idan za a iya tunawa, harkar gudanar da Tashoshin Jiragen Ruwa na Afrika ta Yamma na fuskantar kalubale da suka hada da, yin aiki da kayan da suka dade da rashin samar da dawamammen tsari da kuma rashin rungumar yin aiki...
An fara gina magudanan ruwa domin dakile afkuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomin Malam Madori da Kaugama dake jihar Jigawa. Tawagar Injiniyoyin jihar karkashin jagorancin Daraktan kula da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa, Injiniya Mukhtar Muhammad Usman sun ziyarci kananan hukumomin domin duba yadda aikin ke gudana. Haka zalika Daraktan da mataimakin sa Injiniya Mahdi Isyaku da sauran ma’aikata ssn ziyarci wurin da ambaliyar ruwa tayi ta’adi a garin malam Madori. A lokacin da tawagar ta fara auna fili da tona magudanun ruwan, daraktan ya ce an fara aikin tona magudanar ruwa mai tsawon kilomita 2 a matsayin wani ɓangare na aikin karkatar da ruwan da ya lalata wurare zuwa sabon wurin da aka tsara. Yana mai cewar,...
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bi sahun dan rajin kare hakkin dan adam kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, wajen yin kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sakin jagoran kungiyar Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu. A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na D, Atiku, ya bayyana ci gaba da tsare Kanu a matsayin “rashin girmama bin doka a Nijeriya.” Kanu dai, na fuskantar tuhumar ta’addanci ne da cin amanar kasa da kuma nuna tunzura a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, wanda kuma a lokuta da dama yake musanta hakan. Har ila yau, ya kasance a tsare tsawon shekaru duk da hukuncin da kotu ta yanke na bayar da umarnin...
Rahotanni sun bayyana cewa marziyeh Ja’afari ta kafa tarihi inda ta samu kyautar da hukumar kwallon kafa ta asiya ke bayarwa , inda ta zama kociyar da ta kasance zakara a wannan shekara, yayin da Salar Aghapur kuma ya zamo gwarzo a bangare kwallon Fustal na shekara ta 2025 da hukumar AFC ke bayarwa a duk shekara a wani biki da aka gudanar a birnin Riyadh Biki karo na 29 da hukumar kwallon kafa ta Asiya ke shiryawa a duk shekara don mika kyaututtuka ga wadanda suka yi kwazo, kamar wanda yafi iya taka leda, da kociyan da yafi, da kuma kungiyar kwallon kafa da ta fi a wannan shekarar ya gudana ne a kasar Saudiya. Jaafari an girmamata ne...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Ismail Baqaei yayi maraba da dakatar da bude wuta da aka yi tsakanin kasashen Pakistan da Afghanistan, kuma yayi kira ga kasashen biyu da su warware sabanin dake tsakanin ta hanyar tattaunawa da kuma diplomasiya. Iran ta dade tana ba da shawarwarin magance matsalolin tsaro a yammacin Asiya da kuma Kudancin Asiya, da kuma nuna rashin amincewa kan tsoma bakin kasashen waje kan rashin fahimtar dake tsakanin kasashen musulimi, yace rikicin dake tsakanin Kabul da islam abad barazana ce ga zaman lafiya yankin, kuma zai amfanar da kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi masu so su yi amfani da tarzoma a iyaka. Rikicin kan iyaka tsakanin Pakistan da Afghanistan yayi Kamari a yan kwanakin nan inda...
Aƙalla jami’an tsaro takwas, ciki har da ɗan sanda guda ɗaya da masu tsaron al’umma bakwai, sun rasa rayukansu a wani harin kwanton bauna da aka kai musu a hanyar Gusau–Funtua da ke Jihar Zamfara a ranar Alhamis. Lamarin ya faru ne a lokacin da gamayyar jami’an tsaro, waɗanda suka haɗa da ’yan sanda da mambobin rundunar tsaro ta jihar Zamfara ke amsa kiran gaggawa daga kauyen Tungawa da ke ƙaramar hukumar Tsafe. An ceto mutane 3 da aka yi garkuwa da kama wasu a Bauchi Majalisar Dattawa ta amince da Amupitan Shugaban INEC “Maganar da nake yanzu haka, an kwashe gawarwakin jami’an da suka mutu zuwa Gusau domin jana’iza,” in ji wani shaida da aka bayyana sunansa da Tsafe....
Taron wanda ya hada jami’ai daga kungiyar AU da jami’an diplomasiyya daga kasashen Afrika da Sin da masana da sauran jami’ai a nahiyar, ya bayyana muhimmancin hada hadin gwiwar Sin da Afrika da shirin nahiyar na TVET. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa October 16, 2025 Daga Birnin Sin Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar? October 16, 2025 Daga Birnin Sin Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin October 16, 2025
Kafin cimma nasarar hakan, an kwashe sama da shekaru biyu ana gwabza fada da mamaya a Gaza, lamarin da ya haddasa asarar rayuka sama da 67,000, da barnata dukiyoyin da aka kiyasta darajarsu kan kusan dalar Amurka biliyan 70, kana an lalata kusan kaso 90 bisa dari na daukacin gine-ginen dake Gaza, baya ga al’ummun zirin sama da miliyan guda da suka rasa matsugunansu. Ko shakka babu wannan yanayi ya haifar da wani rauni da zai jima ba a manta da radadinsa a tarihin bil’adama ba. Falasdinawa da bangaren al’ummun Israila sun tafka asarar rayuka, da dukiyoyi, da kudaden kashewa a ayyukan soji, da tabarbarewar alakar sassan kasa da kasa, da ganin baiken yaki daga sassa daban daban....
Kungiyar Euro-Med ta bukaci bangarori su shiga Gaza domin tattara bayanai kan kisan kiyashin Isra’ila
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-med mai hedkwata a Geneva ta yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da shiga Gaza ba tare da ‘yan jarida, masu bincike, da masana harkokin shari’a don tattara bayanan kisan kiyashin da Isra’ila a Gaza da kuma hukunta wadanda suka aikata laifin. A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, Hukumar ta ce, biyo bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a Masar ranar Litinin, “Dole ne duniya ta ga abinda ya kasance a Gaza.” Kungiyar ta ce a yanzu dole ne a bar duniya ta ga irin barnar da aka yi, wa matsugunai, da kuma haddassa wahalhalun ga bil adama sanadin yakin da Isra’ila ta yi na...
Ƙungiyar kare muradun Fulani makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta ayyana dakatar da wasu jagororinta daga muƙamin shugabanci a jihohi uku da ke yankin Arewacin ƙasar nan. A wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren hulɗa da jama’a na ƙungiyar na ƙasa ,Ambasada Muhammad Tasiu Sulaiman da aka bayyanawa manema labarai a ranar Alhamis. An ceto mutane 3 da aka yi garkuwa da kama wasu a Bauchi Majalisar Dattawa ta amince da Amupitan Shugaban INEC Ƙungiyar ta ce dakatarwar ya shafi shuganta a Jihar Adamawa Usman Abubakar Yirlabe da na jihar Taraba, Banmi Bello Jane, sai na Jihar Bauchi Muhammad Hussaini Buzaye. Sanarwar ta ƙara da cewa, matakin dakatar da shugabnnin uku ya biyo bayan wasu ƙorafe-ƙorafe ne daga...
Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla tsakanin kungiyar Hamas da Isra’ila, akalla Falasɗinawa uku sun rasa rayukansu a ranar Alhamis sakamakon hare-haren Isra’ila a Gaza, in ji majiyoyin lafiya a yankin. Wata hukumar gwamnatin Isra’ila ta ce zai yi wuya ta buɗe iyakar Rafah da ke tsakanin Gaza da Masar don zirga-zirgar mutane. Za a kafa kamfanin ƙera kayan sola a Kano ’Yan sanda sun kama gungun masu fashi a kan hanyar Katsina zuwa Kano Tuni dai Ministan tsaron Isra’ila ya umarci rundunar sojin kasar da ta yi kwakkwaran shiri don murkushe Hamas muddin ta karya yarjejeniyar tsagaita wutar. A nata bangaren, Hamas ta mayar da gawarwakin wasu Isra’ilawa biyu da ta kama, amma ta amince cewa tana...
Gwamnatin Jihar Kano ta ce nan ba da jimawa ba za a fara ƙera fanel da sauran kayayyakin samar da wutar lantarki daga hasken ranar a jihar. Hakan a cewar gwamnatin ya biyo bayan samun masu zuba jari a fannin na makamashi, bayan rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanoni biyu da suka shahara a fannin, wato Tricell Solar Solutions da IRS Green Energy.. ’Yan sanda sun kama gungun masu fashi a kan hanyar Katsina zuwa Kano Ka da a ɗora wa Tinubu laifin rikicin da ke faruwa a PDP — Fayose An kulla yarjejeniyar ne tare da haɗin gwiwar Hukumar Wutar Lantarki ta Karkara (REA) domin bayar da shawarwari na fasaha da daidaita ayyuka, a yayin taron Sabunta Makamashi na...
Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama gungun mutane 11 da ake zargi da kasancewa ’yan fashi da makami da ke addabar matafiya a kan hanyar Katsina zuwa Kano. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Abubakar Aliyu, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba a Katsina cewa waɗanda ake zargin sun kware wajen tare hanyoyin zuwa Sha’iskawa-Charanchi da Katsina-Kankia-Kano, suna kwace dukiyoyin matafiya. DSS ta cafke tsoffin jami’anta 2 kan aikata zamba Kotu ta daure kocin kwallon kafa a Kano shekara 8 saboda aikata luwadi Ya bayyana sunayen waɗanda aka kama da suka haɗa da Dikko Ma’aru, Dardau Kabir, Muntari Musa, Labaran Amadu, Usman Ma’aru, Lawal Zubairu, Nasiru Sanusi, da Adamu Kabir. Sauran sun haɗa da Abdullahi Zubairu, Muhammad...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a jawabin da ya gabatar a taron tsakiyar shekara ta ministocin harkokin wajen kungiyar yan ba ruwammu wato NAM a birnin Kampala babban birnin kasar Uganda a jiya Laraba, ya jadda bukatar hadin kai da goyon baya a tsakanin kasashen kungiyar, wajen fuskantar rashin mutunta dokokin kasa da kasa da kuma nuna iko na bangare guda. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Araqchi yana cewa yana daga cikin manufofin kafa kungiyar NAMA tabbatar da yencin ko wace kasa a duniya. Don haka akwai bukatar nuna wannan a aikace. Dangane da yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran a cikin watan yunin da ya gabata, Aragchi...
Bayan juyin mulkin da aka yiwa Andry Rajolina a kasar Madagaska kungiyar tarayyar Afirka ta bada sanarwan jingine kasar daga zama mama a cikinta har zuwa abinda hali yayi. \ Tashar talabijin ta Almayadin ta nakalto majiyar kungiyar AU na bada wannan sanarwan, kwana guda bayan da sojoji suka yi juyin mulki wa shugaba Andria Rajolina juyin mulki a tsibirin Madagaska. Sabon shugaban kasar Madagaska Micheil Rondri Yorinina ya bayyana cewa zai yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar zuwa lokacinda kasar zata koma cikin hayyacinta. Sannan a san abinda za’a yi. Mutanen kasar Madagaska dai sun dade suna zanga-zangar bukatar Rajolina ya sauka tunda ya kasa kyautata rayuwar mutanen kasar. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login...
Kasar Afirka Ta Kudu Ta Jaddada Aniyarta Ta Ci Gaba Da Shari’ar Neman Hukunta Isra’ila Kan Batun Gaza
Kasar Afirka ta Kudu tana ci gaba da shari’ar da ta shigar kan gwamnatin mamayar Isra’ila duk da tsagaita bude wuta da aka yi a Gaza Ma’aikatar huldar kasa da kasa da hadin gwiwa ta Afirka ta Kudu ta tabbatar da cewa: Tsagaita bude wuta a zirin Gaza ba zai kawar da laifukan da aka aikata kan fararen hula ba, tana mai jaddada cewa: Karar da aka shigar kan haramtacciyar kasar Isra’ila a gaban kotun kasa da kasa na da nufin hana sake aukuwar keta haddi, ba wai don dakatar da su na wani dan lokaci ba. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a ranar Larabar da ta gabata ta ce: “Tsarin shari’ar ya nuna irin sadaukarwar da...
Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar ‘yan baruwanmu a taronsu karo na 19 da ke gudana a birnin Kampala na kasar Uganda a ranakun 15 da 16 ga wannan wata na Oktoban 2025, sun bayyana matukar damuwarsu kan halin da ake ciki a yankin Caribbean, tare da tabbatar da cikakken goyon bayansu ga Jamhuriyar Venezuela wajen fuskantar duk wata barazana daga waje. Ministocin sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, inda suka nuna matukar damuwa kan yadda lamurra suka kara tabarbarewa sakamakon tura karin sojoji da kayan yaki da Amurka ta jibge a yankin, wanda hakan ke nuni karuwar barazana ta tsaro a daukacin yankin. Haka nan kuma Ministocin sun yi nuni da muhawarar baya bayan nan...
Tsohon ɗan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya ce afuwar shugaban ƙasa ya yi masa, ta ba shi kwarin guiwar yin wata sabuwar tafiyar siyasa. Ya bayyana cewa ya bar tafiyar Kwankwasiyya ne saboda jagorancinta ya yi watsi da shi lokacin da ya fi bukatrsu. ’Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun sace dabbobi a Katsina Kaso 92 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su iya wanke hannu ba — UNICEF Lawan, wanda ya wakilci mazabar Bagwai/Shanono a Jihar Kano, yana cikin mutane 175 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa afuwa a ranar 9 ga watan Oktoba. An kama shi a shekarar 2021 bayan samun sa da laifin karɓar cin hanci a 2012, domin cire sunan wani kamfani daga jerin...
Kwamatin harkokin lafiya na majalisar dokokin jihar Jigawa ya ce gyaran fuskar da aka yiwa dokar da ta kafa asusun adashen gata na kiwon lafiya na jihar ya sahalewa asusun damar samo kudade daga wasu bangarori da ba na gwamnati ba. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Guri, Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari, ya yi wannan tsokaci lokacin da ya jagoranci ‘yan kwamatin domin ziyarar aiki a ofishin asusun da ke Dutse. Ya bayyana bukatar ganin asusun JICHIMA ya nemo kudade daga hannun masu taimakon al’umma da cibiyoyi da ‘yan siyasa da kwamitocin zakka da na waqafi domin bunkasa asusun, ta yadda zai biya bukatun kiwon lafiyar al’ummar jihar. Alhaji Usman Musari ya lura cewar fadada hanyoyin samun kudade ga...
Shugaban Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano (HMB), Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya kai ziyarar ba-zata ta duba aiki a Asibitin karbar Haihuwa na Imamu Wali, na Marmara, da kuma Asibitin Sabon Bakin Zuwo. Ya kai ziyarar ce domin tabbar bin umarnin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na wucin gadi wajen sauya wuraren gudanar da ayyukan karbar haihuwa da na yara zuwa wasu cibiyoyi daban. A karkashin wannan umarni, an mayar da sashen haihuwa na Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase zuwa Asibitin Haihuwa na Imamu Wali, yayin da aka mayar da ayyukan yara kyauta da ake yi a Asibitin Yara na Hasiya Bayero zuwa Asibitin Haihuwa na Marmara. Wadannan canje-canjen sun biyo bayan ci gaba da...
A Lokacin Yaki, Iran Ta Tarwatsa Wata Cibiyar Leken Asirin Yahudawan Sahayoniyya Da Ke Yankin Farar Hula
Iran ta kai hari a wani sansanin sojan Isra’ila na sirri da ke karkashin wata hasumiya a Tel Aviv Yankin Gray, wani dandali ne na bincike, ya bayyana samuwar wani maboyar sirri na sojan Isra’ila da ke karkashin wani hasumiya a Tel Aviv, wanda ake kyautata zaton yana cikin wadanda aka kaiwa hari da makami mai linzami na Iran yayin harin da aka kai ranar 13 ga watan Yuni. Bisa binciken da aka gudanar, dandalin ya gano wurin da wani wurin karkashin kasa da aka fi sani da “Site 81”, wani rukunin jami’an leken asiri na hadin gwiwar sojojin Amurka da Isra’ila da ke karkashin rukunin gidaje na Da Vinci a wata unguwa mai yawan jama’a a tsakiyar birnin Tel...
Kungiyar Jihadul-Islami Ta Falasdinu Ta Ce; ‘Yantar Da Fursunonin Falasdinawa Abu Ne Mai Muhaimmanci
Babban sakataren kungiyar Jihadul-Islami ta Falasdinu ya jaddada cewa: ‘Yantar da sauran fursunonin manufa ce da ba za ta fice daga muhimman abubuwan da suka aka sa a gaba ba Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Jihadul- Islami ta Falasdinu, Ziyad al-Nakhalah, ya tabbatar da cewa: Ba za a taba mantawa da manufar ‘yantar da sauran jajirtattun fursunonin Falasdinu daga gidajen yarin ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya ba saboda yana daga cikin muhimman abubuwan da ‘yan gwagwarmaya suka sa a gaba. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palestine Today cewa: Kwamandan al-Nakhalah ya jaddada a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar litinin cewa: Tutocin gwagwarmaya suna ci gaba da wanzuwa a kasa...
Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya
Daga nan sai kakakin ya ce, “Ba zai yiwu bangaren Amurka ya nemi tattaunawa a bangare guda, alhali a daya hannun yana barazanar kaddamar da sabbin takunkumai kan kasar Sin ba. Wannan ba ita ce hanya mai dacewa ta gudanar da cudanya da Sin ba.” (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani October 14, 2025 Daga Birnin Sin Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa October 14, 2025 Daga Birnin Sin Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin October 14, 2025
Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani
A nata bangare, Sima Bahous ta yabawa ci gaban da Sin ta samu wajen cike gibin fasahohi tsakanin jinsi, da ingiza ci gaban harkokin mata ta kowanne bangare da kare hakkoki da muradun mata. Ta kuma yi kira ga kasa da kasa su hada hannu tare wajen karfafa gwiwar mata da ‘yan mata su samu ci gaba a zamanin amfani da fasahohi. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa October 14, 2025 Daga Birnin Sin Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin October 14, 2025 Daga Birnin Sin Shawarwarin Sin Sun Bude...