Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC
Published: 21st, October 2025 GMT
Kwamandan ya ƙara da cewa yayin yaƙin “Operation Zero” na shekarar da ta gabata (Disamban 2024 zuwa Janairun 2025), mutane 432 ne suka mutu, yayin da 2,070 suka jikkata a haɗura 533; adadin ya ragu idan aka kwatanta da na baya.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sabon Shugaban Hukumar Kidaya, Kwamishinoni da Manyan Sakatarori
Daga Bello Wakili
Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) da kwamishinoni biyu na hukumar, tare da sabbin manyan sakatarori guda biyar da aka nada a gwamnatin tarayya.
Daga nan ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Bayan karanta takardar tarihin rayuwarsu, manyan sakatarorin biyar Abdulkarim Ibrahim, Dr John Ezeamama, Dr Abdul-Sule Garba, Dr Isiaku Mohammed da Dr Ukaire Chigbowu, sun dauki rantsuwar kama aiki, sannan suka sanya hannu a kundin rantsuwa.
An kuma rantsar da Dr Aminu Yusuf, wanda shugaban kasa ya nada a matsayin Shugaban NPC a ranar 9 ga Oktoba, da kwamishinoni biyu ciki har da Dr Tonga Betara daga Jihar.
NPC ita ce hukuma da ke da alhakin gudanar da kidayar jama’a a hukumance, yin rajistar haihuwa da mace-mace, da tattara bayanan kimiyyar jama’a domin tsare-tsare.
Majalisar ta yi shiru na minti guda domin tunawa da tsohuwar Ministar Harkokin Waje, Ambasada Joy Ogwu, wadda ta rasu a ranar Litinin, 13 ga watan Oktoban 2025 tana da shekaru 79.