Aminiya:
2025-12-06@20:20:56 GMT

Gwamnatin Borno rufe makarantun jihar saboda rigakafin ƙyanda da Polio

Published: 22nd, October 2025 GMT

Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya, Fasaha da Kirkire-Kirkire ta Jihar Borno ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun Firamare da Sakandare na gwamnati da masu zaman kansu na tsawon kwanaki biyu domin gudanar da aikin rigakafin cututtukan ƙyanda da shan inna. Sanarwar umarnin rufe makarantun ta fito ne daga ofishin Kwamishinan Ma’aikatar, a ranar Talata, a birnin Maiduguri.

Labarin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya ƙarya ne – Sarkin Musulmi Fashewar tankar mai ta yi ajalin mutum 30 a Neja A cewar sanarwar, za a rufe makarantun daga ranar Alhamis, 23 ga Oktoba, zuwa Juma’a, 24 ga watan Oktoba, 2025. An kuma umarci dukkan makarantun da su ci gaba da ayyukansu daga Litinin, 27 ga Oktoba, 2025, kamar yadda aka saba. An bayyana cewa rufe makarantun na da nasaba da Ranar Rigakafi ta Kasa na shekarar 2025, wanda Ma’aikatar Lafiya da Ayyukan Jinƙai ta Jihar Borno ta shirya. Sanarwar ta ce aikin rigakafin zai shafi yara masu watanni 9 zuwa shekaru 14 domin rigakafin ƙyanda (Rubella), sai shekaru 0 zuwa watanni 59 domin rigakafin shan inna (Polio). Gwamnatin ta bukaci dukkan shugabannin makarantu da sakatarorin ilimi na kananan hukumomin jihar da su tabbatar da bin wannan umarni na rufe makarantu na tsawon kwanaki biyu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Rufe Makarantu rufe makarantun

এছাড়াও পড়ুন:

Kakakin majalisar dokokin Ribas da takwarorinsa 16 sun fice daga PDP zuwa APC

Kakakin Majalisar Dokokin jihar Ribas, Martin Amaewhule tare da mambobin majalisar su 15 sun sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Amaewhule ya bayyana shawarar ’yan majalisar ne a zaman majalisa na ranar Juma’a, inda ya ce akwai abin da ya kira “rarrabuwar kai a fili” a cikin PDP wanda ya sa suka yanke wannan shawara.

Muna tafe da karin bayanai…

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jigawa Ta Bada Kiyasin Kasafin Kudi na Sama da Naira Biliyan 161
  • Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudin 2026 a Gaban Majalisa
  • Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista —Gwamnati
  • Jigajigan Majalisar Ribas 17 Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC
  • Gwamnatin Gombe da UNICEF sun tallafa wa yara masu fama ƙarancin abinci mai gina jiki
  • An harbe manomi saboda rikici kan filin kiwo a Borno
  • DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan Kwara
  • Kakakin majalisar dokokin Ribas da takwarorinsa 16 sun fice daga PDP zuwa APC
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar da Wutar Lantarki a Yankunan Kananan Hukumomin Jihar
  • Mutum 6 sun rasu, 13 sun jikkata a hatsarin mota a Kogi