Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira biliyan ɗaya domin gyaran ajujuwan karatu a wasu makarantu na gwamnati.

Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse.

A cewarsa, majalisar zartarwar jihar ta amince da kashe fiye da Naira miliyan 528 domin gyaran ginin ajujuwa a wasu zababbun makarantu na gwamnati a fadin jihar.

Ya bayyana cewa, manufar aikin ita ce inganta yanayin karatu, tabbatar da tsaro, da kuma samar da iingantaccen ilimi karkashin shirin gwamnatin jihar na farfado da ilimin asali.

Sagir Musa ya kuma ce, majalisar ta amince da kashe sama da Naira miliyan 512 domin  samar da kujeru da gadajen ɗalibai, domin ƙarfafa tsarin ilimi tare da tabbatar da walwala da inganci a makarantu.

 

Usman Mohammed Zaria

 

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa Makarantu

এছাড়াও পড়ুন:

NLC ta sa zare da gwamnati kan yajin aikin ASUU

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni huɗu domin ta warware duk wata tankiya da ke tsakaninta da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da sauran ƙungiyoyin jami’o’i da na manyan makarantu.

Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin ganawa da ’yan jarida a Labour House da ke Abuja.

An maka mahaifi a kotu kan cefanar da gidan ɗansa a Kano APC ta rage wa Mata kuɗin tsayawa takara a Borno

Ajaero ya ce, idan gwamnati ta gaza kammala tattaunawa da ƙungiyoyin cikin wa’adin da ta bayar, NLC ba za ta yi wata-wata ba wajen ɗaukar matakin da ya dace ta hanyar amfani da dukkan wani tanadi da doka ta yi.

Ya kuma bayyana cewa sun gano cewa wasu ƙungiyoyin haɗin gwiwa a ƙarƙashin NLC suna ganawa da jami’an gwamnati ba tare da izini ko umarni daga uwar ƙungiya ba, wanda shi ne dalilin da ya sa yarjejeniyoyi da dama ba a cika su ba.

Jawabin da Kwamared Ajaero ya yi na zuwa ne bayan taron da NLC ta yi da shugabannin ƙungiyoyin jami’o’i ciki har da ASUU, SSANU, NASU da NAAT.

A makon da ya gabata ne ASUU ta ayyana yajin aikin gargaɗi na makonni biyu, bayan ƙarewar wa’adin na kwanaki 14 da ta bai wa gwamnati, dangane da batutuwan da suka shafi walwala da jin daɗin ma’aikata, albashi, da aiwatar da yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya tun a shekarar 2009.

Sai dai Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya ce bai kamata ASUU ta shiga yajin aiki ba, domin a cewar tattaunawa ta ta yi nisa, kuma gwamnati ta saki Naira biliyan 50 na kuɗaɗen alawus ɗin malaman jami’o’i, tare da ware Naira biliyan 150 a cikin Kasafin 2025 domin gyaran jami’o’in.

A yayin taron da NLC ta gudanar, Kwamared Ajaero ya jaddada cewa daga yanzu, ƙungiyar ƙwadago ko wata ƙungiya a ƙarƙashinta ba za ta sake ganawa da jami’an gwamnati ba tare da izini ba, musamman waɗanda ke da alhakin aiwatar da yarjejeniyoyin da ake sanya hannu a kai.

Ya kuma soki matakin da gwamnatin ta ɗauka na amfani da dokar “ba aiki, ba albashi” kan mambobin ASUU yana mai cewa:

“Mun yanke shawarar bai wa gwamnati wa’adin mako huɗu domin ta kammala dukkan tattaunawa a wannan bangare. Mun fara da ASUU, amma matsalolin sun wuce na ASUU kaɗai.

“Idan bayan mako huɗu ba a kammala komai ba, za mu kira taron gaggawa na ƙasa domin ɗaukar matakin gama-gari, wanda dukkan ma’aikata da ƙungiyoyi a faɗin ƙasa za su shiga ciki.”

Ya ƙara da cewa, “Zamanin sanya hannu kan yarjejeniyoyi da yi wa ƙungiyoyin da ke neman haƙƙinsu barazana ya ƙare.

“Wannan batu na ‘ba aiki, ba albashi’ daga yanzu zai zama ‘ba albashi, ba aiki’. Saboda mun gano cewa fiye da kashi 90 cikin 100 na yajin aikin da ake yi a ƙasar nan na faruwa ne saboda rashin cika ƙa’idar yarjejeniyoyi.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 
  • Majalisa ta soma binciken yadda aka kashe $4.6bn na tallafin kiwon lafiya
  • Majalisa Ta Tabbatar Da Yusuf A Matsayin Sabon Shugaban NPC, Wasu 2 A Matsayin Kwamishinoni
  • Uba Sani ya yi wa ma’aikatan manyan makarantu ƙarin kashi 70 a albashi
  • Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Aikin Hanya Akan Kudi Sama Da Naira Biliyan 4
  • EFCC ta ƙwato fiye da naira biliyan 500 a shekara biyu — Shetima
  • Muna Samun Gagarumin Cigaba Wajen Dawo Da Zaman Lafiya A Zamfara-Gwamna Lawal
  • NLC ta sa zare da gwamnati kan yajin aikin ASUU