Aminiya:
2025-10-27@23:15:29 GMT

Alassane Ouattara ya lashe zaɓen Ivory Coast karo na huɗu

Published: 27th, October 2025 GMT

Shugaba Alassane Ouattara, ya sake lashe zaɓen shugabancin ƙasar Ivory Coast wanda ya ba shi sabon wa’adin mulki a karo na huɗu.

Ouattara mai shekaru 83, ya samu kashi 89.77 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, kamar yadda hukumar zaɓe ta ƙasa ta tabbatar a ranar Litinin.

Tinubu ya gana da sabbin hafsoshin tsaro An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi

Fiye da mutane miliyan tara ne suka cancanci kada ƙuri’a a zaben da aka gudanar a ranar Asabar, wanda aka gudanar cikin yanayi na fargaba, bayan da manyan abokan hamayyarsa biyu — tsohon shugaban ƙasa Laurent Gbagbo da tsohon shugaban Credit Suisse, Tidjane Thiam — aka hana su tsayawa takara.

Sakamakon ya nuna cewa, duk da ƙarancin fitowar masu jefa ƙuri’a a wasu sassan ƙasar, Ouattara ya samu rinjaye har ma a yankunan da ake ganin masu adawa ke da tasiri.

Tsohon Ministan Kasuwanci, Jean-Louis Billon ne ya zo na biyu da kashi 3.09 cikin 100, sai kuma matar tsohon shugaban ƙasa, Simone Gbagbo ta samu kaso 2.42, yayin da hukumar zaɓe ta bayyana cewa adadin waɗanda suka kaɗa ƙuri’a sun kai kashi 50.10 cikin 100 — kwatankwacin na shekarar 2020.

Masana harkokin siyasa sun ce rashin halartar manyan ‘yan adawa da kiran su na a ƙaurace wa zaɓen ya sa jama’a da dama suka ƙi ita kaɗa ƙuri’a.

Sai dai duk da nasarar da Ouattara ya samu, jam’iyyun adawa sun ƙi amincewa da sakamakon, inda suka buƙaci a gudanar da sabon zaɓe.

Rahotanni sun ce aƙalla mutane takwas ne suka mutu yayin tarzomar da ta barke kafin zaben, lamarin da ya sa gwamnati ta kafa takunkumin fita da dare a wasu yankuna tare da jibge jami’an tsaro 44,000 don tabbatar da tsaro.

A yanzu haka dai harkokin yau da kullum kamar yadda aka saba sun kankama a birnin Abidjan bayan sanar da sakamakon zaɓen da wasu jaridu ke yabawa a matsayin “zaɓe na kwanciyar hankali,” yayin da wasu ke cewa ya sake nuna rarrabuwar kawuna a ƙasar.

Ouattara ya fara hawa mulkin Ivory Coast ne bayan rikicin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2010-2011 tsakaninsa da Laurent Gbagbo, wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 3,000 daga ɓangarorin magoya bayansu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Alassane Ouattara Ivory Coast Ouattara ya

এছাড়াও পড়ুন:

Sule Lamiɗo na neman takarar Shugaban PDP na Ƙasa

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamiɗo ya bayyana kudirinsa na sayen tikitin neman zama sabon Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa.

Tsohon ministan ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa kudurinsa na ganin an dawo da martabar dimokuraɗiyya da kuma farfaɗo da darajar jam’iyyar yadda take da, ba zai taɓa yankewa ba.

Tsohon gwamnan na Jigawa na cikin sahun farko na wadanda aka kafa jam’iyyar ta PDP da su a Nijeriya, kuma na gaba-gaba a takarar neman zama sabon shugaban jam’iyyar ta PDP daga Arewa maso Yamma.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zeben Ivory Coast: Alassane Ouattara na kan gaba da tazara mai yawa
  • An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi
  • Kamaru : Paul Biya, ya lashe zaben shugaban kasa a karo na takwas
  • Ƙaddamar da Kyautar Jaruman Indomie Karo na 17: Matasan Najeriya Sun Fafata, An Samu Zakaru
  • Paul Biya mai shekara 92 ya lashe zaɓen Kamaru
  • Ƙaddamar da Kyautar Jaruman Indomie Karo Na 17 Yayin Da Zakarun Matasa Suka fafata daga karshe an samu zakaru
  • Sule Lamiɗo na neman takarar Shugaban PDP na Ƙasa
  • ‘Yan Ivory Coast na jiran sakamakon zaben shugaban kasa
  • Yau Ne Ake Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa  A Ivory Coast