2025-10-28@14:58:33 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1907

«Mataimakin Ministan Harkokin Waje»:

    Messi, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau takwas, zai cika shekaru 39 a watan Yuni mai zuwa. Ya ce yana jin daɗin zama a Miami bayan shekaru masu yawa da ya shafe a Barcelona da kuma lokacin da ya yi a Paris Saint-Germain. Messi ya buga wasanni 195 tare da Argentina, inda ya zura ƙwallaye 114, kuma ya taimaka musu wajen lashe manyan kofuna kamar Copa América, Finalissima, da Kofin Duniya na 2022 a Qatar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid October 26, 2025 Wasanni Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni...
    Al’ummar Unguwar Filin Samji da ke garin Katsina sun buƙaci hukumomi su tabbatar da adalci, bisan zargin da ake wa jami’an Hisbah da na Rundunar Tsaron Al’umma na gwamnatin jihar (C-Watch) da harbin mutane da kuma lakaɗa musu duka ba tare da dalili ba. Wata matar aure mai suna Khadija Hamisu Wada ta samu raunuka sakamakon harbin bindiga, yayin da wasu mutane da dama suka ji raunuka bayan an kai musu hari da adduna, wuƙaƙe da sanduna. A cewar mazauna yankin, aƙalla mutane bakwai ne suka ji munanan raunuka a lokacin da abin ya faru. An ruwaito cewa Khadija na dauke da harsasai biyu a ƙugu, kuma likitoci sun gargadi cewa cire su da gaggawa na iya jawo mata matsalar...
    Mataimakin Ministan Harkokin Waje kan Harkokin Siyasa na Iran ya bayyana cewa: Iran ta yi imani da diflomasiyya amma ta yi watsi da duk wata tattaunawar dole da aka tilasta mata Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Harkokin Siyasa na Iran ya jaddada cewa: Iran ta yi imani da diflomasiyya, amma ta yi watsi da duk wata tattaunawa da aka tilasta mata bin duk wani ra’ayin wani bangare guda. Ya jaddada cewa: Warware takaddama cikin lumana zai yiwu ne kawai idan bangarorin biyu suna kan daidaito kuma babu wanda ke neman sanya sharuddansa. A lokacin taron kasa da kasa na hudu na nazarin Iran na zamani, a wani zama mai taken “Iran da Duniya Bayan Yakin Kwanaki 12,” Mataimakin Ministan Harkokin...
    Wani rahoto da hukumar kula da kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta fitar a yau Litinin ya nuna cewa, ribar da manyan masana’antun kasar Sin suka samu cikin watanni tara na farkon shekarar 2025 da muke ciki, ta karu da kashi 3.2 cikin dari. A cewar hukumar ta NBS, masana’antun da ke samun kudaden shiga da suka kai akalla yuan miliyan 20 (kimanin dala miliyan 2.8) a shekara-shekara, sun samu jimillar ribar da ta kai yuan tiriliyan 5.37 a cikin watanni taran. A watan Satumba, ribar da manyan masana’antun ke samu ta farfado sosai, inda ta karu da kashi 21.6 cikin dari a kan na makamancin lokacin a bara, kamar yadda hukumar ta NBS ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare...
    A yau Litinin 27 ga Oktoba, kungiyar jigilar kayayyaki da sayayya ta kasar Sin ta ba da rahoton bayanan ayyukan jigilar kayayyakin dake bukatar kankara a watannin Yuni da Yuli da Agustan bana. Bayanan na nuna cewa, a karkashin jagorar manufofi da bukatun kasuwa, aikin jigilar kayayyakin dake bukatar kankara ya nuna samun ci gaba mai karfi tare da fadada girman kasuwa. Bayanan sun nuna cewa, jimillar da aka samu a wannan bangare a wadannan watanni 3 ta kai tan miliyan 117.3, wadda ta karu da kashi 4.72% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. A cikin watanni 3 na farko na wannan shekara, jimillar jigilar abincin dake bukatar kankara ta kai tan miliyan 309.3, wadda ta karu da...
    Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce kasar Sin a shirye take ta yi aiki wajen kare tsarin cinikayya tsakanin mabanbantan sassa bisa matukar himma, tare da kasancewa cikin shirin aiki tare da dukkanin sassa, don kare martabar cudanyar mabanbantan sassa bisa gaskiya. Li, ya yi tsokacin ne cikin jawabinsa a yau Litinin, yayin taron shugabanni karo na biyar, na cikakkiyar yarjejeniyar kawance ta cinikayya cikin ‘yanci ta yankin Asiya da Fasifik ko RCEP, wanda aka bude a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia. Kazalika, a birnin na Kuala Lumpur, yayin da yake jawabi a dandalin taron kasashen gabashin Asiya karo na 20, Li Qiang ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da mabanbantan sassa, wajen ingiza...
    Mutane biyu ne suka yi shahada, yayin da wasu biyu suka jikkata a harin da Sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan gabashin kasar Lebanon Hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wata mota a garin  Hafir yammacin Ba’alabak sun yi sanadiyyar shahadan mutane biyu tare da jikkata wasu biyu na daban a jiya Lahadi, a cewar wakilin gidan talabijin na Al-Mayadeen a Baka’a. Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hare-haren ne ta hanyar jiregen saman yaki kan motar da take dauke da fararen hula lamarin da ya yi sanadiyyar shahadan ‘yan ƙasar Lebanon biyu, wasu biyu kuma sun ji Rauni. Majiyoyi sun kuma ruwaito cewa: Wani jirgin saman yakin Isra’ila mara matuki ciki ya harba makamai...
    Rundunar Rapid Support Forces ta Dakarun Kai Daukin Gaggawa a Sudan ta karɓe iko da Barbi da El Fasher a daidai lokacin da ake gargaɗin jin kai Rundunar Rapid Support Forces ta Dakarun Kai Daukin Gaggawa ta sanar da gwace iko da birnin El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa, jim kaɗan bayan sanar da ikonta a Barbi a Arewacin Kordofan. Rahotannin cikin gida sun yi gargaɗin jin kai sun yi magana game da kisan gilla da kuma ƙaura daga wurare daban-daban, kuma matsin lamba na ƙasashen duniya yana ƙaruwa don rage lamarin da kuma sauƙaƙe hanyoyin samun agaji zuwa yammacin Sudan. Abubuwan sun ƙaru a jihohin Arewacin Darfur da Arewacin Kordofan bayan da Rundunar Kai Daukin Gaggawa ta...
    Shugaban majalisar Mohammad Baqer Qalibaf ya bayyana cewa, wasika ta hadin gwiwa da Iran, Rasha da China suka aike wa Majalisar Dinkin Duniya a cikin ‘yan kwanakin nan, da ke adawa da yunkurin Turai na sake dawo da takunkumi kan Iran wannan ya nuna hadin gwiwa mai karfi a tsakanin manyan kasashen uku. Ya yi wannan jawabin ne a lokacin wani zaman majalisa a Tehran a ranar Lahadi, mako guda bayan da kasashen uku suka mika wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban Kwamitin  Tsaro wasikarsu, inda suka tabbatar da kawo karshen aikin kuduri mai lamba 2231, wanda ya amince da yarjejeniyar nukiliya ta 2015 wadda Amurka ta yi watsi da ita. “A cikin ‘yan kwanakin nan, mun shaida...
    Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke shirin tafiya kasar Koriya ta Kudu, domin halartar kwarya-kwaryar taron shugabanni karo na 32, na kungiyar hadin-gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pasifik wato APEC, tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar, an gudanar da wani taron tattaunawa, mai taken “Shugabancin duniya da samun wadata tare a yankin Asiya da Pasifik” a nan birnin Beijing, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da jami’ar Yonsei  da gidan talabijin na YTN na Koriya ta Kudu suka shirya tare.   Yayin taron, shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya ce “CMG na fatan yin hadin gwiwa mai zurfi tare da kasashen yankin...
    Sai dai ya yabawa masu ba da agajin gaggawa, da jami’an tsaro da kuma ‘yan sa-kai da suka yi aiki tuƙuru wajen ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su, tare da ba su agaji, yana mai cewa ɗaukin gaggawan da suka kai ya taimaka wajen rage munin ibtila’in. A yayin da take addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa, ƙungiyar Gwamnonin Arewan ta bada tabbacin cewa za ta ci gaba da haɗa hannu da hukumomin tarayya dana jihohin da abin ya shafa don ƙarfafa tsarin rigakafi da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin al’umma.   ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Masu Ƙananan Sana’o’i Biliyan 75 Domin...
    A kwanan nan, wata manufa da aka zartas a yayin wani taron kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ta janyo hankalin al’ummun duniya, wato yadda kasar Sin take neman gaggauta dogaro da kai wajen kirkiro sabbin fasahohi, da zama mai jagorantar ci gaban masana’antun zamani a duniya. Inda dimbin kafofin yada labaru na kasashe daban daban ke ganin cewa, manufar ta nuna muhimmancin da kasar Sin ta dora a bangaren raya kasa ta wata ingantacciyar hanya, da bunkasa fannin kimiyya da fasaha, wadda ita ma ta zame wa sauran kasashe abin koya. Hakika, a wannan zamani da muke ciki, kusan dukkan kasashe suna sa lura kan aikin raya sabbin masana’antu. Saboda ra’ayi na kariyar cinikayya ya haifar da...
      Masu sharhi na wasanni sun bayyana cewa wasan na yau zai kasance mai cike da fasaha da kwarewa, musamman ganin cewa kungiyoyin biyu na da ‘yan wasa matasa masu zafin guiwa kamar Vinicius Jr., Jude Bellingham, da Lamine Yamal, wadanda ke son rubuta sunayensu cikin jerin manyan taurarin da suka taba buga El Classico. Dukkan idanu yanzu sun karkata zuwa Madrid, inda ake jiran ganin wanda zai yi nasara a wannan karon. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu October 25, 2025 Wasanni Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya...
    Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa kwamitin shugaban ƙasa kan ba da tallafi ya ƙaddamar da rabon naira miliyan 50, inda mutum miliyan 1 za su samu naira dubu hamsin kowanensu tare da wasu shirye-shirye na bunƙasa ƙananan sana’o’i.  Ya ƙara da cewa ƙanana da matsaƙaitan sana’o’i a Jihar Katsina za su samu 250,000 daga gwamnatin tarayya wanda zai taimaka wa sana’o’insu wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya  Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatinsa tana aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya wajen ƙirƙirar ayyuka, wanda yanzu haka an samar da kuɗaɗai har naira biliyan 5.5, inda aka raba biliyan ɗaya ga mutane 701 a faɗin jihar.  Gwamna Raɗɗa...
    Waɗannan matsalolin, sun sanya ake yin jigilar  kayan ta kan hanya, a manyan motoci, wanda hakan ya sanya masu ruwa da tsaki a fannin ke ci gaba da kokawa, saboda kuɗaɗen da suke kashewa masu yawa, wajen jigilar kayansu wanda hakan ya saɓawa manufar ta kafa Tashodhin  Jiragen Ruwan ta kantudu. Injiniya Kayode Opeifa Shugaban Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa na ƙasa ya tabbatar da waɗannan matsalolin a taron 2025 Ƙungiyar ‘Yan Jarida Wakilai  da ke ɗauko rahotannin ɓangaren sufuri TCAN, da aka gudanar a jihar Legas. A cewar Kayode, ƙalubalen rashin tsaro, a jihar Neja, hakan ya tilasta Hukumar dakatar da jigilar kayan ta hanyar amfani da Jirgin ƙasa zuwa Kaduna. Sai dai ya bayyana cewa gwamnonin jihohin...
    “Yayin da ake gudanar da samamen bisa ga bayanan sirri daga wasu mazauna garin Farin Ruwa da ke karamar hukumar Shanono, jami’an hadin gwiwa na rundunar yaki da ta’addanci ta rundunar da kuma jami’an rundunar da ke Shanono, sun gudanar da samamen na kwarewa a ranar Juma’a, 24 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 02:00 na dare. Hakan ta sa, an samu nasarar kama wasu mutane biyu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne,” in ji sanarwar.   Kwamishinan ‘yansanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa al’ummar Farin Ruwa, yana mai bayyana yadda suka bayar da bayanan sirrin a matsayin muhimmin abu ga nasarar aikin. Ya bukaci mazauna yankin da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani...
    Ya ƙara da cewa Kaduna ita ce jihar da ta cika ƙa’idojin da aka shimfiɗa a yarjejeniyar Malabo kan saka hannun jari a harkar noma. Shugaban AUDA–NEPAD a Nijeriya, Honarabul Jabir Abdullahi Tsauni, ya yaba wa gwamnatin Jihar Kaduna bisa samar da kuɗaɗen haɗin gwiwa da suka bai wa shirin damar faɗaɗa zuwa dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar. A cewar Tsauni, an horar da ƙanana manoma 345 kan kyawawan hanyoyin noma da kuma dabarun noma masu jituwa da yanayin sauyin yanayi, ciki har da noman lambu na gida irin su tumatir, barkono mai zaƙi, masara, wake, da waken soya. Komashinan noma na Jihar Kaduna, Murtala Dabo, ya bayyana cewa wannan shiri ya nuna yadda Kaduna ke da niyyar mayar...
      Wannan nasara mai ban mamaki ta sa kungiyar Niger Tornadoes ta koma matsayi na biyu a teburin gasar, inda yanzu take da maki 17 a kasan Nasarawa United. Hakazalika, sakamakon ya bar Kano Pillars a cikin mawuyacin hali a gasar yayin da ta ke matsayi na 19 da maki 8 kacal. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus October 25, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15 October 25, 2025 Daga Birnin Sin An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC October 25, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take October 24, 2025
    “Muna godiya ga sadaukarwar da sojoji da hukumomin tsaro ke yi. Wannan wasa tsakanin tsoffin ’yan wasan Barcelona da tsoffin ’yan wasan Afirka shaida ce ta nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu wajen dawo da zaman lafiya,” in ji shi. Tsoffin ’yan wasan Barcelona sun isa Nijeriya domin buga wasa da tsoffin ’yan wasan Afirka a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja, a ranar Asabar, 25 ga watan Oktoba, 2025. Yayin da Matawalle ke tarbarsu a ofishinsa, ya miƙa saƙon maraba da fatan alheri ga tawagar a madadin Gwamnatin Tarayya da al’ummar Nijeriya, inda ya yi musu fatanalheri. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni An Sake Saka Sunan Osimhen A Cikin ‘Yan Takarar Kyautar Gwarzon Dan...
    Mahalifinsa, Chief Thomas Osen Ekpemupolo, da mahaifiyarsa, Mrs. Ewe Ekpemupolo, sun rayu cikin al’umma mai arziƙin mai a lokacin da ake tsaka da nema a yi wa yankinsu adalci. Daga cikin wannan rikicewar ya taso mutum wanda daga baya zai zama ɗan gwagwarmayar Niger Delta don neman daraja, adalci, da samun ikon gashin kai. Sojoji Sun Kama Mutane 69 Masu Fasa Bututun Mai A Yankin Neja-Delta Sojoji Sun Lalata Matatun Mai 20 A Yankin Niger Delta A tsakiyar shekarun 1990, arzikin mai na Nijeriya yana samu wadata a wasu wurare amma ya zama ana barin al’ummomi masu arziƙin mai cikin talauci, gurɓawa, da kuma rashin muryar magana. Ga matashin Tompolo, yin shiru wannan bai zama zaɓi ba.   Gwagwarmaya Da...
    Shugaba Gustavo Petro ya ce, ba wai kawai ba ya wata mu’amala ta kasuwanci da Amurka ba ne, ba shi ma da koda dala kwaya daya a cikin wani asusu na bankunan Amurkan balle a ce an rufe shi. Gustavo ya kara da cewa; ko kadan ba zai taba rusunawa a gaban Amurka ba, ba kuma zai ja da baya ba. A jiya Juma’a da marece ne dai Baitulmalin Amurka ya sanar da kakaba wa shugaban kasar ta Columbia takunkumi. Gustavo ya kuma ci gaba da cewa; Yadda yake fada da yaduwar muggan kwayoyi na shekaru masu tsawo, shi ne ya sa Amurkan ta dauki wannan irin matakin akansa alhali kasarsa Columbia tana taimakawa wajen hana Amurkawan shan hodar Iblis....
    Kasar Iran ta yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan kasar Lebanon Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da hare-haren da yahudawan sahayoniyya suka kai ta sama kan yankunan kudancin Lebanon da kwarin Beka’a na kasar. Baqa’i ya bayyana hare-haren da ‘yan sahayoniyya suka kai a ranar Alhamis a yankunan kudancin da kwarin Beka’a na Lebanon, wadanda suka yi sanadiyyar shahada da kuma raunata wasu fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, ciki har da dalibai a wata makaranta a kwarin Beka’a, tare da bayyana harin a matsayin “laifi na ta’addanci” kuma ya yi suka mai tsanani kan su. Baqa’i ya gabatar da alhini da...
    Gwamnatin kasar Iraki ta yi Allah wadai da matakin da Majalisar Dokokin Isra’ila “Knesset” ta dauka na mamaye yankin Yammacin Kogin Jordan da kuma gine-gine matsugunan yahudawa ‘yan kaka gida ba bisa ka’ida ba Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar Iraki ta bayyana Allah wadai da amincewa da kudurorin biyu na Majalisar Dokokin Isra’ila “Knesset” ta yi da su da nufin sanya kwace iko da mallakar yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye da kuma gudanar da matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida ba bisa ka’ida ba. Ma’aikatar ta ce a cikin wata sanarwa cewa: “Tana bayyana kakkausar suka da Iraki ta yi kan amincewar da Majalisar Dokokin Isra’ila ta yi da kudurorin biyu da nufin kwace iko da mallake yankin Yammacin...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), ya jagoranci wani taron karawa juna sani a ranar 27 ga watan Augusta, domin jin ra’ayoyin wadanda ba ‘yan jam’iyyar ba, dangane da shawarwarin da kwamitin kolin JKS ya gabatar game da tsara shirin raya kasa na shekaru 5 karo na 15, da ke da nufin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar. (Fa’iza Muhammad Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Shugaban Kasar Sin Zai Halarci Taron APEC Da Ziyarar Aiki A Korea Ta Kudu October 24, 2025 Daga Birnin Sin Fahimtar Sabon Tunani: Samar Da Wadata Ga Dukkan Jama’a Ta Daidaita Gibin Dake Tsakanin Hamshakai Da...
    Wasu jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) guda uku da ke hanyarsu ta zuwa jihar Anambra domin shirye-shiryen zaben gwamna na ranar 8 ga Nuwamba, sun shiga hannun ‘yan bindiga a jihar Kogi. Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa an yi garkuwa da jami’an ne a ranar Talata, a ƙauyen Aloma da ke ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi. Tinubu Ya Rantsar Da Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC Sienna da suka ke tafiya da ita ya bayyana a cikin wani kiran waya cewa ƴan bindigar sun tare hanya, suka buɗe musu wuta, har suka lalata gilashin gaban motar, lamarin da ya tilasta...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cikin ‘yan watannin da suka gabata, an sake ganin karuwar hare-haren Boko Haram da ISWAP musamman a yankin Arewa maso Gabas. Kazalika, ko a kwanan nan ma anga irin wadannan hare hare.   Wadannan hare-haren sun fi karkata kan sansanonin sojoji, inda ake samun asarar rayuka da dama, da kuma lalata kayan aikin gwamnati. Rahotanni daga Borno da Yobe da ma wasu sassan kasar nan sun nuna yadda ‘yan ta’adda suka sake samun karfi wajen kai hare-hare cikin dare, tare da amfani da dabaru irin na soji da kuma kayan yaki na zamani. Wannan lamari ya jawo tambaya daga al’umma: shin wannan karin hare-hare alama ce ta dawowar kungiyar Boko Haram da...
    Mutanen da yawansu bai wuce kashi 1 cikin dari a duniya ne ba sun samu wadatar arziki da fiye da kashi 60 cikin dari. Yayin da ake fuskantar matsalar gibin dake tsakanin hamshakai da matalauta a duniya, kasar Sin ta samar da gudummawarta wajen daidaita matsalar. Confucius ya taba cewa, abin damuwa shi ne yadda kowa ba ya samun daidaito, amma ba zama da talauci ba. Kana kasar Sin ta kawar da talauci ga mutane miliyan 100 a cikin shekaru 8, kuma a halin yanzu ana kokarin sa kaimi ga dukkan jama’ar kasar su samu wadata tare, yayin da ake kokarin zamanintarwa irin ta kasar Sin. Kasar Sin ba ta bi hanyar kasashen yammacin duniya wacce ta haifar da matsalar...
    Jami’ar mai aikin tsarawa MDD rahoto akan Falasdinu  Farencesca Albanese ta bayyana cewa; tsagaita wutar yaki da aka yi a Gaza, bai wadatar ba, wajibi ne a kawo karshen tsarin mamaya a Falasdinu. Albanese ta kuma ce Amurka ce take bai wa ‘yan mamaya cikakken goyon baya a kisan kiyashin da take yi wa al’ummar Falasdinu,don haka ya zama wajibi a kawo karshen yadda ‘yan mamayar suke sarrafa albarkatun al’ummar Falasdinu,sannan kuma a tarwatsa tsarin mulkin mallaka na mamaya. A halin da ake ciki a yanzu dai Albanese tana kasar Afirka Ta Kudu, inda take halartar taron shekara-shekara akan “Nelson Mandela” za kuma ta gabatar da jawabai a wurin. Tun a cikin watan Mayu ne dai Amurka ta kakawa ma’aikaciyar...
    A yau Alhamis 23 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya karyata wani rahoto na zuki-ta-malle da wata cibiyar bincike ta Amurka ta bayar kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ta Yamma. Ya yi nuni da cewa, rahoton ya kawo rudani ga ra’ayoyi na kaifin basira, sannan daga bangare guda kawai aka tattaro shi, kuma har ma ya ruwaito wasu bayanan da ba a tantance ba, tare da shafa kashin kaji da kuma muzanta hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen yammacin Afirka. Wannan ya kasance wani bakon abu a fili kuma abin kyama. An ba da rahoton cewa, cibiyar nazarin al’amura ta Amurka ta Atlantic Council, ta fitar...
    Alkalan kotu a Kamaru sun yi watsi da bukatar da jamiyyun adawa suka ka gabatar masu ta neman ko dai su soke wasu sakamakon zaben shugaban kasar ko kuma su soke zaɓen baki daya, inda suka ce za su sanar da sakamako a ranar Litinin, sai dai ta dage lokacin daga baya. Zanga-zanga ta barke a wasu manyan biranen kasar, inda ƴan adawa suka yi zargin an tafka kura-kurai a zaɓen na ranar 12 ga watan Oktoba. Alkalan kotun tsarin mulki sun yi watsi da korafi har takwas da aka gabatar masu, domin a cewar su babu cikakkiyar shaida mai tabbatar da su. Dan takarar ƴan adawa, Issa Tchiroma Bakary ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben, wani...
    Wani mutum mai suna Mallam Surajo Muhammad Shehu ya rasa ’yan uwansa takwas, lokacin da tankar mai ta yi bindiga a garin Essa da ke kan hanyar Agaie zuwa Bida, a Jihar Neja. Lamarin ya auku a ranar Talata, wanda aƙalla mutum 28 ciki har da mata da ƙanana yara, suka rasa rayukansu lokacin da tankar ta kife kuma ta kama da wuta yayin da jama’a ke ƙoƙarin ɗibar mai. Tun da PDP ta bar mulkin Najeriya maguɗin zaɓe ya ragu – Akpabio Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi Wasu da dama sun ji rauni kuma an garzaya da su Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC) da ke Bida. Shehu, ya ce mata ne suka fi...
    A yau Laraba 22 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana cewa, huldar diflomasiyya ta shugabanni na matukar taka rawar gani wajen jagorantar dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka, kuma shugabannin kasashen biyu suna ci gaba da cudanya da kuma sadarwa a tsakaninsu. Shugaban Amurka Trump ya ce, yana sa ran kasashen Sin da Amurka za su cimma matsaya kan batutuwan kasuwanci a taron kolin APEC da za a yi a mako mai zuwa, amma ya ce, watakila shugabannin Sin da Amurka ba za su gana ba a lokacin. Guo Jiakun ya yi wadannan bayanai ne a lokacin da yake amsa tambayoyi game da wannan batu, inda ya yi nuni da...
    Bisa kididdigar da hukumar kula da kudaden kasashen waje ta kasar Sin ta gabatar a yau ranar 22 ga wannan wata, a watan Satumba, yawan kudin da aka yi hada-hadarsu ta fuskar samun kudin shiga da kuma wadanda aka kashe na kamfanoni da daidaikun mutane da sauran hukumomin da ba na banki ba na kasar Sin ya kai dalar Amurka triliyan 1.37, wanda ya karu da kashi 7 cikin dari bisa na watan Agusta. Yawan kudin shiga da na kashewa da ya shafi kudaden kasashen waje na kasar Sin a farkon rabu’i na uku na bana ya kai dalar Amurka triliyan 11.6, wanda ya kai matsayin koli a tarihi, kana ya karu da kashi 10.5 cikin dari bisa na makamancin...
    A cewar sanarwar, “A ranar 15 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 11:00 na rana, wata mata da ke zaune a unguwar Federal Low-Cost, Gombe, ta bayyana cewa a daidai wannan ranar da misalin karfe 2:30 na dare, wani wanda ba ta san ko wanene ba, dauke da wuka ya kai mata hari, inda ya sace mata kayanta.   “Abubuwan da aka sace, sun haɗa da iphone 13 Pro Max, an kimanta kudinta akan ₦800,000, kwamfutar ‘Apple MacBook’ da darajarta ta kai ₦250,000, da agogon ‘Apple’ da darajarsa ta kai ₦35,000, ‘power bank’ na Oraimo wanda darajarsa ta kai ₦30,000, da jakar makaranta akan darajar ₦25,000.”   Abdullahi ya ce, nan take jami’an ‘yansanda na shiyyar suka dauki matakin kama...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars October 22, 2025 Labarai Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta October 20, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara October 20, 2025
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta yi kira ga Maniyyata Aikin Hajjin 2026 da su biya kafin alkalami nan da ranar 14 ga watan Nuwamban 2025. Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Ibrahim Datti ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba 22 ga watan Oktoban 2025. Hukumar wacce ta ce kudin kama kujerar kar su gaza Naira Miliyan Biyu, ta ce Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON, na kokarin sama wa Maniyyata rangwame bisa kudin kujera da ta sanar a baya. Ta kara da cewa duk wanda bai biya ba kafin karshen wa’adin da ta bayar, ba zai sami kujerar Aikin Hajjin Bana ba. Har ila yau Hukumar ta ce Maniyyata za su...
      A cewar ministan, shirin sake gina bangaren samar da kayayyaki da samar da ci gaba wanda na wucin gadi ne tsakanin manufar bunkasa ayyukan masana’antu ta kasar da wa’adinta ya kare da kuma sabuwar manufa ta shimfida tubali mai kwari ga ajandar bunkasa masana’antu ta kasar.   Ya kara da cewa, bangaren samar da kayayyaki wanda ya mamaye kaso 15.3 na alkaluman GDP na Zimbabwe a 2024, shi ne kan gaba wajen ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar. (Mai fassara: Fa’iza) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya  October 21, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da...
    Majalisar zartarwa ta jihar Jigawa ta amince da kashe Naira biliyan 2.55 domin gudanar da binciken na musamman, wanda zai mayar da hankali kan albarkatun mai, gas, da sinadarin uranium, tare da cikakken binciken kimiyyar kasa kan ma’adinai a fadin jihar. A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar, ya bayyana cewa wannan muhimmin shiri na gwamnatin yanzu babban mataki ne na gaba wajen cika alkawarin gwamnati na ganowa da kuma amfani da albarkatun kasa masu tarin yawa da ke cikin jihar Jigawa. A cewarsa, wannan bincike zai samar da bayanai masu muhimmanci game da ma’adinai, da mmn fetur da iskar gas da ke karkashin kasa, wanda zai taimaka wajen yanke shawara mai...
    “Da ba sojoji, da ba za mu iya gudanar da wannan taro cikin kwanciyar hankali ba. Don haka dole mu ci gaba da ƙarfafa musu gwiwa,” in ji shi. Sarkin Musulmi ya kuma nuna damuwa kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo ba tare da tunani ba, inda ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace don tsara amfani da su, inda ya bayyana cewa shi kansa ya taɓa fuskantar matsala bayan yaɗa labaran ƙarya a kansa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta October 22, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin...
    Dr Majid Ghayour Mubarhan kwararre kuma farfesa a jami’ar kiwon lafiya ta birnin mashahada ya samu kyautar hukumar WHO na gabashin meditareniya saboda namijin kokarin da yayi na kirkiro abin da zai kula da kuma kare kamuwa da cututtuka da basa yaduwa, kamar cutar kansa ciwon zuciya da kuma ciwon Sugar. Wannan kyautar tana nuna irin ci gaban da Iran ta samu ne a bangaren kimiyyaa yankin duk da takunkumi da kuma takurawar da take fuskanta daga bangaren kasashen turai dake takaita halartar masana kimiyyar kasar  hallara a matakin kasa da kasa. A duk shekata hukumar lafiya ta duniya tana bada kyauta ga duk wani masanin kimiya da yayi kwazo wajen kirkiro wata fasaha a bangaren lafiyar gama gari,  da...
    Majalisar Dattawa ta amince da sabuwar doka da ta tanadi daurin rai da rai ga duk wanda aka samu da laifin lalata da yaro ko yarinya karama. Dokar na son kare hakkokin kananan yara ne, kuma ta shafi maza da mata baki daya, ba tare da wani zabi na biyan tara ba. Sanata Adams Oshiomhole (Edo ta Arewa), ya ce yara ba su da iko ko yardar wajen amincewa da yin jima’i kuma irin wannan abu na jefa su cikin tashin hankali har abada. Da farko ya ba da shawarar a daure mai laifi na tsawon shekaru 20, amma yawancin sanatoci sun nemi hukunci mafi tsauri. Sanata Muhammad Adamu Aliero (Kebbi ta Tsakiya) ya bayar da shawarar daurin rai da...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Siyasa Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya October 21, 2025 Siyasa Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu October 20, 2025 Siyasa Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027 October 17, 2025
    Piwuna, ya ce gwamnati ta gaza cika alƙawurran da ta ɗauka duk da sanarwar kwanaki 14 da ASUU ta bayar tun a ranar 28 ga Satumba, 2025. Ya ce babu wani abin da aka cimma wanda zai hana ƙungiyar aiwatar da shawarar majalisar zartarwarta na fara yajin aikin. “Dukkanin rassan ASUU a faɗin ƙasar nan an umarce su da su janye ayyukansu daga misalin ƙarfe 12 na dare ranar Litinin,” in ji Piwuna Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin cikin wannan lokaci, za ta ɗauki mataki mafi tsanani bayan kammala yajin aikin gargaɗin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe...
    Piwuna, ya ce gwamnati ta gaza cika alƙawurran da ta ɗauka duk da sanarwar kwanaki 14 da ASUU ta bayar tun a ranar 28 ga Satumba, 2025. Ya ce babu wani abin da aka cimma wanda zai hana ƙungiyar aiwatar da shawarar majalisar zartarwarta na fara yajin aikin. “Dukkanin rassan ASUU a faɗin ƙasar nan an umarce su da su janye ayyukansu daga misalin ƙarfe 12 na dare ranar Litinin,” in ji Piwuna Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin cikin wannan lokaci, za ta ɗauki mataki mafi tsanani bayan kammala yajin aikin gargaɗi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe...
    Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na makonni biyu da ta fara. Ƙungiyar ta kuma bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin wata ɗaya don biyan buƙatunta. Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe ASUU ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta gaza ɗaukar mataki cikin wa’adin da ta bayar, za ta iya komawa yajin aiki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe October 22, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas October...
      A ranar 30 ga watan Mayun bana, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci bikin sanya hannu kan yarjejeniyar da ta tabbatar da kafuwar kungiyar IOMed, kuma a madadin kasar Sin, ya sanya hannu kan yarjejeniyar aikinta a yankin musamman na Hong Kong.   Tun daga watan Agustan bana, kasashe 37 sun sanya hannu kan yarjejeniyar kafuwar kungiyar, kana takwas daga cikinsu sun amince da fara aiwatar da ita. A matsayin wadda ta gabatar da shawarar kafa IOMed, kuma mai masaukinta, kasar Sin na kira ga karin kasashe da su gaggauta shiga kungiyar, su kuma shiga a dama da su cikin hadin gwiwar kut-da-kut na ayyukanta, kana su samar da sabuwar gudunmawa ga wanzuwar zaman lafiya da...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira biliyan ɗaya domin gyaran ajujuwan karatu a wasu makarantu na gwamnati. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse. A cewarsa, majalisar zartarwar jihar ta amince da kashe fiye da Naira miliyan 528 domin gyaran ginin ajujuwa a wasu zababbun makarantu na gwamnati a fadin jihar. Ya bayyana cewa, manufar aikin ita ce inganta yanayin karatu, tabbatar da tsaro, da kuma samar da iingantaccen ilimi karkashin shirin gwamnatin jihar na farfado da ilimin asali. Sagir Musa ya kuma ce, majalisar ta amince da kashe sama da Naira miliyan 512 domin  samar...
      “Wadanda aka nada sun bayyana a gaban kwamitin don tantancewa a ranar Talata, 14 ga Oktoba, 2025,” in ji shi. “Kwamitin bai samu koke ko korafe-korafe ba a kansu, sun nuna shiri da cancanta akan ayyukan da aka zabo su”.   Ya bayyana sunayen wadanda aka tantance a matsayin: “Aminu Yusuf (Jihar Neja) – Shugaba, Joseph Haruna Kigbu (Jihar Nasarawa) – Kwamishina, Tonga Betara Bularafa (jihar Yobe) – Kwamishina. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi October 21, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja October 21, 2025 Manyan...
    Ofishin da yake tafiyar da hukuma a Gaza, ya sanar da cewa daga tsaaita wutar yaki zuwa yanzu adadin motocin dake dauke da abinci da aka bari su ka shiga yankin ba su wuce 986 ba alhali yawansu ya kai 6600. A bisa yarjejeniyar da aka kulla ta tsagaita wutar yaki, adadin motocin da ya kamata a bari su shiga yankin na Gaza, zuwa jiya Litinin 10/21/2025, shi ne 6,600. Daga cikin kayan agajin da ake son shigar da su cikin Gaza da akwai tukwanen Gas na dafa abinci a cikin manyan motocin dakon kaya 14, da kuma wasu motocin 28 masu dauke da makamashin da gidajen Burodi, asibitoi  za su yi aiki da su. Yankin na Gaza dai yana...
    DSS ta gurfanar da su bisa tuhumar laifuka 32 da suka shafi ta’addanci. Usman ya amsa laifi ɗaya kacal na haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, amma ya musanta sauran. Abba kuwa ya ƙi amsa dukkanin laifukan da ake tuhumar sa da su. An zarge su da kai hari sansanin soja na Wawa da ke Jihar Neja, sace mutane, samar da kuɗin ta’addanci, da kuma samun horo a ƙasar Mali daga wata ƙungiyar ta’addanci ta waje. Haka kuma DSS ta ce sun sace jami’in Kwastam da wani jami’in Shige da Fice wanda ya mutu a hannunsu, tare da karɓar kuɗin fansa na miliyoyin Naira daga iyalan waɗanda suka sace kafin a kama su. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai NLC...
    Kwamandan ya ƙara da cewa yayin yaƙin “Operation Zero” na shekarar da ta gabata (Disamban 2024 zuwa Janairun 2025), mutane 432 ne suka mutu, yayin da 2,070 suka jikkata a haɗura 533; adadin ya ragu idan aka kwatanta da na baya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi  October 21, 2025 Labarai ’Yansanda Sun Kama Ɗan Fashi Sanye Da Kayan NYSC A Enugu October 21, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu October 21, 2025
    Wasu direbobi sun bayyana cewa tsarin ya taimaka wajen tabbatar da tsaro, ko da yake  fyana jinkirta tafiya. Wasu kuma sun ce farashin sufuri ya ɗan ƙaru sakamakon sabon tsarin. Mutane da ƙungiyoyin farar hula sun yaba da nasarar, amma sun buƙaci gwamnati ta tabbatar da cewa yaran da aka ceto sun samu kulawa, ilimi, da sake gana su da iyayensu. Dakta Sabo ya ce hukumar sufuri za ta ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro tare da faɗaɗa ayyukanta domin tallafa wa tattalin arziƙin jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara October 20, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da...
    Mahdieh Esfandiari, malamar jami’a ba’iraniya tana daga cikin Iraniyawar da za’a yi musayarta a shirin musayar fursinonin tsakanin JMI da Farans a cikin yan kwanaki masu zawa. Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mataimakin ministan harkokin wajen  kasar Iran Vahid Jalalzadeh yana fadar haka ya kumakara da cewa JMI ta yi amfani da hanyoyin diblomasiyya wandanda sukakai ga musayar fursinonin tsakanin ta da kasar Faransa kuma daga cikin wadanda Faransa zata yi musayar da su har da ita Mahdieh  Esfandiari wacce gwamnatin kasar Faransa ta tsare ta tun watan Maris na wannan shekara saboda ta nuna goyon bayanta a Falasdinawa a shafinta na yanar gizo. Jalalzadeh ya kara da cewa , duk tare da cewa gwamnatin kasar Faransa...
    Kakakin majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Berri ya bayyana cewa babu kuma wata tattaunawa da HKI, bayan da jakadan Amurka na musamman a kasashen Siriya da Lebanon Thomas Barrach ya isar da sako garesu kan cewa HKI ta ki amincewa da tattaunawa kan ficewarta daga wasu yankunan kasar Leabanon da ta mamaye da kuma shata kan iyakar kasashen biyu. Kakakin majalisar ya fadawa Jaridar Asharqul Awasat a jiya litinin kan cewa ba abinda ya rage a halin yanzu, sai kasashen da suke kula da tsagaita wutan da aka cimma da ita a cikin watan Nuwamban shekara ta 2024 su yi aikinsu. Yace su yi aikinsu na tabbatar da cewa HKI ta mutunta yarjeniyar mai lamba 1107 ta MDD wacce ta...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar Cerebral Palsy, wato tsukewar ƙwaƙwalwa, na daga cikin manyan matsalolin lafiyar yara da ke tasowa tun daga haihuwa. Wannan cuta tana faruwa ne sakamakon rauni ko lalacewar wani ɓangare na ƙwaƙwalwa da ke kula da motsi, magana, da daidaiton jiki. A mafi yawan lokuta, cutar tana bayyana ne tun daga ƙuruciya, a wasu lokutan kuma kamar yadda masana kiwon lafiya suka bayyana, cutar na faruwa ne tun kafin a haifi yaro. Ko ta waɗanne irin hanyoyi wannan cuta take kama yaro? NAJERIYA A YAU: Shin Ya Kamata A Saki Shugaban IPOB Nnamdi Kanu? DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan October 20, 2025 Daga Birnin Sin Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira October 20, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing October 20, 2025
    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada cewa yaki da matsalar rashin tsaro a jihar nauyi ne na  gwamnatinsa da sauran masu ruwa da tsaki, da ma al’umma baki. Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Litinin, ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 18 da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Gusau. Sanarwar ta ce, majalisar ta tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi jihar, ciki har da tsaro, ilimi, kiwon lafiya, da cigaban ayyukan raya kasa. Dr. Lawal ya tunatar da mambobin majalisar muhimmancin hadin kan su wajen yaki da rashin tsaro a karkashin wannan gwamnati. “Muna samun...
    Fitaccen jarumin barkwancin finafinan Indiyan nan Asrani ra rasu. Asrani, wanda  asalin sunansa shi ne Govardhan Asrani, ya rasu yana mai shekaru 84, kuma ya shafe sama da shekara 50 yana fitowa a finafinan Indiya, inda ya fito a finafinai sama da 350. Dan wasan finafinan, ya shahara wajen taka rawar barkwanci da kuma ƙaramin jarumi wanda ake kira da mai taimaka wa jarumi wato supporting actor. Daga cikin fina-finansa da suka yi fice akwai Sholay, inda ya fito a matsayin ɗansand da Bawarchi da Chupke-Chupke da Hera Pheri da Muqabla da Dhamaal da Yamla Pagla Deewana da Dillagi da Welcome da Bhool Bhulaiya da Garam Masala da Baghban da The Burning Train da Ajnabee da Seeta aur Geeta da...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Tana tabbatar da yin riko da hakkokin kasarta na kare hakkin mallakar makamashin nukiliya na zaman lafiya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa, a yayin shawarwarin da aka yi a birnin New York da kuma fahimtar da mahukuntan birnin Alkahira suka yi da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, jami’an yammacin duniya da ke bin Amurka, sun bukaci a maido da kudurorin takunkumin da kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya kakaba kan Iran a shekarar 2006 zuwa 2010, to amma kasashen China da Rasha sun fito fili suna adawa da wannan gurguwar tunani tare da jaddada rashin amince da shi. A farkon taron manema labarai...
    Wakilin Amurka na Musamman a kasar Siriya ya matsa kaimi domin ganin kasashen Saudiyya da Lebanon da kuma Siriya sun kulla alakar jakadanci da haramtacciyar kasar Isra’ila Wakilin Amurka na musamman a Siriya Tom Barrack, ya gabatar da manufofinsa na sake fasalin yankin Gabas taTsakiya a siyasance bayan kawo karshen yakin Gaza. A cikin dogon hangen nesa, wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, Barrack ya yi ikirarin cewa abu mafi muhimmanci shi ne samar da zaman lafiya a yankin, da kwance damarar Hizbullah, da shigar da kasashen Labanon da Siriya cikin yarjejeniyoyin kyautata alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya kara da cewa Saudiyya ma tana dab da kyautata alakarta da haramtacciyar kasar Isra’ila. Barrak ya bayyana cewa: Taron Sharm...
      Gwamnan ya kuma buƙaci mambobin majalisar da su kasance masu aiki da faɗakarwa, su kasance kusa da jama’ar yankunansu da kuma shugabannin ƙananan hukumomi. Ya umarce su da su riƙa isar da rahotanni na yau da kullum ga Kwamishinan Tsaro, tare da yin addu’a ga waɗanda suka rasa rayukansu wajen kare al’umma da zaunar da zaman lafiya a jihar.   Bugu da ƙari, Gwamna Lawal ya ƙarfafa mambobin majalisar su ƙara haɗin kai da sauran jami’an gwamnati domin tabbatar da ingantacciyar tafiyar da al’amuran mulki da gudanar da ayyukan ci gaba cikin nasara. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta October 20, 2025 Ra'ayi...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20 October 19, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin October 19, 2025 Daga Birnin Sin Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka October 19, 2025
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Alkalan Najeriya su kasance masu gaskiya, rikon amana da tsoron Allah wajen yanke hukunci. Ya ce duk wata al’umma tana fara rushewa ne idan bangaren shari’a ya lalace. Ya bayyana cewa gwamnati na kokarin inganta walwala da albashin Alkalan domin karfafa ikon cin gashin kansu. Da yake bude taron bita na EFCC da NJI a Abuja, Shugaban  wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta  ya ce adalcin Alkalai ne ginshikin ci gaban kasa. Ya nuna damuwa kan yadda ake jinkirta shari’o’in manyan laifukan rashawa, yana mai cewa an fi hanzarta shari’ar masu laifin yanar gizo. Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ba a taba kare kowa saboda siyasa a gwamnatinsa ba, inda ya bayyana cewa EFCC...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Alkalan Najeriya su kasance masu gaskiya, rikon amana da tsoron Allah wajen yanke hukunci. Ya ce duk wata al’umma tana fara rushewa ne idan bangaren shari’a ya lalace. Ya bayyana cewa gwamnati na kokarin inganta walwala da albashin Alkalan domin karfafa ikon cin gashin kansu. Da yake bude taron bita na EFCC da NJI a Abuja, Shugaban  wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta  ya ce adalcin Alkalai ne ginshikin ci gaban kasa. Ya nuna damuwa kan yadda ake jinkirta shari’o’in manyan laifukan rashawa, yana mai cewa an fi hanzarta shari’ar masu laifin yanar gizo. Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ba a taba kare kowa saboda siyasa a gwamnatinsa ba, inda ya bayyana cewa EFCC...
    Hukumar gudanarwa ta ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sanar da dakatar da Mai Ba da Shawara a harkokin koyarwa na ƙungiyar, Ogenyi Evans, da Babban Koci, Ahmed Garba (Yaro Yaro), saboda rashin gamsasshen sakamako da ƙungiyar ke samu a farkon kakar wasa ta 2025/2026 Nigeria Premier Football League (NPFL).   A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne sakamakon jerin sakamakon wasanni marasa kyau da suka gaza cika tsammanin masoya da masu ruwa da tsaki a ƙungiyar.   Ya yanzu dai, kungiyar ta Sai Masu Gida ta buga wasanni takwas, inda ta samu nasara a biyu kacal, ta kuma tashi kunnen doki a wasanni 2, sannan suka sha kaye a...
    Don haka, an nada “tsohon kaftin din kungiyar kuma mataimakin koci, Gambo Muhammad, tare da mai horar da masu tsaron gida, Suleiman Shuaibu, su maye gurbin wadanda aka sallama na dan wucin gadi. Bugu da kari, Koci Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai taimakawa wadanda aka nada na dan wucin gadin”.   LEADERSHIP ta ruwaito cewa, kungiyar mai taken ‘Sai Masu Gida’ tana fama a ‘yan makonnin nan. Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya ta kuma ci tarar kungiyar tarar kudi sama da Naira miliyan 9 biyo bayan rikicin da ya ɓarke a yayin da suke karawa da wata kungiya a filin wasa na Sani Abacha. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A...
    An ce wanda ake zargi da kisan, sananne ne a garin Zing saboda yawo a kan tituna, sanye da fararen kaya yana yin kamar yana wa’azi.   Wakilinmu ya ruwaito cewa, lamarin da ya faru da misalin karfe 11 na daren ranar Asabar, ya jefa al’ummar garin Zing da kewaye cikin rudani kan hakikanin yanayin lafiyar wanda ake zargin.   “Daga cikin wadanda suka jikkata akwai ’yan banga guda biyu, wadanda a baya suka yi kokarin hana wanda ake zargin shiga jama’a saboda irin halayyarsa,” in ji wani ganau. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta October 20, 2025 Labarai Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC October...
    Gwamnatin kasar Colombia ta bada sanarwan cewa sojojin Amurka wadanda suke cikin ruwan tekun Carabian sun shiga ruwan yankin kasar kuma sun kashe wani mai kama kifi a itasayen da suke yi a cikin tekun don hana abunda suka kira yaki da safarar miyagun kwayoyi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran IP ya nakalto shugaban kasar ta Colombia yana fadar haka a shafinsa X a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa ‘jami’an gwamnatin kasar Amurka sun aikata laifi, inda suka kashe wani dan kasar mu mai suna Alejandro Carranza a cikin tekun Carabian, sannan ya kara da cewa shi ba mai safarar miyagun kwayoyine ba, aikin kamun kifi shi ne aikinsa tun da dadewa. Gustavo Petro ya kara...
    Gwamnatin kasar Colombia ta bada sanarwan cewa sojojin Amurka wadanda suke cikin ruwan tekun Carabian sun shiga ruwan yankin kasar kuma sun kashe wani mai kama kifi a itasayen da suke yi a cikin tekun don hana abunda suka kira yaki da safarar miyagun kwayoyi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran IP ya nakalto shugaban kasar ta Colombia yana fadar haka a shafinsa X a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa ‘jami’an gwamnatin kasar Amurka sun aikata laifi, inda suka kashe wani dan kasar mu mai suna Alejandro Carranza a cikin tekun Carabian, sannan ya kara da cewa shi ba mai safarar miyagun kwayoyine ba, aikin kamun kifi shi ne aikinsa tun da dadewa. Gustavo Petro ya kara...
    Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, wanda ake zargin wanda aka ce shi ne Shugaban kungiyar ‘yan acaɓa reshen Ejiba, ya amsa cewa, ya siyo ƙwayoyin ne a wani shagon sayar da magunguna da ke Egbe domin kai wa abokan hulɗar sa da ke cikin dajin.   Babban sakataren yaɗa labarai na shugaban karamar hukumar Yagba ta yamma, Adeyemi Babarinde Sunday, ya ce an kuma samu wanda ake zargin da kuɗi har ₦600,000, wanda ake zargin kudaden hada-hadar ta’addanci ne. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza October 19, 2025 Labarai Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani October 19, 2025 Manyan...
    Yanzu kuma za a ci gaba da tattaunawa kan yadda za a aiwatar da sauran sharuddan da ke ke kunshe a yarjejeniyar.   Masu sanya ido na ganin cewa aikin sake ginan yankin Gaza wanda aka rushe kusan daukacinsa a yakin da aka yi na shekara biyu, zai zama babban kalubale.   Wannan ce ranar da kowa ke jira -Trump A lokacin da Donald Trump ya yi jawabi, ya bayyana yau a matsayin “ranar da kowa ya yi ta hankoro da addu’ar ganin zuwan ta.” Shugaban na Amurka ya ce “Wannan yarjejeniya mai matukar tarihi” wadda gungun shugabannin duniya suka sanya wa hannu, na nuna cewa “addu’ar miliyoyin al’umma ta karbu”. Daga nan sai ya ce shugabannin sun samu nasarar...
    Wata kotu a Amurka ta yanke hukuncin hana kamfanen samar da kayakin leken asiri na HKI NSO kakkafa na’urar leken asiri a kamfanin sadarwa ta WattsApp saboda ayyukan leken asiri. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya nakalto mai sharia Phyllis Hamilton na cewa kamfanin NSO ya kakkafa na’urarsa ta leken asiri  Pegasus kan wayoyin mutane kimani 1,400 in da na’urar yake kunna camera dau daukar hotuna na mutane, da sauti ko kuma ya shiga ya dauki sakonni masu muhimmanci a cikin wayoyunsu ba tare da sun sani ba. Amma Hamilton bata amince da taran dalar Amurka miliyon  $168  wanda kamfani Meta ta bukata ba. Na’uran leken asiri na Pegasus dai ana tsarashi ne a HKI kuma kamar yadda...
    Majiyar hatkwatan sojojin Najeriya ta musanta labaran da suke yaduwa kan cewa, an fasa gudanar da faretin cika shekaru 65 da samun yencin kan kasar a ranar daya ga watan Octoba ne saboda yunkurin yi wa  shugaba Bola Ahmad Tunubu juyin mulki ne. Jaridar daily Trust ta Najeriya ta nakalto majiyar sojojin kasar na musanta aukuwar haka, kuma tace labarin jita-jita ne wanda bai da kanshin gaskiya a cikinsa. Babu wani kokarin juyin mulki a kasar, inji majiyar. Sojojin sun ce an fasa gudanar da faretin cika shekaru 65 da samun yencin kan kasar ne, saboda bawa shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu damar halattan wasu tarurruka masu muhimmanci a kasashen waje, kuma fasawar bai da dangantaka ko kadan da juyin...
    A ta bakin shugaban bikin, kuma gwamnan Jihar Tillabery Maina Boukar, taron na wannan karo ya shaida aniyar gwamnatin Nijar, ta bai wa wadanda suka rungumi shirin ajiye makamai damar sauya rayuwarsu, da taimaka musu wajen cimma nasarar komawa cikin al’umma cikin mutunci.   Boukar ya ce, “Wannan muhimmin zabi, ya nuna aniyar gwamnatin Nijar ta kare ikon mulkin kai, da wanzar da tsaro, da tabbatar da zaman lafiya karkashin kyawawan manufofin kasa, ba tare da dogaro ga wasu ajandoji daga ketare ba.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi October 19, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki October 18, 2025...
    Gusau, ya ƙara da cewa binciken da ake yi kan wasu jami’ai 16 ba shi da alaƙa da wani juyin mulki, illa kawai don tabbatar da ƙwarewar aikin soja. Ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa dakarun soji suna nan daram da goyon bayan kundin tsarin mulki da kuma gwamnatin Shugaba Tinubu, tare da kira ga jama’a da su yi watsi da wannan rahoton. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna October 18, 2025 Manyan Labarai Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi October 18, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Kuduri mai lamba 2231 ya ƙare aiki a yau A cikin wata wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ministan harkokin wajen kasar Iran ya tabbatar da cewa a karshe kuduri mai lamba 2231 ya kare a yau, kuma duk wani kira na farfado da shi ko dawo da wa’adin kudirorin da ya kare, ba shi da wani tushe na shari’a, kuma ba zai iya haifar da wani tasiri na tilasta aiki da shi ba. Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Sayyid Abbas Araqchi ya aike da wasika zuwa ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da kuma shugaban kwamitin sulhu...
    Ya ce “Daga wancan lokacin zuwa yanzu, mun rasa Farsesoshi 309,wasu sun je Jami’oi masu zaman kansu a Nijeriya, sauran wasu sun je London, Saudi Arebiya, Kameroon da kuma wasu kasashe.Kwarrunmu wadanda babban jari ne suna barin aiki saboda sharuddan aikinsu babu wani abin jin dadin da zai sasu ci gaba da kasancewa wuraren aikinsu na koyarwa kamar yadda ya ce,”.   Sabo ya bayyana cewa kungiyar za ta fara yajin aikin mako biyu daga ranar Litinin, idan har gwamnatin tarayya ta ci gaba watsi da maganar bukatunta da kuma inganta masu sharuddan aiki.   “Mun yi shiru har abin ya wuce misali.Hakkin mune nu ceto jami’oin gwamnati. Idan har gwamnati ta ci gaba da yin biris da mu, ba...
    “Wannan mummunan lamari da ya faru a ranar 11 ga Oktoba, 2025, a Wawa Cantonment, Jihar Neja, ya haifar da yanayi mai cike da tashin hankali, inda mazauna sansanin suka shiga cikin mamaki kan yadda irin wannan abin takaici zai iya faruwa,” in ji wani bangare na sanarwar.   A cewar rundunar sojoji, an gano gawarwakin Lance Corporal Femi da matarsa a cikin gidansu dake gini na 15, daki mai lamba 24, Corporals and Below Kuarters, a cikin sansanin.   Binciken farko ya nuna cewa sojan yana kan aiki a lokacin kuma ya nemi izini daga babban jami’i domin ya kula da wasu harkokin kansa kafin ya dawo aiki.   “Rundunar Sojin Nijeriya tana matukar bakin ciki kan wannan lamari,...
    Mataimakin firaministan kasar Sin, kana jagoran tawagar kasar mai tattauna batutuwan tattalin arziki da cinikayya da tsagin Amurka He Lifeng, ya zanta ta kafar bidiyo da sakataren baitul-malin Amurka Scott Bessent, da wakilin cinikayyar kasar Jamieson Greer a jiya Asabar. Yayin zantawar tasu, jami’an sassan biyu sun amince da gudanar da sabon zagayen tattaunawa game da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya nan ba da jimawa ba. Kazalika, sassan biyu sun yi musayar ra’ayoyi bisa sahihanci, da zurfafa tattaunawa, da musaya mai ma’ana dangane da yadda za a aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, yayin tattaunawarsu ta wayar tarho a farkon shekarar nan, da ma muhimman batutuwa masu nasaba da dangantakar tattalin arziki da cinikayya...
    Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC, za su koma APC a mako mai zuwa. A makonnin da suka gabata, ’yan siyasa da dama daga jam’iyyun adawa suna sauya sheƙa zuwa APC, yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027. HOTUNA: Al’ummar Jihar Neja sun yi addu’o’in neman zaman lafiya Ta’addanci: An fi kashe Musulmi a kan Kiristoci a Najeriya — Jakadan Amurka Idan ba a manta ba, Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya koma APC, sannan Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, shi ma ana sa ran zai sanar da sauya sheƙarsa a hukumance nan ba da jimawa ba. Yilwatda, yayin ganawarsa da mambobin APC a Jos, Jihar Filato, ya ce: “A...
    Ya kara da cewa, Allah ya albarkaci Jihar Taraba da dimbin dabbobi, wanda kuma gwamnatin jihar za ta yi dukkan mai yiwuwa, wajen samar da kayan aiki tare da kara bunkasa fannin kiwo na jihar.   Kazalika, ya sanar da cewa; gwamnatin za kuma ta tabbatar da ta kara bunkasa kasuwancin fannin, musamman domin wadanda suke a fannin su kara samun kudaden shiga tare da kuma kara samar wa da gwamnatin kudaden shiga.   Nicholas, ya sanar da hakan ne, ta bakin wakilinsa Daraktan Kula da Harkokin Dabbobi da ke Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci na jihar, Daudu A. Mbaamo   Kwamishinan ya ci gaba da cewa, har yanzu fannin aikin noma, da shi jihar ta dogara a...
    Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC, za su koma APC a mako mai zuwa. A makonnin da suka gabata, ’yan siyasa da dama daga jam’iyyun adawa suna sauya sheƙa zuwa APC, yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027. HOTUNA: Al’ummar Jihar Neja sun yi addu’o’in neman zaman lafiya Ta’addanci: An fi kashe Musulmi a kan Kiristoci a Najeriya — Jakadan Amurka Idan ba a manta ba, Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya koma APC, sannan Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, shi ma ana sa ran zai sanar da sauya sheƙarsa a hukumance nan ba da jimawa ba. Yilwatda, yayin ganawarsa da mambobin APC a Jos, Jihar Filato, ya ce: “A...
    Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Fulham, Alex Iwobi, na dab da kafa sabon tarihi a gasar Firimiya a matsayin ɗan wasan Nijeriya da ya fi buga wasanni a tarihin gasar. Idan Iwobi ya buga wasan da Fulham za ta kara da Arsenal a filin Craven Cottage yau Asabar, zai zama ɗan wasan Nijeriya na farko da ya kai buga wasanni 299 a Firimiya. A halin yanzu, Iwobi ya buga wasanni 298, inda yake daidai da tsohon ɗan wasan Newcastle United, Shola Ameobi, wanda ya riƙe wannan tarihin tsawon lokaci. Wannan zai kasance babbar nasara ga Iwobi wanda ke da shekaru 29 a duniya, tun da ya fara wasansa na farko a Firimiya ranar 27 ga watan Oktoba, lokacin da Arsenal...
    Dan wasan gaba na Barcelona Robert Lewandowski ba zai buga wasan hamayya tsakanin FC Barcelona da Real Madrid wanda ake yi wa take da El Classico ba bayan da zakarun na Sifaniya suka gano cewa yana fama da rauni a kafarsa ta hagu, dan wasan mai shekaru 37 ya samu rauni ne a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Poland ta buga da kasar Lithuania ranar Lahadi. Lewandowski yana da tsagewar tsoka a cikin femoris na cinyarsa ta hagu,” in ji Barcelona a cikin wata sanarwa, yayin da kafofin yana labarai na Sifaniya suka ruwaito cewa zai iya yin jinyar makonni hudu zuwa shida, Barcelona za ta kara da Real Madrid wadda ke jagorantar gasar La Liga...
      Gwamna Radda ya jaddada cewa hukumomin tsaro kadai ba za su iya fada da ‘yan ta’adda ba, sai dai da gudummuwar ‘yan kasa. Ya yi kira ga ‘yan Nijeria da su zama masu sanya ido da kai rahotanni cikin gaggawa da bayar da ingantattun bayanai ga jami’an tsaro.   Ya yaba wa gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu bisa inganta tsaro da maido da martabar tattalin arzikin kasar nan. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi October 18, 2025 Labarai Fitar Da Kudi Ta Haramtacciyar Hanya Na Kara Dagula Matsalar Tattalin Arziki – IMF October 18, 2025 Labarai Majalisar Wakilai Ta Gayyaci CBN Da...
    An gudanar da bikin bayar da lambar yabo ta wasan kwallon kafa na Asiya da Futsal na shekarar 2025 a birnin Riyadh na kasar Saudiyya. A bangaren mata kuwa, Marzieh Jafari, shugabar kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Iran, ita ce babbar mai horar da mata, yayin da Salar Aghapour ta lashe kyautar ‘yar wasa mafi nuna kwazo a wasan Futsal a wannan  shekara. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran: Kudurin Kwamitin Tsaro Kan Yarjeniyar JCPOA Ya Kawo Karshe A Yau...
    Shagaya ya ce: “Wadannan hanyoyin da bankuna ke amfani da su wajen zaluntar kwastomomi na fiye da kima suna shafar ‘yan kasuwa, masu karamin karfi, dalibai da kuma kungiyoyin da ke cikin mawuyacin hali a wannan yanayin tattalin arziki mai tsanani. Idan ba a gudanar da bincike da daukar mataki cikin gaggawa ba, wannan matsala za ta ci gaba da rage amincewar jama’a ga tsarin banki tare da lalata kokarin shigar da jama’a cikin tsarin hada-hadar kudi.” Bayan amincewa da kudurin, Majalisar Wakilai ta umurci CBN da ta wallafa jerin caje-cajen da aka amince da su cikin sauki, tare da kakabawa bankunan da suka saba dokoki hukunci mai tsanani. ‘Yan majalisar sun kuma bukaci babban banki ya kafa wata hanyar...
      Shin menene makasudin shirya irin wannan taro na masu ruwa da tsaki akan sha’anin ilimi da aka gudanar a yau? Makasudin wannan taro shi ne a fadakar da mutane ayyukan wannan hukuma ta TETFUND da take yi, sannan kuma a yi magana da wadanda suka fi amfana da shi wannan tsari na TETFUND. Kamar jami’ai da makarantu da kuma dalibai sannan kuma a karbi shawarwari ga jama’a akan yadda za a bunkasa wannan aikin na hukumar tallafawa manyan makarantu na gaba da Sakandire a Nijeriya. Wannan shi ne makasudi kuma na farko da ake san a jawo al’umma a ciki su dan abinda ake yi da yadda ake kashe kudaden da kuma yadda ake tarawa da makasudin tara su...
    Hukumar Tsaro ta Najeriya (NSCDC) ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da kare muhimman kadarorin gwamnati a kokarinta na cimma manufar kafa ta. Kwamandan hukumar a Jihar Kaduna, Malam Panam Musa, ya bayyana haka yayin da yake gabatar da wasu mutane uku da ake zargi da lalata kayayyakin gwamnati a gaban manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Kaduna. Kwamanda Musa ya bayyana cewa jami’an hukumar sun cafke wadanda ake zargin ne yayin wani sintiri a kusa da hanyar NNPC da ke Kakau, Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna. Ya ce binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin an kama su ne suna kokarin lalata igiyoyin wutar lantarki na musamman da ke da alaka da wata cibiyar...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da tarwatsa wasu muhimman wurare 21 na ‘yan sahayoniyya a lokacin yakin 12 Kwamandan Dakarun sa-kai na Basij Birgediya Janar Gholamridha Sulaimani ya bayyana cewa: Tunanin kawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin yakin kwanaki 12 da aka yi, wauta ce ta makiya yahudawan sahayoniyya, wadanda suka gaza a yunkurin da suka yi. Ya jaddada cewa: Iran ta lalata muhimman wurare 21 na ‘yan sahayoniyya da makamanta masu linzami a yakin karshe. Birgediya Janar Gholamreza Soleimani ya bayyana a wurin taron tunawa da shahidai a Isfahan cewa: Makiya sun yi tunanin cewa za su iya kawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran nan da kwanaki 10, kuma sun yi niyyar haifar da hargitsi da...
    Sabbin alkaluman da babbar hukumar kula da haraji ta kasar Sin ta bayar yau 17 ga wata sun nuna cewa, a cikin watannin tara na farkon bana, kamfanoni sun kara zuba jari wajen kirkire-kirkire, kuma sabbin masana’antu bisa manyan tsare-tsare sun ci gaba da habaka. Lamarin da ya shaida cewa, ana samun ci gaba cikin sauri wajen raya sabon karfin samar da kayayyaki da hidimomi mai dorewa ta kasar Sin.   Zhang Bin, darektan kwamitin jam’iyyar kwaminis ta Sin dake cibiyar nazarin dabarun tattalin arziki da hada hadar kudi ta kwalejin kimiyyar zamantakewar al’umma ta kasar Sin,ya bayyana cewa, bisa alkaluman da hukumar harajin ta fitar, ana iya ganin cewa, ana kara habaka sabon karfin samar da kayayyaki da hidimomi...
    Kasar Iran ta yi Allah wadai da harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan yankin kudancin kasar Lebanon Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai da hare-haren da yahudawan sahayoniyya suka kai a wurare da dama a kudancin kasar Lebanon. Ya jaddada cewa, sun biyo bayan yadda aka ci gaba da yin sassauci da rashin daukar nauyin masu daukar nauyin yarjejeniyar tsagaita bude wuta – Faransa da Amurka – yana mai nuni da alhakin kai tsaye da ke kan kasashen biyu a wannan fanni. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Baqa’i ya dauki hare-haren da yahudawan sahayoniyya suka kai a jiya da rana da kuma dare kan wasu wurare a kudancin...
    Kungiyar Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani da su matsa wa haramtacciyar kasar Isra’ila lamba kan aiwatar da sharuddan yarjejeniyar Gaza Kungiyar Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani da su ci gaba da taka rawa wajen bin diddigin aiwatar da sauran tanade-tanaden yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, musamman ma wadanda suka shafi shigar da adadin taimakon da ake bukata. A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta jaddada bukatar gaggauta fara kafa kwamitin tallafawa al’umma domin fara gudanar da ayyukansa na gudanar da harkokin yankin zirin Gaza. Kungiyar Hamas ta bayyana jin dadin ta ga kokarin da masu shiga tsakani a Masar, Qatar, da Turkiyya suka yi na cimma yarjejeniyar dakatar da yakin wuce...
    An tsara fara sauraron ƙarar a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2025, a gaban Mai Shari’a Yusuf Ubale. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja October 17, 2025 Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025 Manyan Labarai Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa October 16, 2025
    Rundunar ’yan sandan Jihar Oyo, ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Lawal Faruƙ da ake zargin ya bankawa tsohuwar masoyiyarsa wuta bayan da dangantakar su ta yi tsami. Majiyar PUNCH Metro ta samu labarin a ranar Alhamis cewa, lamarin ya faru ne a barikin sojoji da ke Ibadan babban birnin jihar. Jami’an tsaro sun kama ’yan bindiga 2, sun ƙone sansaninsu a Kogi Ba mu ji dadin yi wa mahaifinmu afuwa tare da riƙaƙƙun masu laifi ba – Iyalan Herbert Macaulay Wani ƙwararre a fagen yaƙi da ’yan tada ƙayar baya, Zagazola Makama wanda ya bayyana yadda lamarin ya faru a shafinsa na sada zumunta na X, ya bayyana cewa, wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa shi...
    An fara gina magudanan ruwa domin dakile afkuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomin Malam Madori da Kaugama dake jihar Jigawa. Tawagar Injiniyoyin jihar karkashin jagorancin Daraktan kula da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa, Injiniya Mukhtar Muhammad Usman sun ziyarci kananan hukumomin domin duba yadda aikin ke gudana. Haka zalika Daraktan da mataimakin sa Injiniya Mahdi Isyaku da sauran ma’aikata ssn ziyarci wurin da ambaliyar ruwa tayi ta’adi a garin malam Madori. A lokacin da tawagar ta fara auna fili da tona magudanun ruwan, daraktan ya ce an fara aikin tona magudanar ruwa mai tsawon kilomita 2 a matsayin wani ɓangare na aikin karkatar da ruwan da ya lalata wurare zuwa sabon wurin da aka tsara. Yana mai cewar,...
    A yammacin jiya Alhamis ne sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow inda ya isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ga shugaban na Rasha. Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka hada da huldar dake tsakanin kasashen biyu, da hadin gwiwar tattalin arziki, da ci gaban yankin, da kuma sauran batutuwa na kasa da kasa. A makon da ya gabata, Putin ya ce mahukuntan Isra’ila sun bukaci ya isar da sako ga Iran cewa ba su niyar sake kaddamar da wani hari a kan kasar ta Iran. “Muna ci gaba da samun sakonni daga jagorancin Isra’ila suna neman...
      Kafin cimma nasarar hakan, an kwashe sama da shekaru biyu ana gwabza fada da mamaya a Gaza, lamarin da ya haddasa asarar rayuka sama da 67,000, da barnata dukiyoyin da aka kiyasta darajarsu kan kusan dalar Amurka biliyan 70, kana an lalata kusan kaso 90 bisa dari na daukacin gine-ginen dake Gaza, baya ga al’ummun zirin sama da miliyan guda da suka rasa matsugunansu.   Ko shakka babu wannan yanayi ya haifar da wani rauni da zai jima ba a manta da radadinsa a tarihin bil’adama ba. Falasdinawa da bangaren al’ummun Israila sun tafka asarar rayuka, da dukiyoyi, da kudaden kashewa a ayyukan soji, da tabarbarewar alakar sassan kasa da kasa, da ganin baiken yaki daga sassa daban daban....
      An dage ci gaba da binciken har sai ranar 20 ga wata. Maris na shekara mai zuwa, a makon da ya gabata, dubban mutane ne suka yi jerin gwano a kan titunan birnin Manchester domin gudanar da jana’izar Hatton, wanda ya kasance shahararren dan wasan dambe a kasar Ingila.   Dan wasan gaban Oasis Liam Gallagher, tsohon dan wasan Ingila da Manchester United Wayne Rooney da kuma tsohon zakaran ajin masu nauyi na duniya Tyson Fury na daga cikin taurarin duniya na wasanni da suka halarci jana’izar Hatton. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc  October 15, 2025 Wasanni Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo October 14,...