Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?
Published: 27th, October 2025 GMT
Sa’an nan matakin da kasar Sin ke dauka yanzu, shi ne jagorantar manyan gyare-gyare kan tsare-tsaren samar da kayayyaki na duniya, ta yadda ita da dukkan kasashe masu tasowa za su samu damar inganta tsare-tsarensu na tattalin arziki, musamman ma a bangaren masana’antu. Dangane da batun, babbar darektar hukumar kasuwanci ta duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana a wajen taron dandalin tattaunawa na Abuja karo na 6, da ya gudana a kwanakin baya, cewa “Sauyawar tsare-tsaren samar da kayayyaki na duniya ta haifar da damammaki ga kasashen Afirka, ta fuskar janyo jari, da karfafa bangaren masana’antu.
Hakika, ma iya cewa maganar Madam Ngozi ta riga ta zama gaskiya, ta yin la’akari da yadda kasar Sin take zuba jari da raya masana’antu a kasashen Afirka daban daban. Sai dai ci gaban masana’antun kasashen Afirka da Sin suna haifar da sauyawar yanayi kan tsohon tsarin tattalin arzikin duniya. Hakan ya sa kafofin yada labarai na kasashen yamma suka dinga yada jita-jita game da kasar Sin, da hadin gwiwarta da kasashen Afirka. To, abun da ya kamata kasashen Afirka da kasar Sin su yi, shi ne rufe kunnuwansu, da kokarin neman ci gaban tattalin arziki, da gina wata duniya mai adalci da samun daidaito. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: da kasar Sin
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumomin Ilimi a Jihar Jigawa Sun Kare Kasafin Kudinsu a Gaban Majalisa
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar bunkasa ilimin manya ta jihar Jigawa tace za ta kashe naira milyan 400 wajen gudanar da harkokin ta a sabuwar shekara ta 2026.
Shugaban hukumar. Dr. Abbas Abubakar Abbas, ya bayyana haka lokacin kare kiyasin kasafin kudin hukumar a gaban kwamatin ilimi matakin farko na majalisar dokokin jihar Jigawa.
Dr Abbas Abubakar Abbas ya ce hukumar za ta yi amfani da kudaden wajen inganta shirye shiryen koyon karatu da rubutu ga manya maza da mata da na ci gaba da karatu don kammala karatun sakandare da na masu son sake jarrabawar sakandire da koyon karatu ta Rediyo da cibiyoyi daban daban da ke fadin jihar.
Shi ma da ya ke kare kiyasin kasafin kudin hukumarsa , shugaban hukumar makarantun Tsangaya, Dr. Hamisu Maje, ya ce sun yi kiyasin naira milyan dubu 3 da milyan 500 tare da kudurin kammala aikin ginin makarantun Tsangaya guda 3 da ke Ringim da Kafin Hausa da Dutse.
Ya ce an yi tanadi domin kafa cibiyar koyar da sana’oi da gidajen alarammomi da masallaci tare da samar da ruwan sha da wutar lantarki a kowacce makaranta.
Dr. Hamisu Maje ya kuma bayyana cewar hukumar za ta gyara makarantun Tsangaya guda 7 da aka gada daga gwamnatin tarayya da ke sashen jihar domin karfafa tsarin ilimin makarantun Tsangaya na zamani.
A daya bangaren kuma, kwalejin fasaha ta jihar da ke Dutse da Kuma hukumar bada tallafin karatu ta jihar sun kare kiyasin kasafin kudadensu a gaban kwamatin kula da manyan makarantu na majalisar dokokin jihar Jigawa.
Da ya ke kare kiyasin kasafin kudin, shugaban kwalejin fasaha ta jihar da ke Dutse, Dr. Ahmad Badayi, ya ce sun yi kiyasin fiye da naira milyan 700 wadda daga ciki an kebe naira milyan 330 domin sayo kayayyakin aiki a dakin gwaje-gwaje da koyon aikin hannu da gyaran ofisoshi, yayin da za a yi amfani da ragowar kudaden wajen kammala manyan ayyuka.
Shi ma da ya ke kare kiyasin kasafin kudin hukumar sa, shugaban hukumar bada tallafin karatu ta jihar Malam Sa’idu Magaji, ya ce sun yi kiyasin kashe naira milyan dubu 10 domin bada tallafin karatu na cikin gida da na kasashen waje.
A nasa jawabin, shugaban kwamatin kula da ilimin manyan makarantu na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Sule Tankarkar Alhaji Muhammad Abubakar Sa’id, ya jaddada bukatar ganin masu ruwa da tsaki a bangaren manyan makarantu sun yi dukkan mai yiwuwa domin inganta harkokin ilimi mai zurfi a sabuwar shekara.