Wilayati: Kasashen Ian, China Da Rasha Suna Taka Rawa A Fagen Kafa Sabon Tsarin Duniya
Published: 28th, October 2025 GMT
Mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara akan harkokin siyasar kasa da kasa Dr. Ali Akbar Wilayati ya ce; Da akwai kasashe uku a cikin Asiya wadanda suke da ‘yanci da su ne Iran, China da Rasha, kuma suna taka rawa domin samar da sabon tsarin tafiyar da duniya.
Dr. Wilayati ya bayyana hakan ne dai a yayin ganawarsa da jakadan China a Iran “Zong Bi Wuu” yana mai kara da cewa; Alaka a tsakanin kasashen biyu ta dade da kuma zurfi.
Har ila yau Wilayati ya ce alakar kasashen biyu ta ginu ne akan maslaha da kuma girmama juna da kuma cin gashin kai na siyasa, da hakan ya mayar da su, tare da kasar Rasha zama kasashen Asiya uku masu ‘yanci.
Haka nan kuma Wilayati yay aba wa matsayar da kasar China take dauka akan Iran,musamman dangane da batun takunkumin wanda ya ce, yana nuni da yadda Beijing take taka rawa a fagen siyasar duniya.
A nashi gefen, jakadan kasar ta China a Iran Zong Bi Wuu ya bayyan jin dadinsa akan ganawarsa da Ali Akbar Wilayati, tare da kuma bayyana yadda alaka tare a tsakanin kasarsa da Iran a lokaci mai tsawo.
Haka nan kuma ya ce, kasarsa China tana bayar da muhimmanci ga alakarta da Iran , haka nan kuma ya yi godiya jagoran juyin musulunci da yake bai wa alaka da China muhimmanci.
Bangarorin biyu sun kuma tattaunawa abubuwan da suke faruwa a fagen siyasar kasa da kasa da kuma a cikin wannan yankin na yammacin Asiya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Zaben Ivory Coast: Alassane Ouattara na kan gaba da tazara mai yawa October 27, 2025 Pezeshkian: Hadin kan Musulmi zai iya dakile zalincin kasashen waje October 27, 2025 Amurka ta tsare wani dan jarida musulmi saboda sukar Isra’ila October 27, 2025 Kashi 84% na ‘yan Faransa ba su gamsu da Macron ba a matsayin Shugaba October 27, 2025 Iran ta bukaci MDD ta nisanci nuna bangaranci game da masu keta dokokin duniya October 27, 2025 Kamaru : Paul Biya, ya lashe zaben shugaban kasar a karo na takwas October 27, 2025 An Nada Birgediya Janar Qarshi A Matsayin Mataimakin Babban Kwamandan Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci October 27, 2025 Hamas Ta Ce: Kungiyar Ta Ba Da ‘Yanci Ga Masu Shiga Tsakani Zabar Membobin Kwamitin Gudanar Da Gaza October 27, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe ‘Yan kasar Lebanon Biyu Tare Da Jikkatan Wasu Biyu Na Daban October 27, 2025 Amnesty International Ta Bukaci Bayyana Makomar Masu Fafutukar Kare Hakkin Bil’Adama Da Suka Bace A Uganda October 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Wilayati ya
এছাড়াও পড়ুন:
Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?
Sa’an nan matakin da kasar Sin ke dauka yanzu, shi ne jagorantar manyan gyare-gyare kan tsare-tsaren samar da kayayyaki na duniya, ta yadda ita da dukkan kasashe masu tasowa za su samu damar inganta tsare-tsarensu na tattalin arziki, musamman ma a bangaren masana’antu. Dangane da batun, babbar darektar hukumar kasuwanci ta duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana a wajen taron dandalin tattaunawa na Abuja karo na 6, da ya gudana a kwanakin baya, cewa “Sauyawar tsare-tsaren samar da kayayyaki na duniya ta haifar da damammaki ga kasashen Afirka, ta fuskar janyo jari, da karfafa bangaren masana’antu.” Ban da haka, ta ce, “Huldar abota tsakanin Afirka da Sin wani misali ne na samun ci gaban da zai amfani kowa ta hanyar hadin gwiwa, ga kasashe masu tasowa”, kana “ Kasar Sin ta iya jagorantar hadin gwiwar, ta hanyar zuba jari ga kasashen Afirka, da taimakonsu wajen raya tattalin arziki.”
Hakika, ma iya cewa maganar Madam Ngozi ta riga ta zama gaskiya, ta yin la’akari da yadda kasar Sin take zuba jari da raya masana’antu a kasashen Afirka daban daban. Sai dai ci gaban masana’antun kasashen Afirka da Sin suna haifar da sauyawar yanayi kan tsohon tsarin tattalin arzikin duniya. Hakan ya sa kafofin yada labarai na kasashen yamma suka dinga yada jita-jita game da kasar Sin, da hadin gwiwarta da kasashen Afirka. To, abun da ya kamata kasashen Afirka da kasar Sin su yi, shi ne rufe kunnuwansu, da kokarin neman ci gaban tattalin arziki, da gina wata duniya mai adalci da samun daidaito. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA