2025-10-30@21:07:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 448
«kofin Nahiyyar Afirka na 2026»:
Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya
A baya-bayan nan Robert Tarjan, Ba’amurke masanin kimiyyar na’ura mai kwakwalwa, wanda ya taba lashe lambar yabo ta “Turing”, ya ce Sin ta kafa tsarin bunkasa ilimin kimiyya a matakin farko, a matsayin dabara ta tsawon lokaci da kasar ke baiwa fifiko, kuma hakan abu ne mai matukar ban sha’awa. Kazalika, a halin yanzu, Sin...
Shugaban riƙon ƙwarya na jam’iyyar ADC, David Mark, ya ce Arewacin Najeriya na cikin mawuyacin hali, kuma jam’iyyarsu ce kaɗai za ta iya warware waɗannan matsaloli idan aka zaɓe ta. Ya bayyana hakan ne a taron jam’iyyar ADC da aka yi a Abuja Continental Hotel, inda mambobi da magoya bayan jam’iyyar daga sassa daban-daban suka...
Wasu yan bindiga wadanda ake dangantasu da kungiyar Jaishul-Zulum sun dauki alhakin kai hare-hare a cikin wata kotu a birnin Zahidan babban birnin lardin Sistab Baluchistan a yau Asabar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa yan ta’addan sun shigo da motarsu har zuwa a wata kotu a garin da Zahidan, sannan...
Mai magana da yawun jam’iyyar na wucin gadi ya ki janye ikirarinsa na cewa ADC na fuskantar manyan matsaloli a bangaren shari’a. “Muna da tabbaci kan doka a kowane mataki da muka dauka. Mun tabbatar mun rufe duk wata baraka da jam’iyya mai mulki za ta iya amfani da ita a kanmu,” ya kara da...
Kwanan nan jam’iyyar PDP ta gudanar da taron kwamitin zartarwa karo na 100 da aka gudanar ranar 30 ga Yuni, PDP ta warware rikicin da ya dade yana ci mata tuwo a kwarya na batun mukamin sakataren jam’iyyar na kasa wanda ta tabbatar da Sanata Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar. Duk da wannan warware...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alhinin rasuwar Sarkin Gusau, Dokta Ibrahim Bello na Jihar Zamfara. Sarkin ya rasu da safiyar Juma’a yana da shekaru 71. An yanke wa mutum 3 hukuncin kisa kan kisan kai a Gombe HOTUNA: Yadda Kwankwaso ya karɓi ’yan APC zuwa NNPP a Kano Mai bai wa Shugaban Ƙasa...
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023, ya karɓi ’yan APC zuwa jam’iyyar NNPP a Jihar Kano. Kwankwaso, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a ta shafinsa na X, inda ya ce waɗanda suka sauya sheƙar ’yan jam’iyyar APC ne. An kai hari a ƙauyuka uku da kashe mutum 7...
“Rasuwar Sarkin Zamfara babban rashi ne ga al’ummar jihar Zamfara, Arewa da ma ƙasar nan baki ɗaya. “Sarkin ya sadaukar da rayuwar sa a shekarun nan 10 da ya ya yi hana mulki a matsayin Sarkin Gusau na 15, wanda ya hau a ranar 16 ga watan Maris na shekarar 2015. Ya yi mulki cikin...
An sami hatsarin tashin gobara a cikin wani rumbun ajiyar makamai a garin Mu’arrah dake gundumar Idlib ta Arewa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar mutane da dama. Majiyar lafiya ta kiwon kasar Syria ta bayyana cewa; Mutane 2 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 70 su ka jikkata sanadiyyar fashewar rumbun makamai a...
Kwamitin zartaswa na Jam’iyyar APC na ƙasa ya naɗa Ministan Jin-ƙai da Yaƙi da Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda, a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa. Nan take aka rantsar da Nentawe Yilwatda a wajen taron. Kwalara: Mutum 13 sun mutu sama da 236 na jinya a Neja Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50...
An cimma matsaya kan zaɓensa bayan wata ganawa da aka yi a Abuja tsakanin Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin APC. Ana sa ran manyan shugabannin jam’iyyar za su tabbatar da naɗinsa a yau Alhamis. Farfesa Yilwatda, ya fito ne daga Jihar Filato da ke yankin Arewa ta Tsakiya, yankin da suke da alhakin riƙe kujerar...
Matukar ba a sami sauyin tsare-tsare ba, akwai yiwuwar Ministan Jinkai da Yaki da Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa a yau Alhamis. Majiyoyi da dama a daren jiya sun shaida wa Aminiya cewa Nentawe ne ke kan gaba a cikin mutanen da ake so su dare shugabancin jam’iyyar...
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC kuma Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, ya bayyana cewa Gwamnonin APC sun gudanar da wata muhimmiyar ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar gwamnati da ke Abuja. Da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa bayan kammala taron, Gwamna Uzodimma ya bayyana ganawar da cewa...
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da hukumomin gwamnati wajen danne ’yan adawa. Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da manema labarai a Kano. Uwa ta kashe ’ya’yan cikinta biyu saboda kuncin rayuwa An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano Lamido, ya ce...
Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu ta karɓo bashin ƙasashen waje da ya haura dala biliyan 21 domin aiwatarwa da cike giɓin kasafin kuɗin shekarar 2025 zuwa 2026. Majalisar ta bayyana cewa za a yi amfani da bashin ne wajen aiwatar da muhimman ayyukan ci gaban ƙasa, musamman a fannonin ababen more...
Ya ce ya zagaya dukkanin ƙananan hukumomin Jihar Bauchi domin goyon bayan Gwamna Bala yayin yaƙin neman zaɓe, duk da cewa yana ci gaba da aiki a matsayin Sakataren Gwamnatin Jiha. A watan Janairu 2025, Kashim ya yi murabus daga matsayin SSG, inda ya ce gwamnan ne ya umarce shi da yin hakan. Rahotanni na...
Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta zabi Hon. Kamilu Sa’idu (Wamban Kasuwar Daji) a matsayin dan takararta na Majalisar Dokokin Jihar Kaura Namoda ta Kudu da za a yi ranar 16 ga Agusta, 2025. A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya ce Kamilu...
Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Nijeriya, Femi Gbajabiamila ya ce haɗakar ’yan siyasa a jam’iyyar ADC alheri ce ga siyasar Nijeriya. Ya bayyana cewar haɗaka ’yan adawar za ta taimaka wajen hana ƙasar faɗawa cikin siyasar jam’iyyar ƙwaya ɗaya tal. WFP ya dakatar da tallafin abinci a Yammaci da Tsakiyar Afirka Za a sa zare tsakanin...
A bisa umarnin sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ, an yi nasarar gudanar da zaben majalisar jihar Zamfara a ranar Asabar din da ta gabata cikin kwanciyar hankali da lumana, inda aka dawo da dukkan mukamai ba tare da hamayya ba. Mukamin daya tilo da aka fara takaddama a kai ya sa daya...
Sanata Ireti Kingibe, wacce ke wakiltar Babban Birnin Tarayya, ta fice daga jam’iyyar LP zuwa ADC. Da ta ke magana da ’yan jarida a Abuja, ta ce wannan matakin nata wani shiri ne na tunkarar babban zaɓen 2027. Abin da ya faru tsakani na da DSS bayan kama ni — Ɗan Bello DSS ta saki...
Sanata Ireti Kingibe, wacce ke wakiltar Babban Birnin Tarayya, ta fice daga jam’iyyar LP zuwa ADC. Da ta ke magana da ’yan jarida a Abuja, ta ce wannan matakin nata wani shiri ne na tunkarar babban zaɓen 2027. Abin da ya faru tsakani na da DSS bayan kama ni — Ɗan Bello DSS ta saki...
Wata majiya ta tabbatar da cewa, a yayin da tsohon shugaban majalisar dattawan ya je Jihar Binuwai domin daurin auren jikarsa, “watakila zai yi ganawa da shugabanni da masu goyon bayan tafiyar a shiyyar.” Aregbesola ya samu tarba daga magoya bayansa a lokacin da ya isa Jihar Legas jim kadan bayan kaddamar da jam’iyyar a...
Rahotanin sun bayyana cewa Shettima ya ziyarci Kano ne don yin ta’aziyyar rasuwar hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu kwanan nan, da kuma jajanta wa mutanen Kano kan wannan rashi. Haka kuma rahotannin sun bayyana cewa a irin wadannan manyan taruka a Nijeriya, an saba ganin shugabannin jam’iyya da goyon baya su...
Sojojin Sahayoniya suna ci gaba da yi wa mutane Gaza kisan kiyashi a kwana na 643 a jere. Sojojin sahayoniyar suna amfani da dukkanin kayan yaki da su ka hada jiragen masa masu matuki da marasa matuki, da kuma manyan bindigogi. Tun da safiyar yau Alhamis ne dai sojojin HKI su ka fara kai hare-hare...
Tsohon jigo a Jam’iyyar LP, Kenneth Okonkwo, ya ce dole ADC ta tsayar da ɗan Arewa takara idan tana son ta kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027. A cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Okonkwo, ya ce idan ADC ta tsayar da ɗan Kudu takara, Tinubu...
Jam’iyyar ADC ta musanta labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa wasu shugabanni daga yankin Kudu sun buƙaci Atiku Abubakar, da ka da ya fito takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027. A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ta ce wannan labari ƙarya ne, wanda aka ƙirƙira don haddasa rikici...
Matar tsohon Gwamnan jihar Adamawa, Zainab Boni Haruna, ta fice daga tsohuwar jam’iyyarta ta PDP zuwa jam’iyyar hadakar ’yan adawa ta ADC. Zainab, wacce asalinta ta fito ne daga karamar hukumar Nangere a Jihar Yobe ta bayyana haka ne a wani taro da mata magoya bayan jam’iyyar ta ADC da aka gudanar a Damaturu, babban...
An kaddamar da jam’iyyar African Democratic Party, ADC a Gombe mako guda bayan wasu jiga-jigan ‘yan adawa sun hada kai cikin jam’iyyar. Shugaban jam’iyyar ADC a jihar Gombe kuma tsohon ministan sufuri Alh. Idris Abdullahi, ya ce makasudin shiga jam’iyyar shi ne ceto kasar nan daga kangin tattalin arziki da dora ta kan turbar...
Aminu Dahiru Ahmad, hadimin tsohon shugaban jam’iyar APC na kasa, Abudllahi Umar Ganduje, ya ce jam’iyyar za ta gane ta yi kuskure kan saukarsa daga shugabancin. A wata doguwar wasika da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana takaicinsa kan rashin nuna wa Ganduje halasci, duk da irin ci gaban da ya kawo jam’iyar...
Tsohon Ministan Sufuri, Idris Umar, ya bayyana cewa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ce za ta ceto Najeriya daga halin da take ciki, tare da mayar da APC jam’iyyar adawa a Zaɓen 2027. Yayin wani taron haɗin gwiwar jam’iyyu na adawa a Gombe, an amince da amfani da ADC a matsayin dandalin siyasa na bai...
Jam’iyyar ADC ta zargin Fadar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinuba da shirya mana wata kutungwila mai hadarin gaske domin kawo cikas ga hadakar ’yan adawan da ke kara samun farin jini. Sakataren Yada Labarai na ADC na Kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya ce a sakamakon haka gwamnatin APC a matakin kasa ta kira wani taron...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wannan lamari ya buɗe sabon shafi a siyasar ƙasar nan, inda ƴan adawa suke ci gaba da cewa zuwan sabuwar jam’iyyar wani sauyi ne da za a samu a cikin ƙasar. Wani mai sharhi a kan siyasa, Sani Kabo, ya bayyana abin da ya samu shafin yanar gizon jam’iyyar a matsayin wata ƴar manuniya ga...
Elon Musk, wanda ya taɓa zama mashawarcin Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa mai suna America Party. Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (Twitter), makonni bayan wata taƙaddama da ta ɓarke tsakaninsa da Shugaban Amurka. Tinubu ya umarci sojoji su murƙushe ’yan ta’adda a faɗin Najeriya Mutum 21...
Ɗaya daga cikin hadiman gwamnan jihar Yobe, Hon. Babagana Yakubu Mohammed, ya ajiye muƙaminsa na mai taimakawa gwamna na musamman ya kuma fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC. Babagana, ya sanar da ajiye aikin nasa ne cikin wata wasiƙa da ya aikewa Sakataren Gwamnatin Jihar, Baba Malam Wali. Ba Ni Da Niyyar Barin APC...
Zalum ya kuma shawarci gidajen jaridu da su dinga tantance labarai kafin su yaɗa shi domin kaucewa labaran ƙanzon kuregen da wasu suke yaɗawa. A ƙarshe gwamnan ya ce ya duƙufa wajen hidimtawa al’ummar jihar Borno a ƙarƙashin jam’iyar mai albarka ta APC . Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa zai bar jam’iyyar APC zuwa ADC tare da wasu gwamnoni biyar. A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dauda Iliya, ya fitar, Zulum ya ce wannan labari ƙarya ne, kuma wasu ne kawai ke ƙirƙirarsa domin cimma...
Iran ta Bukaci Gudanar da Bincike Kan Sacewar jami’ar Diblomasiyyar kasar A Lebanon Shekaru 43 Da Suka gabata
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da ci gaba da riki jami’an diblomasiyyar kasar 4 wanda HKI take yi tun shekaru 43 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar tana fadar haka a wata sanarwa da ta fitar shekaru 43 cur da sacewar wadanda...
Ibrahim ya bayyana cewa, sun rarraba mukamai na rikon jam’iyyar a tsakaninsu, kafin babban taro na kasa a nan gaba. Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya tabbatar cewa; hadakar ta ADC, ta zabi Aregbesola a matsayin sakatarenta na kasa na riko, har ma ya wallafa a jawabin karbar mukamin da ya yi a shafukan sada...
Rahotanni daga kudanci Lebanon sun ce, sau uku jiragen yakin HKI su ka kai hare-hare a kan gidajen mutane da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya da kuma jikkatar wasu da dama. A garin Shaqra’dake yankin Bint-jubail, jiragen sama marasa matuki sun kai hare-hare da ya yi sanadiyyar jikkatar mutane biyu da raunuka, kamar...
Dakarun kare juyin musulunci na Iran sun fitar da bayani a lokacin tunawa da sace jami;an diplomasiyyar Iran 4 a birnin Beirut, wanda ya kunshi cewa: Ya zama wajibi ‘yan sahayoniya su kwana da sanin cewa; Duk laifukan da su ka aikata a baya za a yi musu sakamako a kansa,kuma duk wani sabon wuce...
Jam’iyyar NNPP, ta bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya yi mata takarar shugaban ƙasa a 2023, ba zai tsaya takara a 2027 ba. Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dokta Agbo Major, ne ya bayyana haka a wata sanarwa, inda ya mayar da martani kan wata magana da Buba Galadima ya yi. Tinubu ko ɗansa...
Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya ce duk wani yunƙuri da Shugaba Bola Tinubu, zai yi ba zai hana jam’iyyar APC faɗuwa a zaɓen 2027 ba. Yayin wata hira da aka yi da shi a Jos, a Jihar Filato, Dalung, ya ce ko da Tinubu zai naɗa ɗansa Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC), ko...
Salim Sani Shehu Jam’iyyar NNPP ta bayyana a hukumance cewa tsohon ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba zai sake yin takarar shugaban ƙasa karkashin jam’iyyar a zaɓen 2027 ba. Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Agbo Major, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin da yake mayar da martani...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yan Najeriya da dama na ta bayyana mabanbantan ra’ayoyi kan sabon hadakar ‘yan siyasa zuwa sabuwar jami’yyar ADC. A yayin da wasu ke ganin wannan hadaka za ta cire musu kitse daga wuta, wasu kuwa gani suke yi duk kanwar ja ce. A ranar laraban nan ne dai gaggan ‘yan siyasa daga jamiyyu daban...
Daga safiyar yau juma’a, Falasdinawa 17 sun yi shahada sanadiyyar hare-haren da HKI ta kai wa Falasdinawa ‘yan hijira a yankin Mawasi dake Kudancin Khan-Yunus. Tun da safiyar yau ne dai jiragen yakin HKI su ka kai hare-hare a gabashin birnin Gaza, haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun yi amfani da jirgin sama maras matuki...
Dele Momodu, sanannen ɗan jarida kuma jigo a jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa yawancin magoya bayan jam’iyyar sun fara ficewa daga cikinta, suna barin tsarin jam’iyyar a hannun ministan babban birnin tarayya. Dele ya bayyana hakan ne yayin wani shiri a Channels TV, inda ya nuna cikakken goyon bayansa ga sabon ƙawancen jam’iyyun adawa da...
A ci gaba da sauya sheƙar da ’yan Majalisar Wakilai na Tarayya ke yi a ranar Alhamis wasu mambobi bakwai daga Jihar Akwa Ibom sun sanar da sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC mai mulki. Cikin waɗanda suka sauya sheƙa sun haɗa da shida daga Jam’iyyar PDP da kuma ɗaya daga Jam’iyyar YPP. ’Yan Najeriya sun...
Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce wahalhalu sun yi yawa a Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wanda har ya sa mutane suka fara fatan dawowar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari. Yayin da yake magana a birnin Abuja, Amaechi ya ce Najeriya ta taɓarɓare matuƙa, inda ya ce sauyin gwamnati ne kawai zai magance matsaloli. Gwamnatin Yobe...