Gwamnati ta bai wa ASUU N2.3bn domin biyan bashin albashin malamai
Published: 29th, October 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta fitar da naira biliyan biyu da miliyan ɗari uku har da ɗoriya domin biyan bashin albashi da na ƙarin girma ga malamai a jami’o’in tarayya.
Wannan dai wani yunƙuri na ƙara ƙarfafa jin daɗin ma’aikata da kuma ci gaba da tattaunawa da ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU.
Sassauci na yi wa Maryam Sanda ba afuwa ba — Tinubu Super Falcons ta samu gurbin buga Kofin AfrikaMinistan Ilimi, Maruf Olatunji Alausa, ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin da yake jawabi kan tattaunawar da gwamnati ke yi da ƙungiyar ASUU da sauran ƙungiyoyin jami’o’i.
Ya ce an riga an tura kuɗin ta ofishin Akanta-Janar na Ƙasa (OAGF), kuma jami’o’in da abin ya shafa za su fara ganin saƙon biyan kuɗin a asusun su nan ba da daɗewa ba.
Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnati na shirin kammala sakin kuɗaɗen da suka shafi fansho da sauran tsarabe-tsarabe na basussuka, sannan daga shekarar 2026, ƙarin kuɗin alawus na aikin koyarwa (Earned Academic Allowance – EAA) za a haɗa shi kai tsaye cikin albashin ma’aikata domin tabbatar da biyan kuɗaɗen yadda ya kamata.
Alausa ya tabbatar da cewa gwamnati ta ƙuduri aniyar warware duk matsalolin da suka jima suna taƙaddama da ɓangaren ilimi, yana mai cewa duk tattaunawar da ake yi tana gudana ne cikin gaskiya da amincewa.
Sai dai ya jaddada cewa gwamnati za ta shiga yarjejeniyar da za ta iya ɗauka ne kawai la’akari da abin da tattalin arzikin ƙasa ya bayar da dama.
Ya ce kwamitin ƙarƙashin jagorancin Yayale Ahmed na ci gaba da zama tamkar wani tsani na haɗin kai tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin jami’o’i.
Ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu wajen ganin an farfaɗo da harkokin ilimi a ƙasar nan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya
এছাড়াও পড়ুন:
Iyaye Sun Yi Fitowar Farin Dango Don Yi Wa “Yayansu Allurar Rigakafi a Sule-Tankarkar
Daga Usman Muhammad Zaria
Aikin rigakafin watan Disamba a karamar hukumar Sule-Tankarkar ta jihar Jigawa ya samu gagarumar nasara, yayin da iyaye suka fito kwansu da kwarkwata domin tabbatar da cewa an yi wa ’ya’yansu cikakken rigakafi.
Wasu daga cikin iyayen da suka kawo ’ya’yansu domin karbar rigakafin yau da kullum da na shan inna sun bayyana jin dadinsu kan yadda aka gudanar da aikin cikin kwanciyar hankali.
Daya daga cikinsu, Malama Ummahani Danbala, ta ce an wayar da kan jama’a sosai ta hannun mata ’yan sa-kai a unguwarsu, inda aka karfafa gwiwar iyaye mata su kawo ’ya’yansu domin karbar rigakafin yau da kullum da na shan inna.
Malam Yunusa, wani mai sa ido a karamar hukumar, ya bayyana gamsuwarsa da yadda aka gudanar da aikin rigakafin a yankin.
A cewarsa, aikin wayar da kan jama’a ya yi matukar tasiri, domin mutane na kawo ’ya’yansu da kansu ba tare da kin amincewa da rigakafin ba.
Yunusa ya bayyana cewa duk da kasancewar karamar hukumar tana kan iyaka, aikin ya gudana cikin nasara, sakamakon hadin gwiwar da aka samu daga dukkan masu ruwa da tsaki.
Ya kara da cewa ana sa ran rigakafin yara kusan 45,221, inda aka yi niyyar kai rigakafin makarantu da wuraren ibada domin gano yaran da ba a musu ba.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa karamar hukumar na da cibiyoyin lafiya guda 28, kuma aikin rigakafin ya gudana cikin kwanciyar hankali a al’ummomin Ablasu, Kings, Amanda, Togai, Nagwamatse da Hannun Giwa.
Ana sa ran kammala zagayen rigakafin shan inna na watan Disamba a ranar Juma’a a fadin kananan hukumomi 27 na jihar Jigawa.