Aminiya:
2025-12-13@20:31:42 GMT

Tinubu ya janye afuwar da ya yi wa Maryam Sanda da masu manyan laifuka

Published: 29th, October 2025 GMT

Shugaba Bola Tinubu, ya janye afuwar da ya yi wa Maryam Sanda da masu laifukan da suka haɗa da kisan kai, safarar miyagun ƙwayoyi da sauransu.

Maryam Sanda, wadda aka yanke wa hukuncin kisa saboda zargin kashe mijinta, ba ta cikin sabon jerin sunayen wadanda aka yafe wa laifi. Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya tabbatar a ranar Laraba cewa an cire sunayen mutane kimanin 50 daga tsohon jerin bayan ce-ce-ku-ce daga jama’a.

“Bayan duba martanin jama’a, Shugaba Tinubu ya umarci a cire sunayen wadanda aka samu da manyan laifuka kamar garkuwa da mutane, safarar miyagun kwayoyi, da fataucin mutane daga jerin wadanda aka bai wa afuwa,” in ji Onanuga.

Ya kara da cewa an dauki wannan mataki ne “don mutunta ra’ayoyin jama’a, karfafa gwiwar jami’an tsaro, da tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa da al’umma baki daya.”

Tsohon jerin sunayen da aka fitar ya haifar da suka daga jam’iyyun adawa da kungiyoyin kare hakkin dan Adam, wadanda suka bayyana matakin a matsayin amfani da ikon shugaban kasa ta hanyar da bata dace ba, kuma barazana ga tsarin shari’a. Sun yi gargadin cewa sakin manyan laifuka zai iya karfafa aikata laifi da kuma rage amincewa da doka.

Fadar shugaban kasa ta ce sabon umarnin yana nufin tabbatar da gaskiya da amincewa a tsarin bayar da afuwa. Shugaba Tinubu ya kuma umarci a dora aikin bayar da afuwa a karkashin ma’aikatar shari’a, tare da shigar da hukumomin tsaro da na shari’a a cikin tsarin don kauce wa irin wannan ce-ce-ku-ce a gaba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Afuwa Maryam Sanda

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Ta Kara Samar da Shirye-shiryen Inganta Rayuwar Masu Buƙata ta Musamman

Daga Usman Muhammad Zaria

Hukumar kula da masu bukata ta musamman a jihar Jigawa za ta gudanar da aikin gyaran gidajen gajiyayyu na shiyyar Birnin Kudu da Gumel a sabuwar shekara.

Shugaban hukumar, Malam Sale Zakar Kafin Hausa, ya bayyana haka lokacin kare kiyasin kasafin kudin 2026 a gaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa.

Ya ce gidan gajiyayyu na shiyyar Birniwa yana cikin kyakkyawan yanayi da kulawa sosai ta fuskar abinci da sutura da kayan wanka da na wanki da sauran bukatun rayuwa, dan haka gwamnati ta kuduri niyyar gyara sauran gidajen gajiyayyun domin kyautata yanayinsu.

Malam Sale Zakar ya ce an Kara yawan mata masu juna biyu da masu shayarwa da ke amfana da Shirin kula da lafiyar iyali daga 20 zuwa 30 a mazabun jihar 287.

Ya kara da cewa za kuma a kara yawan masu amfana da tallafin masu bukata ta musamman daga 150 zuwa 200 a kowacce karamar hukuma, inda masu bukata ta musamman 540 ke samun tallafin naira 10, 000 a duk wata.

A nasa jawabin shugaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Birnin Kudu Alhaji Muhammad Kabiru Ibrahim ya bayyana gamsuwa da tanade tanaden da aka yiwa mata da yara da tsoffi da marasa galihu da mata masu juna biyu da masu shayarwa da nakasassu.

Ya kuma yi addua’ar Allah Ya sa kasafin kudin ya yi tasiri wajen inganta rayuwar masu karamin karfi da marasa galihu a sabuwar shekara.

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaba Tinubu Ya Karrama Shugaban NPA Da Lambar Yabo Ta Musamman
  • Dantsoho Ya Yaba Wa Ƙoƙarin Oyetola Na Dawo Da Nijeriya Tsarin Sufurin Jiragen Ruwa Na Duniya
  • Kotu ta sa ranar yanke hukunci a Shari’ar Abba Kyari da NDLEA
  • Kotu Ta Umarci EFCC Ta Biya Wani Ƴan Kasuwar Kano Miliyan 5, Ta Nemi Afuwar Su
  • Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Hukuncin Kisa Kan Maryam Sanda
  • Tinubu Ya Yaba Wa Jami’an Tsaro Kan Ceto Dalibai 100 Da Aka Sace A Neja
  • Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Ta Kara Samar da Shirye-shiryen Inganta Rayuwar Masu Buƙata ta Musamman
  • Yadda za ku cike neman aikin dan sandan Najeriya na 2025/2026
  • Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jigawa Ta Nemi Kotuna Su Daina Jan Kafa Wajen Aiwatar da Shari’a