Gwamnan Bauchi na neman ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi 29
Published: 30th, October 2025 GMT
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya rattaba hannu kan sabuwar dokar da ta ƙirƙiri ƙarin ƙananan hukumomi 29 a jihar.
Wata takarda da Aminiya ta samu ta nuna cewa Mukaddashin Mataimakin Magatakarda na Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Musa Yerima, ya tura wannan ƙuduri zuwa Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulki, yana neman amincewar Majalisar Tarayya domin tabbatar da dokar a cikin gyaran kundin tsarin mulki da ake yi.
A halin yanzu, Jihar Bauchi na da ƙananan hukumomi 20 da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya amince da su.
Da ƙarin waɗannan 29 da ake nema, jihar da ke da kimanin mutane miliyan 10 za ta samu jimillar ƙananan hukumomi 49 ke nan.
A cikin wasikar da Mataimakin Magatakarda ya aike wa Sanata Barau Jibrin, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Duba Kundin Tsarin Mulki, ya ce: “Ina farin cikin sanar da ku cewa Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta amince da dokar da za ta ba da damar ƙirƙirar ƙananan hukumomi 29 a Bauchi, 2025.”
“Waɗannan ƙananan hukumomi ba za su fara aiki ba sai Majalisar Tarayya ta amince da dokar da za ta tabbatar da sunayen su kamar yadda Sashe na 8(5) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya tanada.
“Na kwatanta wannan bugun da dokar da Majalisa ta amince da ita, kuma na tabbatar da cewa wannan kwafi daidai ne da dokar da aka amince da ita,” in j wasikar.
Sunayen sabbin ƙananan hukumomin da ake son kirkira sun haɗa da: Balma, Bauchi ta Gabas, Bauchi ta Yamma, Beshongo, Bula, Burra, Chinade, Dagauda/Jalam da Disina.
Sauran su ne: Dogon Jeji/Jurara, Dass ta Yamma, Gadau, Galambi, Ganjuwa ta Gabas, Girawa, Gololo, Gwana, Isawa, Jama’a, Kankara, Lame, Lere, Madara, Sade, Sakuwa, Saye, Udubo, Yankari da Zungur.
Hedikwatocinsu sun haɗa da: Nasaru, Cibiyar Mata, Miri, Beni, Bununu, Chinade, Dagauda, Disina, Dogon Jeji, Lukshi, Gadau, Kangere, Faggo, Gololo, Futuk, Isawa, Nabordo, Akuyam, Karkara, Lame, Lere, Madara, Sade, Sakuwa, Hardawa, Udubo, Yelwan Duguri da Liman Katagum.
Yerima ya ƙara da cewa: “Wannan dokar an tura ta zuwa Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwa na Duba Kundin Tsarin Mulki na Majalisar Tarayya domin ci gaba da matakan da suka dace.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kundin Tsarin Mulki Jihar Bauchi da dokar da
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dattawa za ta tantance sabbin hafsoshin tsaro ranar Laraba
Majalisar Dattawa za ta gudanar da zaman tantance manyan hafsoshin tsaron ƙasar a gobe Laraba waɗanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa kwanan nan.
Shugaba Tinubu ya aike da sunayen sabbin hafsoshin zuwa majalisar ne domin tantancewa da amincewa da su, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.
Rikicin adawa da cin zaben Shugaba Paul Biya ya bazu a Kamaru ’Yan bindiga sun sa harajin N15m kan al’ummar Mazabar Sanata TambuwalA wata wasiƙar fadar shugaban ƙasa da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta yayin zaman da aka gudanar a wannan Talatar, ya ce kwamitin da ke kula da harkokin tsaro zai zauna gobe domin tantance waɗanda aka naɗa.
A makon jiya ne Shugaba Tinubu ya aiwatar da sauye-sauye a bangaren tsaro, inda ya ɗaga likafar Laftanar Janar Oluyede Olupemi daga babban hafsan sojin ƙasa zuwa babban hafsan tsaron ƙasa, don maye gurbin Janar Christopher Musa da aka cire daga muƙaminsa.
Haka kuma, shugaban ƙasar ya naɗa sababbin hafsoshin sojin sama, ruwa da ƙasa, yayin da ya bar Manjo Janar E.A.P. Undiendeye a matsayinsa na babban hafsan sashen tattara bayanan sirri na sojin ƙasa.