Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC
Published: 29th, October 2025 GMT
Lauyan ICPC, Osuobeni Akponimisingha, ya gabatar da ƙarar neman a kwace kuɗin, yana sanar da kotun cewa, ICPC ta bi umarnin wucin gadi na kwace dalolin da ta yi a baya. Ya ce, an buga sanarwa ta jama’a inda aka gayyaci duk wani mutum wanda yake ganin akwai dalilin da zai hana ko kuma bai kamata a kwace kudin ba har abada, amma babu wanda ya amsa.
“Saboda haka, muna neman a ba da umarnin a kwace kudin har abada a mayar da su ga Gwamnatin Tarayya, saboda bin umarnin wucin gadi kuma babu wanda ya nuna adawa da hukuncin,” in ji Akponimisingha ga kotun.
Hukuncin ya biyo bayan umarnin wucin gadi da kotun ta bayar a ranar 30 ga Disamba, 2024, domin amsa bukatar da ICPC da Ma’aikatar tsaron farin kaya ta cikin gida (DSS) suka gabatar tare.
Takardar neman izinin, mai lamba FHC/ABJ/CS/1846/2024, kuma Usman Dauda, Daraktan Ayyukan Shari’a na DSS ya sanya wa hannu, ta nuna cewa an gano kudaden ne a lokacin bincike a gidan Dr. Ali da ke Kano.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Tsohon Jakadan Singapore A MDD Ya Jinjinawa Hangen Nesan Kasar Sin
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Samar Da Damammakin Raya Tattalin Arziki Ga Duniya A Shekara Mai Zuwa December 13, 2025
Daga Birnin Sin Sin Ta Gudanar Da Taron Tunawa Da Kisan Kiyashin Nanjing December 13, 2025
Daga Birnin Sin Kakakin Rasha: Kisan Kiyashin Nanjing Ya Nuna Zaluncin Ra’ayin Nuna Karfin Soja Na Japan December 12, 2025