Shafin Yanar Gizo Na ADC Ya Tsaya Cak Saboda Ɗumbin Magoya Baya Masu Son Yin Rijista
Published: 7th, July 2025 GMT
Wannan lamari ya buɗe sabon shafi a siyasar ƙasar nan, inda ƴan adawa suke ci gaba da cewa zuwan sabuwar jam’iyyar wani sauyi ne da za a samu a cikin ƙasar.
Wani mai sharhi a kan siyasa, Sani Kabo, ya bayyana abin da ya samu shafin yanar gizon jam’iyyar a matsayin wata ƴar manuniya ga irin buƙatar da ake da ita wajen sauya sheƙa da kuma haɗin kan ƴan adawa, inda ya misalta abin da yake faruwa da shekara ta 2013, lokacin da aka samar da jam’iyyar APC wadda ta kawo karshen mulkin jam’iyyar PDP a wancan lokaci.
Shima wani masanin siyasa a Nijeriya wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce wannan ya nuna yadda al’ummar ƙasar suke buƙatar canji.
Magoya bayan Alhaji Atiku Abubakar da Peter Obi suna ci gaba da nuna farin cikinsu da abin da ke faruwa a yanzu. Sai dai shugabannin haɗakar sun ce dole ne a ci gaba kula da lissafa abubuwan da ka iya faruwa a nan gaba kuma sai an yi haƙuri domin samun nasara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Zaɓe
এছাড়াও পড়ুন:
NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3
Hukumar da ke shirya gasar Firimiyar Nijeriya (NPFL) ta hukunta Kano Pillars FC da tarar Naira miliyan ₦9.5, tare da rage musu maki uku da ƙwallaye uku, bayan magoya bayansu sun kutsa cikin fili a yayin wasan da suka buga da Shooting Stars a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano. Hakan ya sa NPFL ta rufe filin wasan tare da umartar cewa Pillars za ta ci gaba da buga wasanninta na gida a filin Muhammad Dikko a Katsina.
A cewar NPFL, hukuncin ya fito ne bisa dokar C1.1, wadda ke hukunta hare-haren da ake kai wa tawagar baƙi da jami’an wasa. Hukumar ta ce wannan mataki yana nufin tabbatar da tsabtace filayen wasa daga tashin hankali da rashin ladabi daga magoya baya. “Za mu zartas da dokoki duk lokacin da irin wannan hali ya faru,” in ji Davidson Owumi, shugaban aiyuka na NPFL.
Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana Kano Pillars Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Gidan Rediyon RFI HausaAn ci tarar Pillars ₦1m saboda gazawa wajen samar da tsaro, da ₦1m saboda rashin shawo kan magoya baya, da ₦1m saboda jifa a cikin fili da abubuwa masu haɗari, da ₦2m saboda kai hari ga ƴan wasan Shooting Stars da jami’an wasa. Haka kuma, Pillars za ta biya ₦2m a matsayin diyya ga ƴan wasan Shooting Stars da ₦1.5m don jami’an wasa da suka ji rauni.
NPFL ta kuma nemi hukumar ƙwallon kafa ta Nijeriya (NFF) da ta sake duba cancantar wasu jami’an wasa daga wasannin Pillars da Shooting Stars, da na Nasarawa United da Rangers. Duk da haka, Kano Pillars na da damar ɗaukaka ƙara kan hukuncin, sai dai za a iya ƙara musu wani hukuncin idan ba su yi nasara ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA