Nentawe Yilwatda ne zai zama sabon shugaban APC na kasa
Published: 24th, July 2025 GMT
Matukar ba a sami sauyin tsare-tsare ba, akwai yiwuwar Ministan Jinkai da Yaki da Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa a yau Alhamis.
Majiyoyi da dama a daren jiya sun shaida wa Aminiya cewa Nentawe ne ke kan gaba a cikin mutanen da ake so su dare shugabancin jam’iyyar mai mulki.
Sai dai a cewar wasu majiyoyin, tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Umaru Tanko Almakura shi ma na daga cikin wadanda ake duba yiwuwar ba kujerar.
Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid a Borno NAFDAC ta gano dakin ajiye kayayyaki makare da sinadaran hada bam a KanoA daidai lokacin da ya rage ’yan sa’o’i gabanin taron Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar, majiyoyi da dama sun shaida mana cewa shugabancin jam’iyyar, wanda ya kunshi Shugaban Kasa da Gwamnoni sun yanke shawarar takaita neman wanda zai hau kujerar tsakan Nentawe da Almakura.
Nentawe dai dan asalin jihar Filato ne da ke shiyyar Arewa da Tsakiya, yankin da aka tsara zai fitar da shugaban jam’iyyar kafin daga bisani a nada tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya ajiye mukaminsa a farkon wannan watan.
To sai dai majiyoyin sun ce an saka sunan Almakura ne a matsayin zabi na biyu.
Tun bayan saukar Ganduje dai ’yan shiyyar Arewa ta Tsakiya ke ta hankoron ganin an dawo da kujerar yankinsu, kasancewar dan cikinsu, wato Sanata Abdullahi Adamu ne ke kanta kafin ya sauka bayan nasarar Shugaba Tinubu a zaben 2023.
Bayanai sun nuna sai da aka yi dogon nazari kafin a yanke shawarar dauko dan yankin kuma Kirista, saboda a hakurkurtar da wadanda zabin Musulmai guda biyu, Tinubu da Kashim, ya bakantawa.
Duk wanda ya yi nasarar dai shi ne zai karbi ragamar da shugabanta na riko na yanzu, Ali Bukar Dalori, wanda mataimakin shugaba ne kafin saukar Ganduje.
Wasu dai na cewa da shi aka kyale ya ci gaba, amma wata majiyar ta ce kasancewarsa daga jiha daya da Kashim sannan kuma Tinubu na so a yi ta ta kare a kan batun shugabancin ya sa dole a zabo wani.
Wata majiyar kuma ta ce, “Tinubu na san wani dan-a-mutun shi ya zama shugaban kamar yadda Abdullahi Adamu ya kasance zamanin Buhari”.
Sauran wadanda a baya aka yi ta rade-radin za su hau kujerar sun hada da Sanata Sani Musa (Neja) da Sanata Salihu Mustapha (Kwara) da Sanata Joshua Dariye (Filato) da Sanata George Akume (Binuwai) da kuma Sanata Abu Ibrahim (Katsina).
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Nentawe Yilwatda
এছাড়াও পড়ুন:
Ina Karanta Rantsuwar Da Na Yi A Kullum Don Tuna Nauyin Da Ke Kaina-Gwamna Namadi
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa yana yawan karanta rantsuwar kama aiki da ya yi domin tunatar da kansa nauyin da ya dauka na yi wa al’umma hidima bisa gaskiya da amana.
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Hamisu Mohammed Gumel, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba bayan nadin sabon shugaban karamar hukumar Gumel.
A wajen bikin da aka gudanar a zauren majalisar gwamnatin jihar da ke Dutse, Gwamna Namadi ya yi nuni da cewa rayuwa na da kurarran lokaci, don haka ya kamata shugabanni su kasance masu tsoron Allah da kuma sanin nauyin da ke kansu.
“Rayuwa ba ta da tabbas, hakazalika shugabanci ba wasa ba ne”. In ji shi.
Ya bukaci masu rike da madafun iko da su kasance masu kula da al’amuransu cikin tsoron Allah da sanin cewa akwai ranar hisabi da mutuwa.
Da yake jawabi ga sabon shugaban karamar hukumar, Gwamnan ya ce: “Rantsuwar da ka dauka ita ce mu ma muka dauka. Na ajiye tamu a kan teburi a ofishina, kuma kullum ina karanta ta. Ina ba ka shawarar kai ma ka rika karanta taka kafin ka fara aiki a kullum.”
Ya ja hankalin sabon shugaban da kada ya bari son zuciya ya shige masa gaba wajen gudanar da ayyukansa, yana mai cewa son kai na daga cikin manyan matsalolin da ke gurgunta mulki mai nagarta.
Ya bukaci sabon shugaban da ya yi aiki da kowa, ya rika tuntubar masu ruwa da tsaki, tare da sanya mutanen da ya ke wakilta gaba a kowanne lokaci.
Gwamnan ya kammala da cewa shugabanci yana bukatar hakuri, kwarewa, da tsoron Allah, yana mai cewa“babu wanda aka haifa da basirar shugabanci, amma da kaskantar da kai da tsoron Allah, za ka yi nasara”
Usman Muhammad Zaria