A cewar Salahudeen, Ranar Yaƙi da Cutar Polio ta Duniya muhimmiyar dama ce ta faɗakar da jama’a kan barazanar da cutar shan-inna ke haifarwa ga rayuwar al’umma da tattalin arziki, tare da sake duba nasarori da kalubalen da ake fuskanta.

 

Ya ce haɗin kai tsakanin gwamnatin jihar da kungiyoyin bunkasa lafiya — musamman Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) — ya taimaka matuƙa wajen cimma wannan gagarumar nasara.

 

“Gwamna Dauda Lawal ya ayyana dokar ta-baci a bangaren lafiya, kuma hakan ya zame ginshiqin da ya taimaka wajen samun tallafi, goyon baya da isassun ma’aikata don tabbatar da an kai rigakafi ko’ina,” inji shi.

 

Dekta Salahudeen ya kara da cewa WHO, UNICEF, Chigari, Sultan Foundation da Salina Foundation sun taka rawar gani wajen taimakawa jihar ta isa ga dukkan al’ummomi, ciki har da yankunan da ke da wahalar kaiwa.

 

Ya ce, waɗannan ƙungiyoyi sun samar da tallafin kudi, kayan aiki, horo ga ma’aikatan lafiya, da kuma goyon baya wajen aiwatar da rigakafi a kananan hukumomi 14 na jihar.

 

Daga cikin manyan nasarorin da aka samu, a cewar shi, akwai damar kai rigakafi har ma zuwa yankunan Fulani makiyaya da wuraren da ake gani a matsayin “hard-to-reach”, baya ga tallafin jami’an tsaro da ya taimaka wajen baje kolin ayyukan rigakafi cikin kwanciyar hankali.

 

“An samu damar ziyarar dukkan yankuna, har da na noma da kiwo, inda muka ga cewa ba zai yuwu mu bar kowane yaro a baya ba,” inji Salahudeen.

 

Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da hada karfi da kungiyoyin hadaka, domin tabbatar da kawar da shan-inna baki daya, tare da cigaba da karfafa wayar da kan jama’a kan muhimmancin rigakafi.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara  October 30, 2025 Labarai Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai October 30, 2025 Manyan Labarai Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda  October 30, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Hutun Kwanaki 2 Don Zaɓen Ƙananan Hukumomi

Ya ce, an ɗauki wannan matakin ne don bai wa masu zaɓe a faɗin jihar damar gudanar da zaɓen da ke tafe a jihar.

 

Ya ƙara da bayyana cewa, Gwamna Bago ya umarci dukkan hukumomin tsaro a Jihar da su tabbatar an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da tsari, yana mai sake tabbatar da alƙawarin gwamnatin Jihar na tabbatar da tsarin zaɓe mai aminci da kwanciyar hankali.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba October 28, 2025 Ra'ayi Riga Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani October 28, 2025 Labarai Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100 October 28, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya
  • Jihar Jigawa Ce Ta Fara Biyan Kudaden Kujerun Aikin Hajjin 2026- NAHCON
  • Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro
  • AA Zaura Ya Yi Kira Ga ’Yan Nijeriya Su Marawa Sauye-sauyen Shugaba Tinubu Baya
  • Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal
  • Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260
  • Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Hutun Kwanaki 2 Don Zaɓen Ƙananan Hukumomi
  • Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100
  • An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi