Kwanan nan jam’iyyar PDP ta gudanar da taron kwamitin zartarwa karo na 100 da aka gudanar ranar 30 ga Yuni, PDP ta warware rikicin da ya dade yana ci mata tuwo a kwarya na batun mukamin sakataren jam’iyyar na kasa wanda ta tabbatar da Sanata Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar.

Duk da wannan warware batun, Atiku da wasu magoya bayansa sun fice daga jam’iyyar sakamakon rashin warware rikicin gida na jam’iyyar.

A ranar 1 ga Yuli, Atiku da Peter Obi da Rotimi Amaechi da Nasir El-Rufai, da wasu sun kulla hadaka a karkashin jam’iyyar ADC, sun ce sun yi wannan hadakar ne domin kalubalantar APC a zaben 2027.

A matsayin wani bangare na wannan yunkurin hadin gwiwa, sun nada tsohon shugaban majalisar dattawa, Dabid Mark a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa na wucin gadi da tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa na wucin gadi.

Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa Makinde da Bala Mohammed su ne manyan ‘yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar a yanzu haka, yayin da ake sa ran wasu jiga-jigan jam’iyyar za su biyo baya kafin zaben 2027.

Majiyar ta ce, “Ana tambayar game da wadanda suka nuna sha’awarsu na neman tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyya a halin yanzu. Duk da dai ba su fito fili sun bayyana ba, mun ji daga wurin shugabannin jam’iyyar, cewa Makinde da Bala Mohammed har ma da wasu tsoffin gwamnonin daga Kudu suna da sha’awar neman tikitin shugaban kasa jam’iyyar PDP a 2027.

“Amma a hakikanin gaskiya, a yanzu haka ba za mu iya sanin adadin wadanda suke sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a PDP, sai idan lokaci ya yi duk za a san su. Don haka, jam’iyyar PDP ta bude kofarta ga kowa, kuma ta kasance jam’iyyar da ke da karbuwa sosai a tsakanin ‘yan Nijeriya.”

Wani jigo a jam’iyyar wanda ya nemi a Sakaye sunansa don ba a shi izinin yin magana a hukumance ba, ya goyi bayan bude tikitin takarar shugaban kasa a PDP a 2027 ga dukkan ‘yan Nijeriya.

Shi kuwa, tsohon mataimakin shugaban PDP na yankin kudu maso yammaci, Eddy Olafeso, ya bayyana cewa shugabannin jam’iyyar sun dauki darashi ga abubuwan da suka faru a baya.

Yayin da tsohon sakataren jam’iyyar na kasa, Ibrahim Tsauri, ya shawarci mambobin jam’iyyar cewa su bar uwar jam’iyyar ta yanke hukunci, sannan kuma ya yi gargadi kan kauce wa bin tsarin karba-karba.

A nasa martanin, daraktan yada labarai na jam’iyyar APC, Bala Ibrahim ya ce Shugaban Tinubu zai kayar da Makinde, Bala Mohammed, ko wani dan takarar da PDP ta tsaida a 2027.

Ibrahim ya bayyana cewa, “Makinde da Bala Mohammed ba su da wata gogewa a matakin kasa na siyasar Nijeriya. Wadannan gwamnonin biyu ba za su iya jure fafatawar siyasar kasa nan ba. Ba su da gogewar da dan takararmu yake da shi.

“Mutane da ka ambata ba su da ikon doke shugaban kasa a kowanne fanni na siyasa. Wannan ba matsala ce da za ta ba mu ciwon kai ba. Koma dai wane yanki PDP zai fitar da dan takarar shugaban kasa ba zai yi nasara ba a 2027.”

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: takarar shugaban kasa a sakataren jam iyyar jam iyyar na kasa a jam iyyar

এছাড়াও পড়ুন:

Asusun Kula Da Kananan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya “UNICEF” Ya Yi Gargadi Kan Bala’in Jin Kai A Gaza

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi karuwar bala’i na jin kai a Gaza

Kazem Abu Khalaf, kakakin hukumar UNICEF a Falasdinu, ya tabbatar da cewa: Abin da ke faruwa a Gaza ba a taba ganin irinsa ba, yana mai cewa har yanzu yana ci gaba da tuntubar wasu ma’aikatan jin kai da dama da suka yi balaguro zuwa yankunan da ake fama da rikici, da bala’o’i, da wuraren yaki a duniya, kuma dukkansu, ba tare da togiya ba, sun amince cewa, ba su taba ganin wani yanayi mai kama da abin da ke faruwa a Gaza ba.

Abu Khalaf ya yi nuni da cewa: Mutanen yankin Zirin Gaza sun fara fama da yunwa, sannan kuma kishirwa, gami da fuskantar kisa, yayin da aka jibge kayan agajin jin kai a kan iyakar da ke da tazarar kilomita goma kacal. Motar bas guda na iya daukar sa’a guda-ko kuma akalla sa’a daya da rabi kafin ta isa tsakiyar zirin Gaza da agaji, amma sojojin mamayar Isra’ila ba za su kyale ta.

Ya bayyana cewa, kasashen duniya suna nuna halin ko-in-kula, tare da nuna rashin damuwa da daukan abin da muhimmanci daga Larabawa a hukumance da kuma juya baya daga al’ummar Larabawan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araqchi Ya Jaddada Cewa; Karfin Kariya Da Makamai Masu Linzamin Iran Ne Suka Tilastawa Makiya Neman Tsagaita Wuta
  • Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki
  • Kungiyar “Human Right Watch” Ta Yi Kira Da A Saki Tsohon Shugaban Kasar Nijar Muammad Bazoum
  • An rantsar da Nentawe sabon shugaban APC na ƙasa
  • Asusun Kula Da Kananan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya “UNICEF” Ya Yi Gargadi Kan Bala’in Jin Kai A Gaza
  • Nentawe Yilwatda ne zai zama sabon shugaban APC na kasa
  • Iran Ta Zargi Amurka Da HKI Da Wargaza Dokokin Kasa Da Kasa Da Kuma Yarjeniyoyin Kasa Da Kasa
  • Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin APC Gabanin Taron Jam’iyyar
  • Shugaban Amurka Trump Ya Bukaci Gurfanar Da Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama A gaban Kuliya