2025-10-30@17:02:20 GMT
إجمالي نتائج البحث: 448
«kofin Nahiyyar Afirka na 2026»:
A ci gaba da wasannin neman shiga gasar cin kofin Nahiyyar Afirka na 2026 da ƙasar Morocco zata karɓi baƙunci, yanzu haka ƙasashe 6 sun samu nasarar shiga gasar. Ƙasashen da suka samu tikitin sun haɗa da mai masaukin baƙi: Morocco da Najeriya da Zambia da Tanzania da Malawi da Algeria da Ghana da Senegal...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Sabuwar dambarwa ta kunno kai tsakanin wasu manyan ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP, inda ake zargin cewa rikicin ya kai ga hana tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, sayen fom ɗin takarar shugabancin jam’iyyar. Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin manyan jam’iyyar a matakin kasa...
Ya ba da shawarar a mayar da wajen ayyukan al’umma kamar filin motsa jiki ko ɗakin taro maimakon a sayar shi. Kiru, ya buƙaci gwamnan jihar da ya ɗauki alhakin kura-kuran da aka tafka a wajen wannan aikin, tare da tabbatar da cewa irin wannan kuskure ba zai sake faruwa ba a nan gaba, musamman...
Wakil, ya gargaɗi masu yaɗa labaran ƙarya da su daina, yana mai cewa duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci bisa dokar laifuka ta amfani da kafafen sadarwa. Ya tabbatar da cewa ba a ƙone gidan shugaban jam’iyyar PDP ba, kuma an dawo da zaman lafiya a yankin. Ya shawarci mazauna yankin da su ci...
Rikicin Jam’iyyar ADC na Jihar Kaduna ya ɗauki sabon salo, bayan da uwar jam’iyyar ta nada tsohuwar Ministar Kuɗi, Sanata Nenadi Usman, a matsayin Shugabar Hadakar Jam’iyyar a jihar. Haka kuma jam’iyyar ta nada tsohon Kwamishinan Kudi na Jihar Kaduna, Bashir Sa’idu, na hannun daman tsohon gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufa’i, a matsayin Mataimakin Shugaban...
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamiɗo ya bayyana kudirinsa na sayen tikitin neman zama sabon Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa. Tsohon ministan ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa kudurinsa na ganin an dawo da martabar dimokuraɗiyya da kuma farfaɗo da darajar jam’iyyar yadda take da, ba zai taɓa...
Tsohon gwamnan, wanda ya dade yana cikin jam’iyyar PDP kuma fitaccen mai fada a ji a cikin jam’iyyar, yana neman jagorantar jam’iyyar yayin da take shirin yin babban taronta na kasa. Ana sa ran jam’iyyar PDP, wacce ta mulki Nijeriya daga 1999 zuwa 2015, za ta zabi sabon Shugabanta na kasa da sauran shugabannin...
Ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Lebanon ta sanar da shahadar mutum daya da kuma jikkatar wani sanadiyyar harin da HKI ta kai wa wata mota a garin Zudhar dake gundumar Nabadhiyya. Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da laabrin cewa a jiya Juma’a sojojin HKI sun bude wuta a cikin Lebanon daga kan iyakar ‘alhamamis”. Bude...
Jam’iyyar ADC ta nemi Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana wa ’yan Najeriya ainihin dalilin da ya sa ya sauya hafsoshin tsaron ƙasa ba zato ba tsammani. Aminiya ta ruwaito yadda shugaban ƙasa ya sauya hafsoshin tsaron da ya naɗa shekaru biyu da suka wuce. Gwamnan Bauchi ya naɗa ɗan uwansa a matsayin sabon Sarkin...
Ya tabbatar da cewa jam’iyyar NNPP a Kaduna tana cikin haɗin kai da zaman lafiya, inda ya bayyana batun tsige shugaban a matsayin yunƙurin ƙirƙirar rikici da tashin hankali a cikin jam’iyyar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Siyasa ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa October 22, 2025...
Ministan Babban Birnin Tarayya , Nyesom Wike, ya yi gargadin cewa irin yadda gwamnonin jam’iyyar PDP ke tafiyar da al’amuranta a yanzu, zai iya sanadin rushewar jam’iyyar. Wike, ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da ’yan jarida a Abuja ranar Juma’a, inda ya zargi gwamnonin PDP da gaza magance rikicin jam’iyyar yadda...
Manzon Allah (S.A.W.) yana da tunani mai zurfi, tunanin nan har ya shigar da shi duniyar tunani, duniyar tunani ta zamar masa gaskiya har yana tu’ammali da duniyar tunani, in ji mai wannan littafin masanin falsafa. Manzon Allah (S.A.W.) cikin gaskiya ya shiga ya yi tafakkuri, ya ya ibada, ya yi zikiri har ya koma...
Sanarwar ta ce, sojojin sun yi aiki da sahihan bayanan sirri, sun kama wanda ake zargin tare da kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, da wata mujalla cike da harsashai na musamman masu tsawon 7.62mm har guda 10, wayar hannu, da kuma kudi naira 12,000. “Sakamakon nasarar da aka samu ya haifar da...
“Allah ya albarkace mu da shugaba mai tsoron Allah da kishin jama’a – mutum ne mai kaunar al’ummar jihar Kano da Nijeriya, kuma me aiki tukuru domin ganin ci gabansu,” in ji Yusuf. Ya kuma jaddada kudirin sa na ciyar da jihar gaba bisa tsarin falsafar Kwankwasiyya, wanda ke jaddada hidima, rikon amana, da...
Shugabannin jam’iyyar PDP Na Arewa Sun Amince Da Turaki A Matsayin Ɗan Takarar Shugabancin Jam’iyyar Na Ƙasa
Sanarwar da aka fitar a karshen taron ta bayyana cewa, matakin na daga cikin kokarin da ake yi na karfafa hadin kan jam’iyyar da tabbatar da daidaiton wakilcin yanki a cikin tsarin shugabancin jam’iyyar PDP. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Waɗanda Fashewar Tankar Mai Ta Rutsa Da Su A Neja ...
Aƙalla shugabanni 15 na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Zamfara sun sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC). An gabatar da waɗannan waɗanda suka sauya shekar ne a gaban Ministan Harkokin Tsaro na Ƙasa, Dr. Bello Mohammed Matawalle, a Abuja ranar Laraba, ta hannun Shugaban APC na Jihar Zamfara, Alhaji Tukur Umar...
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce tsarin zabe a Najeriya ya samu gagarumin ci gaba tun bayan da jam’iyyar PDP ta bar mulkin kasar a matakin tarayya. Akpabio, wanda aka zabe shi sau biyu a matsayin gwamna karkashin PDP kuma ya fara shiga majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar, ya bayyana hakan ne a lokacin...
A yau Laraba 22 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana cewa, huldar diflomasiyya ta shugabanni na matukar taka rawar gani wajen jagorantar dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka, kuma shugabannin kasashen biyu suna ci gaba da cudanya da kuma sadarwa a tsakaninsu. Shugaban Amurka Trump...
Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NSGF), ta bayyana hatsarin fashewar tankar mai da ya auku a ƙauyen Essa a Ƙaramar Hukumar Katcha a Jihar Neja, a matsayin abin baƙin ciki da tausayi. Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne, ya yi alhinin lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Waɗanda ke son...
Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin cikinta game da gobarar tankar mai da ta tashi a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja, inda mutane 38 suka rasa rayukansu. A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta jajanta wa jama’a da gwamnatin Jihar Neja,...
“Sanata Wadada yana cikin rijistarmu tun da farko, kawai mun sake ba shi sabon katin zama mamba ne. Don haka, barka da dawowa gida,” in ji shi. Dakta Bello ya ce APC za ta ci gaba da karɓar duk wanda ke son dawo wa jam’iyyar kuma yana kishin ƙasar nan. A nasa ɓangaren, Sanata Aliyu...
Jam’iyyar APC reshen Jihar Borno ta rage wa mata kashi 50 cikin 100 na farashin fom ɗin tsayawa takara, makonni gabanin zaɓen kananan hukumomi da za a gudanar a ranar 13 ga Disamba, 2025. Da yake sanar da hakan a Maiduguri, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Bello Ayuba, ya ce an ɗauki matakin ne...
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya mika sakon ta’aziyyar shahadar babban hafsan hafsoshin sojan kasar Yemen Birgediya janar Muhammad Gumari ya shugaban Ansarullah Sayyid Abdulmalik al-Husi. Shekh Na’im Kassim ya bayyana alhininsa mai zurfi na rashin Shahid al-Gumari tare da bayyana shahada a matsayin wata daukaka bayan doguwar tafiya akan tafakin jihadi.Haka nan...
Sunana Aisha Isah Abubakar (Mai Waka) Gama: A gaskiya bawa yara kanana kudi wannan ba dabi’a ce mai kyau ba, saboda wata rana idan babu wannan kudi da aka sabawa yaro da shi wallahi illa ce babba. Sabida yau da gobe sai Allah idan suka rasa wannan kudi komai zai iya faruwa za su iya...
Tsohon Shugban Kasar Dimokaradiyyar Kwango Ya Koma Kasarsa Domin Kalubalantar Hukuncin Kisa Da Aka Yanke Kansa
Tsohon shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ya dawo kasarsa daga Nairobi domin kalubalantar hukuncin kisa da aka yanke masa A wani gagarumin ci gaba na siyasa, tsohon shugaban kasar Kwango Joseph Kabila, ya bayyana a bainar jama’a a Nairobi babban birnin kasar Kenya, bayan da a makonnin da suka gabata wata kotun soji a kasarsa ta...
Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC, za su koma APC a mako mai zuwa. A makonnin da suka gabata, ’yan siyasa da dama daga jam’iyyun adawa suna sauya sheƙa zuwa APC, yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027. HOTUNA: Al’ummar Jihar Neja sun yi addu’o’in...
Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC, za su koma APC a mako mai zuwa. A makonnin da suka gabata, ’yan siyasa da dama daga jam’iyyun adawa suna sauya sheƙa zuwa APC, yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027. HOTUNA: Al’ummar Jihar Neja sun yi addu’o’in...
Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnonin Jam’iyyar APC sun gudanar da wani taron sirri a gidan gwamnati da Jihar da ke Birnin Kebbi. An bayyana cewa aƙalla gwamnoni 20 daga cikin gwamnoni 24 na jam’iyyar ne suka gudananar da taron ƙarƙashin shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodinma, wanda shi ne gwamnan Jihar Imo. Gwamnan Gombe ya...
A taron majalsar zartarwar, Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa zabinsa na Amupitan ya yi ta’allaka ne a kan rashin nuna son kai na siyasa, gaskiya da kyakkyawan tarihinsa. Mambobin majalisar, ciki har da shugabanni na yanzu da na baya, sun amince da nadin, suna bayyana Farfesa Amupitan a matsayin mutum mai gaskiya....
Saboda haka, an samu labari daga bangaren Obi cewa, tsohon dan takarar shugaban kasa ba za yi zaben fid da gwani ba da Atiku. Sai dai kuma, sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya ki cewa uffan kan jita-jitan da ke cewa jam’iyyar ta yanke shawarar gudanar da zaben fid da gwani, wanda...
A jiya Alhamis jiragen yakin HKI sun kai hare-hare na wuce gona da iri garuruwa mabanbanta na kudancin Lebanon da hakan ya yi sanadiyyar shahada da kuma jikkatar mutane da dama. Majiyar tsaro daga kudancin Lebanon ta ambaci cewa, mutum daya ya yi shahada yayin da wasu 7 su ka jikkata. Hare-haren sun shafi garin...
Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce bai dace a ɗora wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, laifin rikicin da jam’iyyar PDP ke fama da shi ba. Ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, inda ya ce shugabannin PDP ne suka haddasa matsalolinsu, ba Tinubu ko jam’iyyar APC...
Jam’iyyar ADC ta ce sauya sheƙar da wasu gwamnonin jihohi suka yi zuwa jam’iyya mai mulki ya nuna yadda Shugaba Bola Tinubu, ke ƙoƙarin mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya. A wata sanarwa da Bolaji Abdullahi, mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, ya fitar, ya ce jam’iyyun adawa ba su damu da abin...
Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya fice daga jam’iyyar PDP. Mai magana da yawun gwamnan, Daniel Alabrah, ne ya sanar da hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook na ainihi, kodayake bai bayyana dalilin ficewar gwamnan daga jam’iyyar ba. Har ila yau, bai bayyana ko Gwamna Diri zai koma APC...
“Salon shugabancinsa da amincewa da cancanta sama da son rai ne ya sa kowane mai kishin ci gaba daga ƙarshe yake samun mafaka a APC,” in ji shi. Gwamna Mbah ya bayyana shiga jam’iyyar APC bayan tattaunawa da magoya bayansa, yana mai cewa hakan “sabuwar tafiya ce” ga Jihar Enugu da yankin Kudu maso Gabas...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yadda ‘ya’yan jamiyyar PDP ke ficewa suna komawa jam’iyya mai mulki na cigaba da nuna yadda take kara samun koma baya a siyasar Najeriya. Banda haka, rikicin cikin gida da yaki ci yaki cinyewa na cigaba da yi mata dabaibayi. Shin ko hakan na nufin jam’iyyar ta...
Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da PDP ke shirin gudanar da babban taronta na ƙasa da za a yi a Ibadan, a Jihar Oyo, daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar...
Ɗan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Sabon Gari Daga Jihar Kaduna, Sadiq Ango Abdullahi, ya fice daga Jam’iyyarsa ta PDP. Honorabul Abdullahi wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kwamishinan Hukumar Kula da Hanyoyi (FERMA) ya alaƙanta ficewarsa da rikicin cikin gida da rabuwar kai da ya ki ci ya ƙi cinyewa a jam’iyyar. A ranar Litinin ya...
Sakamakon farko na zaben shugaban kasar Jamhuriyar Kamaru da ake ci gaba da kirgawa ya nuna jagoran adawa, Issa Tchiroma Bakary, ya samu gagarumin rinjaye a yankunan da a bayan Shugaba Paul Biya ya saba rinjaye. Shugaba Paul Biya mai shekaru 92 yana fuskantar abokan hamayya 11 cikin har da tsofaffin mukarrabansa, da ma tsoffin...
‘Yan sa’o’i kafin sanarwar da Jam’iyyar ta RN ta yi ne dai, tsohon Firaministansa Edouard Philippe ya ce yana goyon bayan shirya sabon zaben shugaban kasa a gaggauce. Wannan matsin lamba dai kari ne kan wadda shugaban na Faransa ke fusakanta daga bangaren masu sassaucin ra’ayi, wadanda su kuma bukatarsu ita ce a...
Li ya ce kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga jam’iyyar WPK, don ta bayar da jagoranci ga al’ummun kasar Koriya ta Arewa, wajen neman ci gaba bisa halin da kasar take ciki. A sa’i daya kuma, kasar Sin tana fatan karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025 Siyasa Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu October 9, 2025 Labarai Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025 Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 9, 2025...
Bugu da kari, Xi Jinping ya yi wa jam’iyyar WPK fatan samun karin nasarori, yana mai fatan abotar Sin da Korea ta Arewa za ta dore har abada. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal October 9, 2025 Daga Birnin Sin...
Rahotanni sun bayyana cewa, karar mai lamba FHC/OS/194/2024, ta nemi umarnin tilastawa INEC da shugabanta na lokacin da su sanya sunayen wasu jami’an Jam’iyyar AA a shafin hukumar na yanar gizo bayan an cire su. Sai dai Udeze ya ci gaba da cewa, babu irin wannan hukunci ko umarnin kama shi (Yakubu), yana mai...
Tsohon Gwamnan Jihar Abiya, kuma Sanata mai wakiltar Abiyanta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne, zai sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Ya bayyana hakan a shirin siyasa na gidan talabijin na Channel a daren ranar Lraba. An kashe ɗan shekara 13 da shanu 36 a wani sabon hari...
“Yanzu muna kammala sabbin sharuɗan aikin da ASUU ta gabatar, kuma za mu bayyana amsar gwamnati nan ba da jimawa ba,” in ji shi.“Shugaba Tinubu yana da niyyar kawo ƙarshen wannan matsala gaba ɗaya.”Ya roƙi ASUU da ta ci gaba da tattaunawa maimakon fara yajin aiki, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na da niyyar...
ShareTweetSendShare CGTN Hausa and Sulaiman Related Daga Birnin SinHabakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu 22 hours agoDaga Birnin SinKaramin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas Ya Yi Bikin Bunkasa Al’adu Na Bikin Tsakiyar Kaka 23 hours agoDaga Birnin SinNazari Ya Gano Falalen...
Wani dan kasar Lebanon da matarsa sun yi shahada sanadiyyar hare-haren jiragen yakin HKI a kan motarsu a kauyen Zabdaini na kudancin kasar Lebanon. Tashar talabijan ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto dan rahotonta a yankin yana cewa jiragen yakin HKI wadanda ake sarrafasu daga nesa sun kai hari a kan motar dan kasar...
Jam’iyyar ADC ta zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da rashin mayar da hankali kan yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a ƙasar nan. Jam’iyyar ta ce shugaban yaf i damuwa 2ajen halartar tarukan siyasa da biki, maimakon kare rayukan ’yan Najeriya. Ɓarayin daji sun kashe kwamandan maharba a Kaduna Mata da yara 95,000 ke mutuwa...